← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 69

Sashe 44

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA HU Tun da Uwani ta fito daga gidan baba Isuhu daga shi har Lami babu wanda ya kuma motsin kirki, baba Isuhu ya shar e hawaye ya dubi Lami cikin kallon tsana da jin haushi ya ce. "Tsakanina da ke Allah Ya isa Lami, kin cuce ni kin cuci rayuwata. Ni ban san addarar da ta sa na auro ki ba, duk wannan aton bakin na ki ko ina ya je da ban gan shi ba sai yanzu?" Lami ta wurga masa harara ta ce. "Mun dai cuci juna malam ka gyara maganarka. Ni kaina ban azal da kuma rabo me zan yi da kai? Ka san dai duk a samarina kai ne fa iri matsiyaci." "Wallahi aurena da ke bai are ni da komai ba sai masifa, ina zaman zamana kin jefa ni a jafa'i muguwa mai ashin tsiya..." "Dakata malam, kada ka raina mini hankali. An gaya maka ban san dama can kana 'yan sace-sacenka ba? Ko ka manta kajin Yaya Haladu da muka ta a soyewa?" Shiru baba Isuhu ya yi yana nazari, shi kam ya ci alwashin daga uwar garke har abada ba zai ara ta a kayan wani ba. Dama tun da yake 'yan auke-daukensa ba a ta a kama shi ba, don haka zai ajiye sata salin-alin ba tare da ta tona masa asiri ba. Suna nan zaune suka ji an rafka kiran sallar Isha'i, babu jimawa suka ji takun Goggo Sala tana tafe da baya-baya, taku aya-biyu idan ta yi sai ta ci karo da kwanuka sannan ta furta. "Nasara dai a kanku Isuhu da Lami." Da hannu Lami ta yafito baba Isuhu ta cikin labule take nuna masa ita, cikin gasgata maganar da Uwani ta gaya musu suka saki baki suna kallonta, a angare aya kuma tsoron Goggo Sala ya kama su. Tana shiga akin da suke kwana da Lami ta banko ofa, can uryar bango ta zauna sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai cin zuciya. "Kaico kwa ayina bai amfane ni da komai ba, Allah ka fitar da ni daga wannan gidan annobar. Wallahi nan gaba idan duniya Lami za ta haifa har abada ni da gidanta." Ganin ta shige aki ya sa baba Isuhu ya fita a hankali domin cika umarnin uwar garke, kai tsaye garken Uwani ya nufa yana haskawa kuwa ya yi ido biyu da tukunyar farfesun naman. Nan take irjinsa ya buga, jikinsa ya fara karkarwa sai da ya yi ta maza ya auko tukunyar ya nufi sashensa. WASHEGARI Baba Isuhu tun da ya yi sallar asuba ya gagara runtsawa saboda fargabar goyon da Goggo Sala za ta yi masa, yana zaune a gefen gado ya kallo Lami da ke kwance ita da mai sunan malam. Motsi ya ji a tsakar gida yana le awa ya hangi Goggo Sala tana kaiwa da kawowa, abin duniya ya dame ta saboda gari ya fara haske amma har kawo lokacin babu Isuhu babu motsinsa. Cikin san a ta nufo akin da suke ciki baba Isuhu ya le o ta windo ya ce. "Munafukar Allah ta'ala ina ankare da ke, wato fakona kike za ki hallaka ni ko?" Goggo Sala ta washe baki tana basarwa ta ce. "Isuhu barka da safiya." Baba Isuhu da ya tuna garga in da aka masa, aka ce kar ya yi mata kora da hali shi ma sai ya ya e baki ya amsa. Amma a zuciyarsa ji yake tamkar ya fashe da kuka. Mai sunan malam ne ya motsa Lami ta yi fitgigit ta tashi zaune. "Maza tashi mu je ki kai shi wurin Jafaru." Ba musu Lami ta tashi ta saka hijabinta, baba Isuhu ya manta Goggo Sala da ke waje tana fakonsa ya sa hannu ya bu e sakata suka fito. Har zai yi gaba ya tuna bai ebo rigunan maman Lami da aka ce ya kai wa Dada ba, dama tun a daren ya sa Lami ta ebo masa guda uku daga cikin na ta. Komawa ya yi ya ebo ya zuba a aljihu sannan ya fito. Yana fitowa Goggo Sala ta yi wata uwar sufa za ta cafko baba Isuhu, a firgice ya zuba a guje yana fa "Wayyo Lami ki zo za ta cafke ni, wallahi tsaf za ta sa a tsotse romon kaina." Goggo Sala na ganin rana ta fara fitowa ga shi ba ta cika umarnin uwar garke ba, ya sa ta rufa wa baba Isuhu baya yana gudu tana bin sa. Da yake ya gama tsorata da ita har gani yake kamanin Goggo Sala kamar har riki e masa suke yi, Goggo Sala irin dogayen matan nan ne, shi kuma baba Isuhu ba shi da tsayi kuma ba shi da jiki. Don haka Goggo Sala ta kusa kama shi amma Allah ya taimake shi ya fice daga gidan, Lami ta rufa masa baya da sauri ya tura ofar ya datse ta. Wata gwaruwar ajiyar zuciya ya sauke yana ayyana shi kenan da tuni an bayar da jininsa. angaren Dada a bu e yake don haka ba su sha wata wahala ba suka nufi akin da Jafar yake ciki, Lami ce ta fara wasawa sun an jima sannan Jafar ya bu e da alama bacci yake yi. Daga shi sai singlet da gajeren wando ya bu ofar yana murza idanu. Da mamaki yake bin su Baba Isuhu da kallo ya furta. "Ina kwana baba." Baba Isuhu ya washe baki. "Jafaru an tashi lafiya?" Jafar ya amsa sai baba Isuhu ya ce. "Wurinka muka zo Jafaru amma ko za mu arasa akin Dada?" Zuciyar Jafar fes ya ce. "Ok to bari na saka kaya ga ni nan zuwa." Lami da baba Isuhu suka wuce akin Dada a lokacin tana zaune tana jan carbi. Tana ganinsu ta shafa addu'ar, sai da ta cire hijabin ta ajiye carbin ta ce. "Isuhu lafiya na gan ku da farar safiyar nan?" Cikin ha in baki suka gaishe ta. Baba Isuhu ya ciro rigunan maman hannunsa ya mi a wa Dada ya ce. "Dada ga wannan a saka." Dada ta kar a tana yamutsa fuska. "Kai kuwa Isuhu kamar wanda ya kwana da Uwani a rai, tun da farar safiya ka kawo mata wata rigar mama. Wannan dai rigunan ai na manyan mata ne, ina Uwani ina wannan lalacewar." Baba Isuhu ya an sosa kai ya ce, "Ai dama ba na Uwani ba ne, ke na kawowa Dada..." Tun bai arasa magana ba Dada ta katse shi, "Ni fa Isuhu? Ni kuwa me zan yi da rigar mama tsofai-tsafai? Amma dai ka ci mutumcina Isuhu, wai ko dai ka fara 'yan zu e-zu e ban sani ba?" Idanun baba Isuhu suka ciko da walla sai da ya share hawaye ya ce. "Don girman Allah Dada ki iba ki shiga aki ki saka." Baki sake Dada take kallonsa, ta rafka salati ha e da fa in, "Maza kwashe mini lalatattun kayan nan kafin ranka ya aci. Ni Kulu uban me zan saka a ciki? An ya Isuhu sha anu ba su dafa maka kai a cikin bacci ba?" Uwani da ke uwar aki ta sunne kai asa tana dariya. "Haba Dada da farar safiya ki cika wa mutane kunne da ihu." Jafar ya fa a yana sako kansa cikin akin. Uwani da ke oye a aki ta yi asa da murya ta ce, "Kai ma naka ihun yana tafe." "Ba dole ka ji ihuna ba Jafaru yanzu kamar ni tsofai-tsofai." Sai kuka ya ci arfin Dada sai da ta share hawaye sannan ta watsa wa Jafar rigunan a fuska ta ci gaba. "Wai Isuhu ya rasa me zai kawo mini sai baraziya wai na saka. Yanzu saboda Allah Jafaru ko uwarka Saratu me za ta yi da baraziyya ballantana kuma ni?" Tun Dada ba ta gama magana ba Jafar ya watsar da rigunan sakamakon wani tsami da bashi-bashi da ya ji ya doko hancinsa. "Haba Dada me kike yi haka ne?" Jafar ya fa a a azance. Kafin Dada ta yi magana mai sunan Malam ya sake tsanyarewa da kuka, Lami ta dubi Jafar ta mi a masa shi. Kamar Jafar zai yi magana sai kuma ya basar ya mi a hannu ya kar e shi, yana bin su da kallon mamaki. "Don Allah Jafaru ka taimaki yaron nan ka ba shi mama ya sha ko ya yi shiru." Lami ta fa a a an kunyace. Jafar ya kalli Lami cikin sauri ya ce. "Wane Jafarun?" Jafar ya tambaya a hargitse. "Kai mana Jafaru, don Allah ka yi ka ba shi kada ya shi e don tun azu yake kuka." Baba Isuhu ya furta. Ran Jafar ba aramin aci ya yi ba, ya ha e fuska ya dubi baba Isuhu. "Baba wannan wacce irin magana ce babu tsari, yanzu idan na fa a maka magana a ce na yi rashin kunya. Idan har ni zan iya shayar da shi me ya hana kai ba ka shayar da shi ba?" Dada ta saki baki da hanci tana kallon baba Isuhu a tsorace, don ita a yanzu ya fara ba ta tsoro shi da Lami. A hankali ya ajiye mai sunan malam a gefe sannan ya mi e, yana shirin tafiya Lami ta ce. "Isuhu sai fa mun danne shi..." Tun Lami ba ta arasa magana ba baba Isuhu ya sa afa ya shatalo afar Jafar sai ga Jafar a asa. Dada na ganin haka ta fara tafiya da rarrafe don ta tabbata yau su Isuhu babu lafiya, shi ya sa ta nemi guduwa kafin ita ma su dawo kanta su danne ta su saka mata rigar mama. Jafar ya yi mamakin yadda ya gagara wace kansa a hannun baba Isuhu, don haka jin baba Isuhu ya fara aga masa riga sama ya fara kiciniyar kare kansa, garin yun urin danne rigarsa sai ga Jafar yana sakin tusa. Uwani kuwa me za ta yi ba dariya ba har hawaye saboda mugunta. Ganin haka ba zai kai Jafar ba ya sa ya fara ihu. "Wayyo Dada ki kawo mini auki. Wayyo Allah! Mutanen gidan nan ku kawo min auki
Chapter 44 · 0% Book details