← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 69

Sashe 22

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel inmu. SHAFI NA TARA A madadin Mai Yasin ya saki Yaya Inu ya yi ta kansa, sai ma ya sake ame shi ta baya ya ma ale murya cikin arfin hali ya ce. "Haba Mai gida me kake son mayar da ni?" Sororo Yaya Inu ya yi jin abin da Mai Yasin ya fa a, sai ya fara zargin ko dai shi ne bai shafo daidai ba, ko kuma hannuwansa ne suke yi masa gizo. Don haka ya sake lalubo Mai Yasin ya ji asunbarsa ta masa abe- abe, ya shafa gefen cinyarsa ya ji gajeren wando. A zafafe cikin zafin nama, ya kai masa naushi a fuska yana fa in, "Mai gidan ubanka, an iskan kwarto. Jama'a a kawo auki." Ganin da gaske asirin Mai Yasin yana shirin tonuwa, ya sa shi fita a guje; shi ma Yaya Inu ya rufa masa baya. Sai da suka je tsakar gida Yaya Inu ya fisgo gajeren wandon Mai yasin, saboda babu riga a jikinsa idan ba haka ya yi ba zai iya kama shi har ya cim masa ba. Ganin dumu-dumu ya shiga hannu sai Mai Yasin ya zage iya arfinsa ya barke wandon ya rabe biyu, ya fita a guje saboda tashin hankali a tsammaninsa sashen Inno ya nufa. Ba tare da ya ankara ba, ya haye katangar sashen Labaran ya dira. Cikin akin ya fa a a guje jikinsa har karkarwa yake yi, yana jin sa a kan katifa ya ja bargo ya rufa gumi yana keto masa. Labaran ne ya fito daga zagayen wurin da suke tsugunno, sai da ya ajiye butar a ofar aki sannan ya shiga ya bu e randa ya sha ruwa, ya arasa gefen gadon Rahinatu. Murmushi ya saki a fili ganin mutum ya gangaro wurin kwanciyarsa, a tsammaninsa Rahinatu ce. Cike da shau in soyayya ya furta. "Rahinatuwa kenan! Bari na gyara ki da kaina, don kada na katse miki bacci mai da i." Ya arasa maganar cikin tattausan lafazi mai ha e da soyayya, sannan ya saka hannu ya gyara hannun Mai Yasin da gumi ya gama wanke shi, ya yi mamaki sosai da ya ji hannun kamar ba na Rahina ba saboda ita mace ce mai iba sosai. Da yake akin babu haske sai ya bar abin a ransa ya ra a ta gefe ya kwanta, sauke hannunsa da zai yi a gefen Rahinatu ya ji ana karkarwa ga gumi ya ji e shi. irjinsa ne ya buga da arfi, a sanyaye ya ce. "Rahinatu lafiya kuwa? Me yake damunki na ji kamar kina rawar ari " Daga can gaban Mai Yasin, Rahina ta ago tana an yanutsa fuska ta ce, "Baby lafiya kake magana da tsohon daren nan?" Da sauri Labaran ya zaro ido waje, saboda Mai Yasin a tsakiyarsu yake. Labaran shiru ya yi ya sake sa a hannu ta cikin bargo ya shafo afar Mai Yasin ya ji, don ya tabbatar da ba aljani ne ya jawo masa hari ba. Saboda a fitar da ya yi fitsari a tsammaninsa indai ba aljani ba, babu wanda zai shigo masa ba tare da ya ji arar bu ofa. afar Mai yasin ya shafo ya ji 'yan yatsu irin na shi sa anin kofato da ya yi tsammani, sai ya kai hannu ya shafo kansa. Mai Yasin ya ma ale murya ya ce, "Masoyi kada ka yarda da ita ni ce ainihin matarka." Ware ido Rahinatu ta yi don sai a lokacin ta lura da mutum a kusa da ita, jin furucin Mai Yasin ya sa Labaran ya shafo asunbarsa, ya lalubo irjinsa sai ya ji shi wayam. "Kai la'ananne sai na kashe ka, garsamemen ato a gefen Rahinatuna! weeeeeeeeee huuuuuuu." Labaran ya furta a haukace ha e da yin gurnanin da ya razana Mai Yasin, hakan ya sa ya banka e bargo ya fita da gudu Labaran ya rufa masa baya. Cikin shammata Mai Yasin ya juyo ya yi masa mahangur a a fuska, cikin tsananin jin azaba ya zube a wurin. Rahinatu ta fito tana ihu da kururuwa, a haka Mai Yasin ya samu ya cire sakata ya fice. Ya fita kenan Yaya Inu ya sako kai cikin sashen Labaran, ya shiga wuri-wuri hannunsa auke da barandami da kokara. A haukace Labaran ya fisge daga hannun Rahinatu ya cakumi wuyan Yaya Inu yana fa in, "Wallahi yau ko ni ko kai a gidan nan, tun da ka nemi gwada mini kwartanci." Yana fa in haka ya kai wa Yaya Inu naushi a baki, jin zafin haka ya sa Yaya Inu ya watsar da kokarar hannunsa ya falla wa Labaran mari, nan take suka shiga kiciniya Rahinatu ban da ihu babu abin da take yi. Kafin wani lokaci tuni iyalan Yaya Inu sun cika sashen Labaran, da yar aka raba su kowannensu yana mayar da numfashi. "Kai Labaran idan ka bari na ri e ka wallahi sai na sumar da kai, shashasha wanda bai san ciwon kansa ba." Yaya Inu ya yi furucin yana buga tsalle, kamar zai wace daga hannun su Bashar. Labaran ya ji wani takaici ya lullu e shi, don gani yake Yaya Inu ya gama cin tuwo a kansa, saboda maganar da yake yi masa kamar an dake shi ne kuma aka hana shi kuka. Ya zabura a hassale ya ce. "Ka dai yi asara Inusa, ka ajiye ri a-ri an mata amma kana bibiyar matan wasu, wallahi idan gaba aya mutanen garin nan gatanka ne, sai na auki ha in iyalina da ka shiga har cikin turakar sunna kake arin aikata fasadi." Shiru kowa ya yi, cike da mamaki Hansatu ta ce. "Kai Labaran kana nufin bayan sashenmu kai ma an shigo maka? Yanzu fa ihun Mai gida ne ya taso mu." Yaya Inu ya ago gajeren wandon Mai Yasin ya ce, "Wannan shi ne abin da na samu daga jikin kwarton, kuma wallahi sai na kai wa Mai gobe da nisa ya saka shi a bala'in da bai ta a zato ba." Sai a lokacin jikin Labaran ya yi sanyi, kunyar yayansa ta kama shi, suna shirin watsewa suka jiyo ihun Inno a angarenta. Kamar ha in baki lokaci aya suka bi sashenta sai dai ofar a rufe suka same ta, Yaya Inu ne ya kama katangar ya dire sannan ya bu e wa ragowar ofa. A tsaye suka samu Inno butar hannunta ta tuntsire a bakin ofa ruwan cikinta ya zube, Inno tana ganin su Yaya Inu ta ri e su jiki yana rawa ta ce. "Inusa wani ya shigo gidan nan, don yanzu haka na fita fitsari na ga giftawarsa da gudu. Babban tashin hankalin ma, gamo na yi domin zir insa haka yake ko bante babu." Ba su saurari jin ta bakin Inno ba suka fita da gudu suna haske-haske, Mai Yasin ya yi tsumu-tsumu a aki yana saka kayansa, ya yi lakur a kan katifa yana mayar da numfashi. Sai da suka yi binciken duniya amma ba su gan shi ba, suna cikin haka Mai Yasin ya fito yana tambayarsu kamar bai san abin da ya faruba. Labaran ne ya yi masa bayani, bayan ya gama Yaya Inu ya ce. "Ai na yi mai wuyar tun da na samu tufafinsa, zan sa Mai gobe da nisa ya yi mini aiki mai zafi a kansa. Dama abin da yake bu ata takalmi ko wani abu da aka samu daga jikin arawo ko kwarto, wallahi daga wannan karon ba zai sake haurewa gidan wani ba." Jin haka ya sa cikin Mai Yasin ya ka a, wani zazzafan gumi ya yanko masa. Ya arasa gaban Yaya Inu ya ri o hannunsa da ke karkarwa ya ce, "A'a Inusa ka bar mini komai a hannuna, ka san dai kamar yadda na fa a muku zafin aikina ne ya sa ake kira na da Mai Yasin. To ni zan..." Kallon da Yaya Inu ya shiga wurga masa ne ya sa shi katse kalamansa, don yadda ya ga yana kallonsa har sai da ya sa shi tsarguwa. "Ka bar mini komai a hannuna, ni na san irin shige da ficen da nake yi a wurin malamai, don haka zan ji da shi." Jiki a sanyaye kamar zakaran da ya shuri wu a, Mai Yasin ya ja jiki gefe. Yaya Inu ya fice yana muzurai, babu jimawa kowa ya watse. Ganin duk irin gudun da Mai gari yake fallawa su Mahmud ba su daina bin sa ba, ya sa shi arkewa da kuka yana gudu yana waigensu. Ba shi ya tsaya ba sai da ya arasa tukubar tsiren Mai daban-daban, yana shiga rumfar a guje ya yi bayan su Haladu da ke zaune a kan benci. Zumbur! Suka mi e, cikin damuwa Sallau ya ce. "Subhanallah! Ranka shi da e lafiya kuwa? Me yake faruwa daga kai sai gajeren wando?" Kafin Mai gari ya bayar da amsa su Mahmud suka arasa cikin runfar, ganinsu ya sa bakin Mai gari ya shiga karkarwa hannu yana rawa ya nuna su ya ce. "Su... ne, wallahi ba... mutane ba ne. Ku taimaka..." Bai arasa maganar ba ya yanke jiki ya fa i, cikin su Mahmud ya sake ka awa don Mudassir tuni ya fara hawaye, ya dubi Mahmud ya ce. "Mahmud ka janyo mana masifa muna zaune alau." Sai ya sake arkewa da kuka, hawayen da Mahmud yake ri ewa ne ya alle ha e da wanke fuskarsa lokaci aya. Sun juya za su fita da sauri Mai daban-daban ya dan o wuyan rigarsu yana fa "Billahillazi la'ilaha'illahuwa sai kun tsallaka mai gari, kai babu wanda fa zai bar wurin har sai mai gari ya dawo hayyacinsa." Su Mahmud suka yi tsilli-tsilli irjinsu yana bugawa. "Wallahi a aure su har sai ranka shi da e ya dawo hayyacinsa, idan ba haka ba sai
Chapter 22 · 0% Book details