← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 69

Sashe 64

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kayanta ba. Lokacin da aka kira sallar magriba Uwani wucewa ta yi sashenta don ya gabatar da sallah, tafiyarta babu jimawa Mami ta zagaya ta ga wurin wayam. Sai tsirarin kayan da ta shanya ga wa ansu nan a cikin ruwa. Uwani na zaune tana zaman tahiya Jafar ya shiga ya zaune yana kallonta, a yadda ya lura da Uwani duk hatsabibanci da iriniyarta ba ta wasa da sallah ko ka an. Hakan ba aramin birge shi yake ba, yana nan zaune Mami ta shigo ko shi ba ta yi wa magana ba ta rufe Uwani da duka. Ganin dukan da take wa Uwani ba zai are ba ya sa Jafar ya yi saurin shan gaban ta. "Lafiya kuwa Mami? Me ta yi miki haka?" Jafar ya furta hankali a tashe. "Lallai Jafar wannan abar har kake tarewa?" Mami ta fa a tana sauke numfashi. Ban da kuka babu abin da Uwani take yi, ga gefen bakinta ya fashe jini na iga. Saboda yadda ta galabaita kukan da take yi ko fita ba ya yi, Mami ta sake zuba mata ran washi a ka tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Mami wai me ta yi miki?" "Wanki na saka ta don iskanci za ta zube mini ta zo ta saka miji a gaba, idan uwarki ce ta saka ki za ki ajiye mata." Mami ta yi maganar tana dungurin Uwani, cikin kuka Uwani ta ce. "Sallah aka kira shi ne na zo na yi..." Da sauri Mami ta sake doke Uwani nan take bakinta ya sake fashewa. "Haba Mami, ina ce Haladu ne yake yin wanki. Kuma sallah fa ta ce ta zo..." Tas! Mami ta auke Jafar da mari, ba ta tanka masa ba ta figi hijabin Uwani ta fara janta a asa, ba shiri Uwani ta mi e ta bi Mami. Saboda acin rai tun ba su gama fita ba Jafar ya gegare su ya fice daga gidan zuciyarsa na suya. "Iyeee Allah Jafar watsa mini asa za ka yi a ido yaushe har ka san zafin mace. Wallahi dole kai ma na auki mataki a kanka." Mami ta yi maganar a an tsorace don ta yi tsammanin ko wuta za ta jefa Uwani sai dai Jafar ya taya ta ba dai ya hana ba. A cikin duhu ga sauro haka Uwani ta wanke ragowar kayan da ba ta arasa ba, kanta ban da ciwo babu abin da yake yi. Bayan ta gama ne ta nufi sashen Mami har asa ta zube ta furta. "Na gama wankin." A yamutse Mami ta dube ta tana shirin sallamarta Shukra ta shiga akin tana taunar cingam ta ce. "Ke zan saka ki aiki yanzu saura ki yi mini hauka." Uwani ta aga kai a galabaice ta amsa wa Shukra. Auta da ke zaune a gefe duk sai ta ji babu da i, tana son ta yi magana amma tana tsoron fa an Mami. "Kina ji Shukra na yi miki magana ba za ki iya amsawa ba?" Mami ta yi maganar tana haurin Uwani. Sai da ta goge wallar idonta sannan ta rarrafa gaban Shukra ta tsugunna. "Ga Salim nan ya faka motarsa a cikin gate, za ki je ki wanke masa kuma wallahi idan ba ta wanku ba sai kin sake." Da sauri Auta ta furta. "Aunty Shukra wankin mota fa?" Shukra ta sake shan kunu ta ce, "Waya na yi da shi zai kai wankin mota ya ce ba zai samu zuwa yau ba, so don haka na ce ya zo gida za a wanke masa saboda ina son magana da shi." Cikin tausaya Auta ta ce, "To shi kenan zan ta ya ki Uwani..." "Waye ya gayyace ki? Uwar iyayi da kankanba?" Mami ta katse Auta. Shukra ce ta yi gaba Uwani ta bi bayanta a lokacin zazza i har ya fara rufe ta, lokacin da suka arasa Salim na cikin mota. Da ya hango su ne ya fito yana sakarwa Shukra murmushi. "You are welcome dear." Shukra ta furta tana fari da ido. "Beb an ya zan iya jiran sati ukun nan masu zuwa kuwa? Kin ga yadda kika yi kyau." Salim ya furta cikin shau in soyayya, Shukra ba aramin da i ta ji ba kin kissa ta ce. "Well mu je mu zauna, ga 'yar aikin Mami za ta wanke maka mota." "Za ta iya kuwa Baby? Na ga mata ba sa wankin mota." Salim ya fa a yana bin Uwani da ke raka e a gefe. Shukra ta dubi Uwani a tsawace ta ce. "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?" Jikin Uwani na rawa ta tsugunna ta gaishe da Salim, sannan Shukra ta an yi murmushi ta furta. "Ai in gaya maka daga motar Daddy har ta ya Jafar ita take wankewa za ka sha mamaki." Shukra da Salim suka wuce wurin wasu fararen kujeru, daga wurin da suke zauna suna iya hango Uwani da duk abin da take yi. Sai da ta goge wallar idonta sannan ta auki bokiti ta fara ebo ruwa, da yake wurin iban ruwan yana da an nisa da wurin wankin motar a galabaice ta fara wankin motar har ta gama. Gaban Shukra Uwani ta je ta tsaya ta ce, "Na gama wankewa." Shukra ta bi ta da harara sannan ta ce. "Matso nan." Ba musu Uwani ta matsa gaban Shukra, da arfin tsiya ta fisgo Uwani har sai da ta bugu da aramin table in da ke gabansu ta ce. "Don ubanki ke ba ki da ladabi ba za ki iya tsugunnawa ba?" Shukra ta arasa maganar tana zuba wa Uwani ran washi. "Haba Beb da kin yale ta kin san irin yaran nan ba wani tarbiyya suke samu ba, so don sun yi haka ni ba zan yi mamaki ba." Salim ya fa a a yamace yana duban Uwani da ta gama ji e wa da ruwa sharkaf. "Dallah tashi ki ba ni wuri kina tafe da ba i kamar na zunubi." Dariya sosai Salim ya yi jin abin da Shukra ta fa a ya furta. "Wai yaushe kika koyi masifa ne love?" "Haba ka rabu da ni na tsani yarinyar nan wallahi." Uwani na la e a ta bayan fulawiyin da ke zagaye da harabar gidan, takaici ya mamaye zuciyarta. Wani tunani ne ya fa o mata don haka da sauri ta zagaya can bayan gidan, ta ebo irin manyan bokitan fentin nan guda biyu wa anda ta gama wanki da su. Sai da ta yagi wata igiya ta ha a hannuwansu ta aure, sannan ta saki murmushin mugunta. Cikin san a ta fara tafiya ta cikin fulawoyi, a daidai bayan su Shukra ta tsaya ta ji Salim yana fa "Haba ke dai Baby ba kya mantuwa, wannan fa mahaukacin ma shammatata kawai ya yi amma yadda nake aunarki akwai abin da zan ga zai cutar da ke na gudu ban taimaki rayuwata ba, ke ce fa rayuwata ke ni fa idan za ki rayu da farinciki zan iya sadaukar da komai ciki kuwa har da numfashin da nake zu a." Shukra ta rangwa a kai cikin farinciki, tana shirin ba shi amsa Uwani ta saki murmushi duk da zazza in da ke jikinta. Sai da ta daidaita saitin kansu sannan ta aga bokitan fentin hannunta, ta kifa musu a kansu ta saka iya arfinta ta danne saman ta yadda ba za su iya fisgewa ba. Salim da abin ya ha e masa biyu ga zafin hula ga na bokiti ya ware murya cikin ihu ya ce. "Wayyo Allah wuyana!" "Wayyo kaina, Baby kana ina!" Shukra ta fa a a imauce. Daga Salim har ita sai aga hannuwa suke cikin neman taimako. Sai da Uwani ta ga sun fara galabaita sannan ta fisgo hannun bokitin ta baya, da yake afafuwansu na asan table in da ke gabansu fa uwar da za su yi ta baya sai suka taho da table in da afafuwansu. Uwani na ganin za su kai asa ta yi saurin matsawa a guje, sai ji kake rugugum! kacacar kofuna da ruwan jarkar duka sun watso kansu. Ga bokiti ya sar afe su ga kuma afafuwasu sar afe a cikin table, Uwani ta la e a cikin shukoki tana dariya asa- asa don duk war mutum ba zai gano da mutum oye a wurin ba. Da yar Salim ya samu ya zaro afarsa daga cikin Table, ya tashi zai zuba a guje Uwani da ke la e ta sake fisgo shi da yake igiyar tana hannunta. Da ar Salim ya koma ya fa i hankali a tashe ya ce. "Jama'a a taimaka mana wallahi jana ake yi." Shukra ce ta yun ura ta tashi a guje saboda tashin hankali ko yun urin cire bokitin ba ta yi ba, ita da Salim suka zuba a guje a daidai lokacin Jafar ya shigo harabar gidan. Turus ya yi ya an fara ja da baya ganin afafuwan mace da namiji suna tafe da bokiti a kai, da yake ba sa ganin gabansu yana ganin sun tunkaro shi ya zube takalmansa shi ma ya shige a guje yana ihun. "Wayyo Allah! Lado kana ina?" Jin ihun Jafar ya sake ru a su Salim, a wannan lokacin Lado ya zagayo da buta a hannu shi ma turus ya yi yana kallon ikon Allah. Da yar Salim ya samu ya cire bokitin kansa, hular ta fa i can gefe. Dama takalminsa na cikin asan table ya jima da fita, iya arfinsa ya tattara ya fita a guje yana fa in, "Jama'a ku duba mini kaina idan yana gangar jikina." Sai a lokacin Lado ya gane shi, ya bi bayansa yana fa "Alhaji ka bar motarka." Lado na arasawa bakin gate ko urar Salim bai gani ba sai agogonsa da links in hannun rigarsa da suka zube a wurin. Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki turo ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala za ki turo 800 Free pgs inmu ya kusa arewa #Ummou Aslam Bint Adam [22/06/2024, 13:32] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*
Chapter 64 · 0% Book details