← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 69

Sashe 38

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA Cikin karayar zuciya da acin rai wasu tagwayen hawaye suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake wace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ullin kayan Lami da ke aure a ankwali. Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana fa "Lami kin san irin so da aunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan arfi da yaji? Matu ar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne." Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya ha a da na mai sunan malam ya rungume a irji sai ya sake arkewa da kuka. "Don Allah ki ha ura da yajin nan da za ki yi Lami. Matu ar naman auri ne zai datse igiyoyin so da aunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki al awari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin aurin nan Lami." Lami ta ta e ba ki sannan ta ce. "Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta are, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin auri ballantana na saka rai da an akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture..." Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta. "Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?" Lami ta sake ta e baki ta furta. "Ai a banza man kare, tun da a haihuwar anka na fari guda a ce abin auri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta sa u ba bindiga a ruwa." Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure ha e da aga hannu sama ya ce. "Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa." Lami ta an saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce. "Wai ina Lami take?" Da sauri Lami ta amsa. "Ga ni mana." "A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya." Sai da ya kalli hagu da dama ya yi asa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. "Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki." Da sauri Lami ta washe baki cikin zumu i ta furta. "Uwar garke fa..." "Ki yi asa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?" Baba Isuhu ya katse ta da sauri. an Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa'a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka auke mata uwar garken nan." Lami ta yi maganar murya can asa zuciyarta fes. "Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo." Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya. "Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke 'yar da i miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki..." Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, "Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi." Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. "Hmmm namiji kenan! Ke yanzu da in bakin namiji har zai sa ki zauna..." Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala ra a a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta. "Ke 'yar nan da gaske?" Lami ta gya a kai tana murmushe. "Haba ko da na ji wannan ita ce harkar arzi i, ko ni anwar uwarki ai na samu na lasa wa a bakin salati. Ni fa kin san ni dama na fi kwarkwasa kwa ayi, duk wurin da ake samun mai mai o-mai o a nan na fi arfi." Lami ta yi gaba tana tafiya cikin wambo tana jin ita ma ta isa, kuma ta tabbata matu ar aka wayi gari da an yi mata auri da tinkiya ta san daraja da imarta ta aru a idanun facalolinta. CIKIN DARE A hankali Uwani ta bu e idonta sakamakon jin fitsarin da ya zame mata kamar farilla cikin talatainin dare, sai da ta gama murtsike idanu sannan ta fara tashin Dada. "Dada! Dada don Allah ki tashi ki raka ni fitsari nake ji." Dada cikin takaici ta saki dogon salati sannan ta ce. "Ni kam wallahi Dijen Iro ta cuce ni da ba ta gashe miki mara tun kina zanin goyo ba, wallahi Uwani ki kiyayi ha in tashina tsakiyar dare da kike yi..." "Dada kamar kukan uwar garke nake ji." Uwani ta katse Dada cikin sauri tana sake kasa kunne, don sama-sama take jin kamar kukan dabbobinta kasancewar suna da an nisa da sashen Dada. Dada ta yi mata shiru saboda takaici. "Dada don Allah ta shi mu je ko wani abu ne yake damun su..." "Ai wallahi ko Umaru ne ya dawo daga Lahira bai isa ya fid da ni waje ba, tun wuri ki kama 'yan matan afafuwanki ki yi gaba." Jin takaicin abin da Dada ta fa a ya sa Uwani tashi fuuu ta suri buta ta yi waje. Tamkar sabon munafiki haka Baba Isuhu yake tafe cikin san a yana waige har ya arasa sashen da awakin Uwani suke, sai da ya karkace ma ogaro ya ma e murya kamar yadda Uwani ke yin magana sannan ya ce. "Uwar garkeruruna tayya maza mu je ki ci dusa." Shiru ya ga uwar garke ta yi babu alamin za ta motsa, ganin za ta ata masa lokaci ya sa ya ago ta ya fara ja a hankali. Sai da ya arasa bakin katanga sannan ya taka turmin da ke jingin, sama-sama ya an fara jiyo motsi don haka ya yi kasake. A angare aya irjinsa na bugawa don kada uwar garke ta yi kuka asirinsa ya tonu. Yana ra e a gefen katanga ya ga Uwani ta wuce da buta a hannu sannan ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya, tirmi ya taka a hankali ya le a ya hango Mai gari da ke tsaye yana jiransa. "Haba Isuhu tun azu auko tinkiya ya gagare ka, ko so kake asirinmu ya tonu mutumcina ya bi rariya ya tsiyaye tas a garin nan ina matsayin mai garin garin nan." Baba Isuhu ya yi asa da murya ya ce. "Kai Talle ka san dai fita da uwar garke ta ofa ba zai yuwu ba saboda tsaro, yanzu ga ta ka matso zan cicci o maka ita." Da sauri Mai gari Talle ya matsa jikin katangar. Baba Isuhu ya koma wurin Uwar garke da ke cin dusa, ya tattaro iya arfinsa ya ago ta sai ji kake aaaarrrrrrr wata uwar tusa ta wace masa. Uwani da kawo kanta kenan ta saki murmushi ta ce. "Kai da jin wannan tusar ka san su uwar garke bacci ya yi da i." Har za ta gota sai ta le a garkensu, sai dai haskarwar da ta yi babu uwar garke babu alamunta. Da sauri ta juyo tana shirin fasa ihu ta hango Baba Isuhu rungume da uwar garke, ita kuma uwar garke jin matsar da Baba Isuhu ya yi mata ya sa ta ware baki ta ce. "Meeeeeeeeehhh." Cikin sauri Baba Isuhu ya mi a wa Mai gari Talle, Mai gari na kar a ya fara kici-kicin hawa mashin. Uwani na ganin Baba Isuhu ya mi a uwar garke ta yi caraf ta kama katanga, sai dai tana gani Mai gari shi da wani da ba ta gane fuskarsa ba suka haye mashin suka fita da gudun gaske. A haukace Uwani ta diro daga kan katangar ta ora hannu a kanta cikin tashin hankali ta ce, "Wayyo Allah uwar garkena." Sai kuma ta yi sashen Dada a guje. Ganin haka ya sa Baba Isuhu da sauri ya nufi sashensa. A tsakar aki ya sami Lami don haka tana ganinsa ta ce, "Ya dai Isuhullena an dace kuwa?" Baba Isuhu da ke faman haki ya ce, "Maza ki tafi aki ki kwanta, ni ma lamfo zan yi shegiyar yarinyar nan ta kama mu ni da Talle." Zaro ido waje Lami ta yi ta ce, "Mun shige su Isuhuna ya za ka yi?" "Babu lokaci Lami ke dai ki je ki yi yadda na ce miki." Lami ta yi saurin ficewa shi kuma Baba Isuhu ya fa a uwar aki ya haye gado sannan ya fara sauke numfashi kamar wanda ya jima yana bacci. "Wayyo uwar garke." Uwani ta furta ha e da arkewa da matsanancin kuka. Ganin Dada na sakin bacci har da minshari ya sa Uwani ta buga tsalle ha e da fa in. "Wayyooo uwar garkena!" Sai a lokacin Dada ta ji ihun Uwani. "Kai ni kam Mamman ya cuce ni da ya ha a Uwani da kiwo tun tana anuwarta. Yanzu ban da masifa a ce yarinya har cikin bacci tana ambatar tinkiya, wannan bala'in da me ya yi kama..." Dada ba ta arasa magana ba ta ji Uwani ta fa i a gefen afarta tim! Ta fashe da wani irin matsanancin kuka. A razane ta tashi zaune sannan ta kai hannu ta kunna fitilar akin, hannuwa biyu ta sa ta dafe irji a firgice Dada ta furta. "Uwani ke ce nake gani a gabana ko bu e mini ido aka yi?" Uwani ta ji tamkar
Chapter 38 · 0% Book details