Sashe 43
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
tsoratarwa sannan ta ma e murya ta ce. "Gani gare ki Goggo Sala, ki nutsu ki saurari abin da zan fa a miki domin zai yi miki amfani a matsayinki na jinsin bil'adam." Nan take jikin Goggo Sala ya auki karkarwa kamar mazari, hannu biyu ta sa ta fara kiciniyar goge kumfan fuskarta amma yajin sabulu ya hanata bu e ido. "Nan wurin da kike wanka masarautarmu ce, kuma kina tsaye ne akan karagar shugabarmu ga hadimanta nan sai zagaye ki suke yi. Wani abin haushi kin saka su kallon tsiraici, don ma Allah Ya taimake ki aljani Manu an kwarto ba ya kusa da tuni ya haike miki." Jin haka ya sa Goggo Sala ta fashe da kuka, Uwani ta gimtse dariyarta ta cigaba da cewa. "Ni ce uwar garke wacce kika dafa namanta, to yanzu haka na dawo domin ni dama ba tinkiya ba ce. Kuma namana da kika dafa a tukunya na auke shi na kai garkena, sannan zan kafa miki wani shara i matu ar kika sa a masa zan auke ki zuwa duniyarmu." Goggo Sala baki na rawa ta ce. "To Babata uwar garke fa i kowanna shara i ne ni mai biyayya ce a gare ki." Uwani ta sa hannu ta toshe dariyarta ta ci gaba da cewa. "Shara in shi ne kullin za ki dinga goya Isuhu sau uku a rana, safe, rana da kuma dare. Idan kika zo goya shi ki dinga yi kina lasar baki, kuma idan kika kuskure koda na lokaci aya ne ba ki yi ba take zan auke ki ko kuma na tsotse romon kanki." "Wallahi zan yi ba dai goyo ba, ko har da Lami aka ce zan ha a na goya su." Goggo Sala ta fa a cikin kuka. "Kin taimaki kanki, yanzu kayan da kika cire zan kai shi garkena amma zan bar miki ankwali, kuma kada ki kuskura ki fito sai an kira sallar Isha'i domin anfara tattaunawar fadar aljanu da ke. Sannan an autan shugabanmu ya ce da baya da baya za ki tafi aki kina cewa nasara a kanku Isuhu da Lami." Goggo Sala ta amsa, a zuciyar tana da-na-sanin zuwanta zaman da aro gidan Lami. Uwani na gama maganar cikin san a ta koma har lokacin baba Isuhu yana akin don ta hango shi ta cikin labule, ta ra e a gefen ofar akin ta karkace murya ta fara kukan tinkiya. Shiru ta ji sun yi sannan ta yi wani gurnani tana yi tana buga afa irin tsalle-tsallen da awaki suke yi. "Shi kenan Lami ta zo ina jin tafiya za ta yi da ni." Baba isuhu ya fa a cikin kuka. "Ba zan tafi da kai yanzu ba. Ni uwar garke ni ce na aiko maka da sa azu. Ku bu e kunnenku da kyau, uwar garke ba mutum ba ce. Na zo na kafa muku sharu ana idan kuka bi su zan yafe muku zunubin da kuka aikata mini, idan ba haka ba kuma a gabanku zan yi farfesun mai sunan malam na saka ku cinye shi kuma ku shanye romonsa." "Wallahi ko mene ne kika ce mu yi za mu yi miki biyayya." Lami ta fa a a tsorace. "Kai Isuhu da farko taimakonka za mu fara yi kafin ka ji shara inmu. anwar mahifiyar matarka babbar matsafiya ce a oye, kuma dama da biyu ta zo zaman da aro gidanka. Idan kuma ka yi yun urin korarta za ta halakaka da iyalinka gaba aya. Daga gobe ne wa'adin aikin da take yi a kanka zai fara, don haka yanzu ma za ku ga ta fito tana tafiya da baya-baya tana ambatar sunanku don haka kada wanda ya tanka mata. Kuma gobe za ta zo da sassafe ta ce maka za ta goya ka. Duk rintsi kada ka bari ta ta a maka jikinka." A zabure Baba Isuhu ya ce. "Goyo fa? Ni Isuhu za a goya da giramana ban da iskanci?" Uwani ta katse shi. "Idan muna magana ba a tankawa. Sannan Shara in da za mu kafa maka ya zama wajibi ka auki rigunan mama na Lami guda uku ka kai wa mahaifiyarka Dada ka ce ta saka su..." "Dadar ce za ta saka bireziya..." Baba Isuhu ya furta cikin su utar baki. Uwani ta buga masa tsawa cikin gurnani ta ce. "Idan ka sa a mana wallahi sai mun hallaka ka da kisa mafi muni." Nan take Baba Isuhu ya ce. "Duk abin da kika ce na bi Inna uwar garke." "Na dawo gare ki Lami. Ke kuma akwai dafin da Goggo Sala ta saka miki a ruwan wanka wanda wa'adinsa gobe zai cika, ko ba kya ganin irin maganin da take zuba miki a ruwan wanka kullin?" Da sauri Lami ta gya a kai. "Idan kika sake shayar da ai sunan Malam daga gobe ke da shi mutuwa za ku yi, domin dodonta zai zu e jininku tas." Da yake Lami ta san Goggo Sala da shegen bin malamai nan take ta aminta da kalaman Uwani. "Shara in da zan kafa miki ya zama dole daga gobe ki dinga aukan mai suna Malam kina kai wa Jafar shi yana shayar da shi a sashen Dada." Cikin ha in baki Lami da Baba Isuhu suka ce. "Jafaru kuma? Shi zai shayar da mai sunan Malam?" "To kada ku kai shi dama an autan Go iya kwa ayin romon jariri yake ji sai na dafe masa shi." Uwani ta fa a cikin wata irin murya, don ita kanta dagewa take da tuni dariya ta kwace mata. "Wallahi za mu kai shi, Allah Ya kai mu gobe." Gaba aya suka amsa. "Kuma ya zama wajibi a gare ka, kai Isuhu ka saka arfi ka danne Jafar domin a shayar da mai sunan malam idan ba haka ba komai zai iya biyo baya. Kuma shara in da zan kafa muku na arshe ko da wasa kuka fa i abin da ya faru tsakanina da ku, sai na sa wu ar aljanin mahauta ya ya e fatar jikinku sannan na auke ku zuwa duniyarmu a azabtar da ku kamar yadda kuka azabtar da ni." Uwani na daga tsaye ta fara jiyo shasshekar kukan Baba Isuhu. Sai da ta lalla a ta auke tukunyar naman da aka yi farfe su ta ajiye a soro sannan ta ce. "Tukunyar namana da kuka dafa ku same ta a wurin garkena, kada wanda ya fito har sai an kira sallar isha'i domin tuni an zauna zaman fadar aljanu da ku. Kuma idan kuka bari namana da kuka dafa ya kwana a garkena cikin dare zan gayyato tawagar jinsinmu su auke mini ku." Uwani na gama maganar ta fara kukan tumaki tana wani irin dire-dire sannan ta auki tukuyar ta tafi a hankali, kai tsaye ta wuce garken awakinta. Da yake duhu ya yi awakin Uwani duka sun kwanta, a hankali ta isa turken uwar garke ta ajiye tukunyar. Ta janyo igiyar uwar garke ta sa ale a jikin afar tukunyar, zuciyarta fes ta wuce sashen Dada don ta yi sallar magriba tana tafe tana dariya kamar sabuwar kamu. Har alla-alla take gari ya waye ta ga irin diramar da za a tashi da ita. A lokacin da ta shiga akin Dada Jafar na zaune ta kofin shayi a gefensa , ga laptop a gabansa yana dannawa, dawowarsa daga masallaci kenan. Uwani na are masa kallo ta tuntsire da wata mahaukaciyar dariya, domin yanayin zaman da ta ga ya yi ne har ta hango yadda Baba Isuhu zai danne shi a shayar da mai sunan malam. agowa ya yi ya kalle ta sai kuma ya ci gaba da danna laptop insa, Uwani ta sake kallonsa ta ga yadda yake jin magani sai kawai ta tsugunna a wurin tana she a uwar dariya. "Uban me kike yi wa dariya?" Jafar ya furta a da ile. Tamkar wacce ya sake ingizawa, sai Uwani ta sake fashewa da dariya har da hawaye da ta tuna duk irin ha e fuskar da yake yi wai shi za a danne a shayar da mai sunan malam. "Ba tambayarki nake yi ba?" Jafar ya buga mata tsawa. "Dama wani wasa ne muka fara bugawa ni da awata Lantana shi ne na shirya mata yadda zan cinye ta gobe." Uwani ta yi maganar tana an murgu a baki. "Ba na son shashanci idan wannan iskanci za ki yi ki fice mini ba na son hayaniya." Uwani ba ta kula shi ba ta gimtse dariyarta ta shige uwar akin Dada. Ku kawo wa Jafar auki zai shayar da mai sunan malam 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam [08/06/2024, 11:39] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*