Sashe 32
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai musulmi ne, ka yarda da addara mai kyau da akasinta. Sannan ka san Ubangiji ne ya ba ka an Bishir, a lokacin da ba ka yi tsammani ba. Don haka kenan ko a yau Allah Ya yi niyyar auke abinsa zai iya. To me zai sa ka kashe kanka a banza da wofi, ko ka janyo wa kanka ciwo ya kwantar da kai. Lokacin da na zo likitoci sun tabbatar mini ko a asibitin nan ka yi suma ya fi bakwai, don Allah ka kwantar da hankalinka. Yanzu ina son daga nan zan wuce na je na samu Bala Wanzan, da shi Idi Naira na ji yadda aka haihu a ragaya. Idan na ji ta bakinsu sai mu wuce asibiti ungurungum a yi haihuwa da hanji, amma babu yadda za a yi a dinga fa ar cuta da fatar baki ba tare da an tabbatar ba." Da sauri Baba Sale ya ri o hannunsa ya furta. "Yaya zan bi ka, gara a yi komai a kan idona." Baba Ibrahim ya sake ha ai rai ya ce, "Idan ka san za ka yi mini hayaniya ko ka je kana sume-sume gara ka yi zamanka a nan." Cikin sauri Baba Sale ya girgiza kai, Baba Ibrahim ya yi wa lokitocin bayani sannan ya biya su ku in ruwa da alluran da ake yi masa; suka wuce Police station. Bayan sun gaisa Baba Ibrahim ya gabatar da kansa sannan ya ora da cewa. "Yalla ai zuwa na yi domin na ji kan zancen abin da ya faru, idan da yuwuwar zuwa asibiti a yanzu sai mu wuce gaba aya." Sergent in da ke tsaye ya bu e wani file ya zaro takarda ya ce, "Alhaji wani mutum mai suna Malam Shehu mai doya shi ya kawo arar Bala wanzan, yana tuhumarsa da cin zarafinsa bayan ya je ofar gidansa. Sannan laifin da Bala ya yi har da zagin aya daga cikin ma'aikatanmu, abin da kuma ya sake dagula case in zargin cutar HIV da ake yi wa Alhaji Idi Naira. Yanzu haka shi ma Idi ya kawo Malam Shehu wurinmu, a kan zargin yana a ta masa suna da wannan cutar." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu za mu iya ganin Bala Wanzan in?" "Gaskiya sai dai zuwa gobe idan Allah Ya kai mu." ansandan ya furta. Babu yadda suka iya haka suka wuce gida, sai dai kaso talatin a cikin ari na damuwar Baba Sale ta ragu, saboda ya ji an ce Alhaji Idi Naira ya yi arar Malam Shehu zai ata masa suna. Mai Yasin tun da ya saka 'Yar gwal a idonsa soyayyarta ta dawo masa sabuwa fil a ransa, haka a angare aya kishinta ya mamaye shi, yana jin tsanar anladi a ransa don dai kawai yana shakkarsa ne. Yana daga akinsa ya hango ta, ta nufi ban aki da buta a hannu shi ma ya yi zaraf ya auki buta ya rufa mata baya. Tana shiga ban aki za ta turo ofa ta ji mutum yana arin turowa, suna ha a ido ta saki murmushi irin na 'yan bariki ta ce. "Mai Yasin namu, ashe a wannan lungun ka lafe?" Mai Yasin ya ri o hannunta ya ce, "Ga ni kuwa kin gani, wai dama 'Yar gwal za ki iya auren wani namijin ba ni ba?" 'Lallai wannan gafalallan tsohon naka wasa ne.' Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Ka da ka sake kallona a matsayin matar aure, saboda wannan auren nawa shi da babu duk aya. 'Yar gwal ta auri anladi ne domin ta yi masa tatsar mai, idan ta kwashe albarkar aljihunsa sai ta ara gaba." "Sai da ke 'Yar kunama!" Mai Yasin ya yi maganar yana dariya, sannan ya yi asa da murya ya ce. "Yanzu ni ya za ki yi da ni?" "A'a ka ji da tsohuwar da ka samu, idan fa muka bari suka san ala armu na rantse da Allah ni da kai sai dai mu yi biyu-babu. Kawai mu cigaba da sabgarmu, kowa ya wawuri abin da ya wawura ko a fakaice ma dinga ha uwa." Guntun tsaki Mai Yasin ya ja, ya ce. "Wa yake ta wata tsohuwa? ila dai a rashinki yau na waiwayi ha ina a wurinta." 'Yar gwal ta saki dariya, sannan ta ce ya yi maza ya tafi don kada wani ya gansu. Bayan 'Yar gwal ta koma a tsakar gida ta ci karo da Laraba tana 'yar carafke, tana shiga ta ebo wankin rigunan mama da an kamfai ta wurga mata a fuska. Tsaminsu ha e da warin man bilicin in da 'Yar gwal take shafawa ya bigi Laraba, ta ture su tana yamutsa fuska. "Ke! Wanke mini su yanzu, ina son su fita sosai." Da mamki Laraba take kallon ta. "Ko ba za ki wanke ba? Kika zubo mini ido irin na marasa tarbiyya kina kallo." Laraba ta tashi ta aga wani wargajejen an kamfai, sai kawai ta tuntsire da dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta tsugunna, ta janyo wata war iyar rigar mama ta ago ta ta sake kwanciya tana dariya. "Don uwarki dariya ma za ki yi mini? Wato ni za ki mayar 'yar iska?" Laraba ta tsagaita da dariya tana an tsuke fuska ta furta. "Kambu... Kada ki sake zagin uwata tana asa, ki zagi kowa nawa ban ta uwata wallahi. Ehe, ba dole mutum ya yi dariya ba wannan ai ya isa na yi hijabi da shi." "Rashin kunya za ki yi mini?" 'Yar gwal ta arasa gaban Laraba a fusace. Laraba ta juya mata baya tana ago ankwalinta gaba ta ce. "Fa a wa eya ankwali ya ba ki amsa 'yan mata." Laraba tana juyowa 'Yar gwal ta wanke ta da mari, a hargitse Laraba ta ago za ta yi magana anladi ya arasa yana fa "Kin yi mini daidai sanyin zuciyata, wato har yanzu kina nan da iskancinki ko Laraba? Maza wuce ki kwashe su ki wanke kada ranki ya aci." Idon Laraba ya yi ja saboda acin rai, ta harari 'Yar gwal a hankali ta ce. "Allah Ya isa ban yafe..." Tun ba ta gama magana ba, kamar ha in baki anladi da 'Yar gwal suka make bakinta, nan take bakin ya fashe amma a dole ta kwashe kayan, ta fara wanki saboda yadda anladi ya ciro belt zai zane ta da shi. Sai da ta yi wa kayan ruwa kusan hu u kowanne 'Yar gwal tana cewa bai wanku ba, sai a na biyar sannan suka bar Laraba ta fara shanya a lokacin har an fara kiran sallar isha'i. Jin shirun Laraba ya yi yawa ya sa Inno ta fito daga sashenta, tana zuwa harabar ta ci karo da ita tana shanyar kaya su anladi suna tsaye a kanta. "Laraba me kike yi haka da daren nan?" Murya tana rawa Laraba ta ce, "Wanki." Inno ta ance ido ta ce, "Mene ne wannan kamar an diras? Ke wuce ciki mu je." Da sauri Laraba ta saki na hannunta ta wuce ciki, Inno ta dubi anladi rai a ace ta ce. "Ba baiwa aka sayo muku ba, tun da ba ka da mutumci haka matarka ma ba ta gaji arziki ba wallahi ba za ku mori Laraba. Mun kwana a gida aya, amma ban da mutumci da za ku zo ku gaishe ni." Inno ta wuce sashenta a zafafe. Ran Laraba ya aci sosai, ita kanta ta san a banza ma tana dafa mutum da ruwan jikinsa har ya nuna, ballantana sun ta o ta da kansu. Don haka ta ci alwashin yadda suka azabtar da ita sai ta rama. Tun da dare ya fara yi Laraba ta fara zarya, tana saka da warwarar abin da za ta aikata, tana wucewa ta ga 'Yar gwal a ofar aki tana dama kunun gya a. Da sauri ta fa akin Inno, a can drower madubi ta bu e ta ciro wani maganin hawan jinin Inno, mai saka bacci ta allo guda takwas. A a'ida Inno aya take sha a wuni guda, kuma a hakan ma bacci yake saka ta sosai. Bayan jininta ya sauka ne aka sauya mata wani, don haka ta daina shansa. A cikin aramar farar leda ta zuba su ta ebi ruwa ka an ta zuba, sai da ya narke sannan ta fita cikin sa'a kuwa ta ga 'Yar gwal ta shiga aki. Da sauri ta matse maganin a cikin jug in kunun, ta juya cikin sauri ta bar wurin. Tana la e a bakin ofar Inno tana le e ta ofa, ta ji lokacin da 'Yar gwal ta auka ta shiga aki. Zuciyar Laraba al da haye katifa ta kwanta, tana shirya irin muguntar da za ta yi musu. A fili ta saki dariya, Inno ta wurga mata harara sannan ta auki furar Mai Yasin ta nufi akinsa. Saboda Laraba ta taki mugunta haka ta zauna tunkur, har kusan arfe ayan dare. Sai da ta fito cikin san a zuwa ofar akin Mai Yasin, ta kasa kunne ta ji munsharin Inno da Mai yasin sannan ta sa a ta fice daga sashensu ta isa akin anladi. A yadda ta fahimta sun jima da yin bacci, don lokacin da ta aga labulen akin a asa ta gansu sun ingire suna bacci, 'Yar gwal tana jingine da bango da kofin kunnu a hannunta. Sai da Laraba ta saka ankwali ta rufe fuskarta, sannan ta auki sauran kunun ta juye mata a fuskar. Wani tunani ne ya fa o mata ta fita da sauri, ta auko jarkar ruwa irin ta 'yan-ga-ruwa ta tuttule musu ruwan gaba aya a akin. Ta janyo galan in man gya arsu ta she a a afafuwan 'Yar gwala da anladi, ta kai jarkar man ta sa ala mata a hannu. A hankali ta lalalla a ta ja afar abladi sai ta ji ya tafi yaraf, daga shi da ma sai gajeren wando da singlet. Ta auko aton omonsu ta zazzage masa a jiki zuwa fuska, har ta je za ta fita ta hango belt insa da sauri ta auka ta fara zabga musu aya bayan aya. Sai da ta ga sun fara motsi sannan ta fice daga akin da sauri, ta nufi akin Inno. Tana zuwa ta shige bargo ta kwanta