Sashe 62
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
cikin murna, don tun daga nesa ta hango motar baba Mamman. Don haka da saurinta ta bu e motar tana fa "Daddy wallahi na yi kewar Dada, ila ma ita tana can ko a jikin..." Kalamanta suka ma ale a ma oshi sakamakon ido biyu da suka yi da Jafar. Wata uwar harara ya banka mata, ta yamutsa fuska tana are masa kallo ta ce. "To kai kuma ina motarka ka auko ta Daddy?" Jafar bai tanka mata ba ya fisgi motar da gudun gaske har sai da wasu yara suka matsa a guje. Suna cikin tafiya babu wanda ya tanka wa wani sai Uwani ta fashe da dariya har da yatawa, a fusace Jafar ya waigo ya zuba mata manyan idonsa. Sai kuwa Uwani ta sake kwashewa da dariya, gangara motar ya yi ya faka ya auke kai gefe a da ile ya ce. "Fice mini daga mota." Uwani ta gimtse dariyarta sannan ta ce. "Kamar ya na sauka ai ba motarka ba ce." "Uban me kike wa dariya?" Uwani ta yi murmushi ta ce, "Wallahi dariya ka ba ni, ni dai ba ba uwa ba ce a wurinka atoh. Kuma dai komai na ka Dada ta ba ni labari tun kana jariri har fa tunbi in da ka dinga yi kana yaro. Sai kuma na ga ka fafaki mota kana yin wani irin tu in 'yan Kaduna-Zaria, to wai ni birgar me za ka yi mini?" Jafar ya ha iyi wani yawu mai aci ha e da fusgar da iska mai zafi, jin irin maganganun da Uwani ta fa a masa. Yana shirin yin magana Uwani ta sake sakin wata dariyar tana fa in. "Kasan Allah yadda ka iya fafakar motar nan da Inuwan Toyota zai ganka tsaf zai auke ka kwandasta, saboda wataran idan ya gaji ya ba ka ani..." "Fice mini a mota." Ya furta mata cikin tsawa. "Wallahi ba zan fita ba ai motar Daddy ce, malam kada ka yi mini gori ni nan gaba ma jirgin sama zan tu a." Kalamanta na arshe suka kusa ba shi dariya. 'Yarinyar da cikakkun sentence na hausa ma ba ta iya ha awa ba ita ce za ta tu a jirgin sama.' Ya raya a ransa. Ganin za ta ata masa lokaci ya sa ya fisgi motar ya ci gaba da sharara gudu, har suka arasa gida wani bai sake kula kowa ba. Tun Jafar bai gama faka motar ba Uwani ta suri jakar kayanta ta alle murfin motar ta fice a guje ko rufe motar ba ta tsaya yi ba, tun daga soro ta fara walla wa Dada kira tana washe baki. Mami da ta rako aminiyarta Hajiya Falmata ganin Uwani ya sake tado mata da wani malolon ba in ciki. wata wannan abar ce fa aka aura wa Jafar, imagine a ce wannan ce sirikata." Hajiya Falmata ta are wa Uwani kallo sannan ta saki wani malalacin murmushi ta furta. "Haba awata wai da wannan 'yar abar ce ke barazana da aurenki? Tun da uruciya ba ki yi yaji ba sai yanzu? Babu inda za ki, matu ar kin bi duk tattaunawar da muka yi wallahi na fa a miki da afarta za ta kori kanta babu boka babu malam." Sai a lokacin Mami ta ara jin warin gwiwa, Hajiya Falmata ta ci gaba da biya mata miyagun shawarwari sannan suka yi sallama. Da murna Dada ta tarbi Uwani don ita kanta ba aramin kewarta ta yi ba, dalilin da ya sa tun safe ta sa baba Mamman ya auko ta. Shi kuma ya ce a bari zuwa bayan azahar sai Jafar ya auko ta. Kuma ya yi haka ne domin so yake kafin lokacin tariyarsu su ara samun fahimtar juna. Sai da aka yi sallar Margriba kamar yadda Baba Yunusa ya ce za a zauna ya tara 'yan uwansa, Dada, na Madina, Uwani, Jafar da kuma Mami. Sai da ya bu e taron da addu'a bayan kowa ga gama sannan ya fara magana. "Alhamdu Lillah! Na san wasu daga cikinku sun san dalilin wannan zaman yayin da wasu kuma ba su sani ba. Ma asudin zamanmu a kan kai Jafar da kuma ke Uwani ne." Jafar ya sunkuyar da kai asa rai a bace. Tsabar takaici ya sa Mami yin wafa a fili, Dada ta dube ta ha e da ta e fuska ta ce. "Aure dai Allah Ya ha a duk mai hassada sai rabo ya kashe shi, yara su haihu kuma a mayar da sunansa." Mami ta shiga aika wa Dada harara a fakaice. "Jafar a yanzu wani nauyi ya hau kanka domin aure ba wasa ba ne, ka ri e yarinyar mutane amana don a yanzu da kake gani komai nata ya dawo ashin ikonka. Ke kuma Uwani wannan da kike gani aljannarki na ashin afarsa, ki bi mijinki sau da afa yi na yi bari na bari. Duk abin da kika san zai faranta ran mijinki shi za ki yi, abin da ba ya so sai ki ha ura da shi don zaman aure an ha uri ne." Sai da Baba Yunusa ya numfasa sannan ya ci gaba. "Mun tattauna ni da 'yan uwana a kan za ku tare tare da Mahaifinku tun da an riga an aura aure babu fa'idar a ce za a zauna har sai nan da wata biyu idan auren su Shukra ya zo. A don haka idan Allah Ya kai mu ranar Laraba mai zuwa ne mahaifinku Mamman ya ce za a arasa gyara komai da saka komai na gidan, tun da akwai wadataccen wuri za ku zauna a aramin part in da ke gefen na Maminku." Wani irin tu in zafi ne a zuciyar Mami har za ta i amimcewa da hakan sai kuma ta tuna da hu ubar awarta Hajiya Falmata. "Saboda haka muka yanke shawarar idan Allah Ya kai mu juma'a mai zuwa ne tariyarku, kuma bayan nan za a nema wa Uwani wata makarantar za ta ci gaba da karatunta. Idan ya so bayan sun yi hutu sai ka auki matarka ku wuce wurin aiki." Jafar ya yi shiru ba tare da ya amsa ba. Wannan maganar ta arshe ba aramin da i ta yi wa Mami ba, don a wannan lokacin ne za ta ci karenta babu babbaka a kan Uwani. "Ni iya abin da zan iya ce wa kenan, Dada kafin mu zo kan ki ko akwai mai magana a cikin?" Gaba aya suka girgiza kai ban da Baba Mustafa da ya ce yana da abin cewa. "Sannu da ari Yaya Allah Ya ara girma, duk bayananka a kan tsari suke. Amma abin da nake gani me zai hana a aga tariyar ta su zuwa nan da kamar sati biyu zuwa uku, duba da yanayin ragowar shirye-shiryen da ya kamata a yi musu. Daga ha a lefe har zuwa wani shirye-shirye na su na mata, sannan a wannan lokacin mahaifiyar yarinyar na cikin halin rashin 'yarta. Amma bayan wannan lokacin ita kanta za ta samu nutsuwar gudanar da bikin yadda ya kamata." Dada ta jinjina kai sannan ta furta. "Wallahi Mustafa ka yi kyan kai, saboda Allah kamar gajiya na yi da Uwanin da za a ce nan da kwana hu u a kai ta akin miji." Baba Yunusa ya yi murmushi ya furta. "Wannan haka ne, Dada me za kike ganin ya dace bayan haka." Dada ta yi jim sannan ta furta. "Ni dai kam nasiha ce zan yi wa Jafaru da ita Uwani, amma kam ba yanzu zan yi musu ba sai ranar da za su tare. Don ina gudun na tofar da yawun bakina a banza, su barba ar da nasihar da na yi musu tun kafin tariyarsu." Tambayar Mami aka yi ko tana da abin fa a ta ce babu, don haka suka aren zaman tun ba a gama addu'a ba Mami ta sa afarta ta fice rai a ace. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam [21/06/2024, 12:32] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*