← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 69

Sashe 23

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sun tsallaka shi, dubi idon munafuka sun yi kama da ba en mayu. Wai ma ku su waye a garin nan!" Daga arshe Sallau ya wurga musu tambaya. Daga Mahmud har Mudassir aka rasa mai magana, ba su yi aune ba Mai daban-daban ya fiszo wata atuwar igiyar da yake aure damin itace, shi da Haladu suka shiga aure Mahmud da Mudassir. "Wallahi mu ba i ne kuma alibai, don Allah ku kunce mu. Wallahi ba mu yi gadon maita ba." Madassir ya fa a murya tana rawa. Babu wanda ya kula shi, sai da suka aure su tsaf sannan suka shiga yayyafa wa Mai gari ruwa. "Wallahi matu ar ranka shi da e ya mutu gaba aya sai mun one ku." Mai daban-daban ya furta, ganin sun gama juye ruwan buta guda a kan Mai gari ba tare da ya motsa ba. Mahmud da Mudassir kusan lokaci aya suka kallo wutar tukubar naman Mai daban-daban, kamar ha in baki sai kawai suka arke da kuka; bayan zuciya ta gama raya musu Mai gari zai iya mutuwa tun da sun ga bai motsa ba. Dukan irjin Mai gari aka fara yi ana shafa masa ruwa a fuska, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya. Ya bu e idanunsa a hankali yana kallonsu aya bayan aya. "Su waye ku? Mu ne ko kuma su in ne?" Mai gari ya fa a yana raba idanu kamar osan sadaka. "Allah Ya taimake ka Mai daban-daban ne, sannu ya jikin naka?" Mai daban-daban ya furta yana tallafo Mai gari. Tashi ya yi zaune ya sake kallonsu, sai a lokacin komai ya shiga dawo masa. "Mai daban-daban ni ka ai kuka gani, ko kun ga wani jinsin bayan ni?" Mai gari ya tambaya a firgice. "Allah Ya taimake ka kai ka ai ka fara shigowa, sai kuma wa ancen matasan." Ya fa a yana nuna masa su Mahmud, da fuskarsu ta kumbure suntum saboda kuka. A zabure Mai gari ya mi e jikinsa yana rawa, gudun kada ya sake fita da gudu ya sa su Haladu suka dafe kafa unsa. A madadin Mai gari ya yi musu bayani sai ya fashe da kuka, yana cusa kansa a cikin jinkinsu. Cikin tashin hankali ya ce. "Wallahi ba mutane ba ne, aljanun Laraba ne daga hukumar kare ha in aljanu ta fa in duniya." A razane suka dubi su Mahmud, Mai daban-daban ya bugi irjinsa sannan ya zaro wani kwalli a aljihu ya saka a idonsa. Ya kalli su Mahmud na wani lokaci ya ce. "Wa annan yaran mutane ne, domin babu wani aljani da ya isa ya yi mini kurari. Sa'a kuka ci na ji an ambaci sunan Laraba da tuni na she a kurwarku iyama." Mahmud ya ame Muddasir irjinsa yana bugawa. "Kai uban me ya kai ku razana Mai gari." Ya wurga musu tambaya yana zare ido. "Dama wannan ne..." Da sauri Mahmud ya katse Mudassir da yake son tona masa asiri, ya kwashe abin da ya faru tsakaninsu da Mai gari na aiken yaro da suka yi, don a yi musu sallama da shi su gabatar da kansu a wurinsa. Kunyar duniya ta lullu e Mai gari musamman da ya gan shi a yashe da gajeren wando, ya dubi Haladu cikin tsare gida da borin kunya ya ce. "Kai Haladu, a suturta mu ba ma son raini. Muna bu atar babbar rigarku, wane irin iskanci ne za a gan mu a haka; kuma a yale mu tsirara ana are wa surarmu kallo?" Haladu ya gimtse dariyarsa, ganin yadda Mai gari yake cijewa yana ha e rai, ya ciro babbar rigarsa ya mi a masa. Mai gari ya dubi Mai daban-daban ya ce. "Ku kuma sai mun bu aci hula za a ba mu saboda rashin girmama na gaba?" Tun bai gama magana ba, ya ciro hular kansa ya mi a masa. Bayan ya saka ya dubi Sallau cikin kurari ya ce. "Ba tun yau ba, muka lura kuna da jiji da kai. Idan ba ku kwa o takalmanku ba, za mu yanke muku hukuncin noman gonar bayan gidanmu." Da sauri Sallau, ya sunkuya ya ce. "Tuba nake ranka shi da e." Daga haka ya mi a masa takalmansa. Mai gari ya dubi su Mahmud yana baza babbar riga ya ce. "A kunce su yanzu, kuma su same mu a ofar fada idan Allah Ya kaimu." Daga haka ya yi gaba, har ya fara tafiya borin kunya ya sa sake juyowa ya ce. "Kai Haladu za a bi bayanmu ana yi mana kirari, ko sai mun tura ku birni gidan yari!" Da sauri Haladu ya koma gefen Mai gari, yana tafe a gefensa yana yi masa kirari. Shi kuma yana tafe cikin asaita kamar ba zai tata asa ba. Mai daban-daban ya kunce su Mahmud, suka fito daga runfar jiki a sanyaye kamar marayun zakaru, suka nufi hanyar gidan da suka sauka. Washegari A hankali yake bubbuga ofar sashen Inno, kusan minti aya yana tsaye ba tare da an bu e ba. Inno ce ta arasa tana fa in, "Waye haka zai alle mini ofa? Saboda Allah mutum bai gina mini ba, da farar safiya ya nemi karya mini ita..." Ba ta arasa maganar ba ta cire sakatar, ganin Fadil a tsaye ya sa Inno ta ance ido ta kalle shi tana fa "Wane ne haka kamar Iro?" Fadil ya saki murmushi don ya fahimci Inno rikici take ji, shi kuma ba zai biye mata ba. "Eh shi ne." Ya ba ta amsa yana gegarewa ta gefe ya wuce ciki. "Kai boka ni fa na gaji da ganinka a sashena, ita waccen figigiyar matar taka ban isa ta zo ta gaishe ni ba kenan? Kullum sai dai ka ebo doro ka shigo mini gida." Fadil bai tanka mata har ya shiga ya zauna, kasancewar ranar weekend ce ta sa koda da ya ga Laraba tana bacci bai tanka wa Inno ba. "Ina kwana Inno?" Ya furta mata. "Lafiya alau boka ya mugun halin matarka? Don ni dai ba zan ce ga abin da ta yi mini na laifi ba, amma wallahi yadda take kwa e fuska kamar kunu kullum babu fara'a, ya sa nake mata kallon mai mugun hali." Ido ya zuba mata yana kallo, ya saki murmushin gefen baki saboda idan ba ka san halin Inno ba, sai ta a ta maka rai a banza. "Inno wata magana na ji, a gaskiya ba zan lamunci ki yi zaman aure da mutumin da ba a tantance jininsa ba." Tun da ya fara magana take kallonsa a gwasale, sai da ya gama ta ce. "Ubanka Iro ma haka ya gan ni ya yale ni, wallahi bokan turai ka shiga taitayinka tun ban yi maka iyaka da angarena ba." Hannu ya saka a aljihu ya ebo wasu ku i masu kauri ya mi a mata. Ino ta kar a tana zuba kabbara. "Allahu akbar kabiran, wato boka ni fa inda kake burge ni kenan. Akwai ka da kyauta har ka fi uwarka mi a hannu, dama ba zan saka Iro ba don babu abin da ubanka yake ba ni." Dariya sosai Fadil ya yi, musamman da ya kalli gwangwanayen madarar da ke kan firjinta, ya tuna gorin da Inno ta yi masa ta ce mahaifinsa ne ya kai mata. Yana shirin yin magana ta ce. "Ka ga idon nan, tun jiya yake yi mini rawa. Ni dama na san ko dai ku i zan samu ko kuma ba i zan yi." Ha a ya ri e yana kallon Inno ya ce. "Kenan saboda fatar idonki tana rawa sai ki samu ku i ko ki yi ba i? Inno me ya sa har yanzu ba za ki watsar da camfe-camfen nan ba? A kimiyance fa ba haka abin yake ba, babu dalili da zai sa don fatar idonki tana rawa ki samu ku i duk camfi ne. Kuma dama duk abin da ka camfa shi, za ka ga yana tabbata kamar yadda tsafi yake gaskiyar mai shi." Inno ta yi kicin-kicin da fuska ta ce, "Kana nufin arya nake kenan? To ba ubanka Iro ba, ko yayan uban Inusa bai isa ya karyata ni ba, ku da komai na ku sai kun sako iyayi da tsurfar aryace- aryacan yahudawa." Fadil ya an girgiza kai ya ce, "Allah da gaske Inno duk camfi ne, a kimiyance fa wasu dalilai ne suke haddasa haka. Har ka ji tsokar jikin mutum, ko wani sashe na jikinsa yana rawa wato (twitching) a kimiyance mu ce nervous ticks. Dehydration, wato bushewar jiki da arancin ruwa a jikin mutum yana haifar da haka. Akwai yawan shan abubuwa masu auke da caffiene , wasu a angare ci ko sha zuwa yawaita shan magunguna hana zugi barkatai, ba tare da shawarar likita ba. Musamman magungunan da za ki ji ana kira da ciwo goma, ko ciwo takwas. Haka idan sinadarin ara arfin ashi wato vitamin D, da vitamin E na rage dattin jiki zuwa calcium suka yi aranci, duk zai iya janyo wani sashe na jiki ya dinga rawa. Akwai kuma rawar hannu, da za ka ji haka kawai hannunki yana rawa. (Neurological disorder) Ana iya gadon rawar hannu, kamar idan iyaye da kakannin suna yi. Shi ma kuma, akwai wanda wani dalili yake saka haka." Inno ta shiga tafa hannu a tsorace ta ce, "Wallahi ni dai a kaf zuri'ar dangin uwata da ubana babu maye ko mayya. Don haka babu ta inda Iro zai gaji maita, ballantana ya haifo maye sai dai ko a can dangin uwarka. Ni kake cewa ban da bitamin a jikina boka? An ya a makarantar da ka yi karatun likitancin nan, ba su sayar maka da maita ba?" Yadda ya ga Inno ta tsorata ne, ya tabbatar masa da gaske take fa ar maganganun har cikin zuciyarta. Ya saka hannu ya dafe kai ya ce. "Haba Inno don Allah ki fahimce ni, ni fa ba haka nake nufi ba. Ina yi miki bayanin abin da yake kawo motsin wani sashe na jiki ne, kamar yadda kika ce fatar idonki tana rawa." Shiru ta yi tana kallonsa a gwasale, ganin haka ya sa Fadil ya cigaba. "Inno har yawan rashin hutu ko wadataccan bacci yana haifar da haka, haka fargaba ko damuwa duk suna cikin abin da yake janyowa.
Chapter 23 · 0% Book details