Sashe 25
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel inmu. SHAFI NA GOMA A zabure Yaya Inu, ya buga tsalle ya dira a gaban Abu da Goggonta da suke shirin fita. Goggo ta ha e rai ta ce, "Kai Inusa, ka ba mu hanya mu wuce. Ciki ne dai Allah Ya raba ta da shi lafiya, don haka muka kawo maka abarka." Yaya Inu saka hannuwa biyu, ya yi bake-bake a bakin ofar ya ce, "Ku je ina? Don Allah Goggo kada ki shiga gonata, saboda akwai ragowar mutumcinki a idona." Ya waiga wurin Abu ya ce. "Wallahi tun muna mu biyu, ki gaggauta auke wancen abin daga cikin gidan nan!" Abu tana shirin magana Indo ta saki shewa har da gu a tana buga cinya. "Ahayye! Allah na gode maka, ai dama Allah ba azzalumin bawa ba ne sai bawan da ya zalinci kansa. Yau ga shi muna ji muna gani, satar kwana da karya dokar Ubangiji ta bayyana a fili mun gani." Indo ta arasa maganar tana sakin dariyar izgilanci. Hansatu ma dariyar take yi ta isa gaban Yaya Inu tana kallonsa a watse ta ce, "Yanzu don Allah mai gida ba ka ji kunyar abin da kuka haifo ba? Ke yanzu Abu ba ki ji kunyar iyayenki da sauran danginku ba? Tir ashi! Yau ake yin ta a gidan nan, abin da muke hange a nesa ya zo kusa da mu. Yanzu mai gida jarabar taka har ta kai ka dinga kusantar Abu tana jinin al'ada?" Yaya Inu da ya gama zuwa wuya a zafafe ya ce, "A gidan uwar wa kika ga na kusance ta tana jini? Ko kin auka ban san hukuncin addini ba." Su Indo suka kwashe da dariya kusan lokaci aya, Hansatu ta kalli wurin da jaririyar take kwance tana mutsu-mutsu ta ce. "Ga shaida can mun gani, ko ba zabiya ta haifa maka ba. Ai an yi wal iya mun ganku, duk munafuncin da kuke yi ashe Allah zai tona muku asiri ba ku sani ba. Ba ni ka ai ba, kowa ya san sai an kusanci mace tana jinin al'ada ake haihuwar zabiya." Abin duniya goma da ashirin ya ha e wa Yaya Inu, ya ha iyi yawu mai aci kamar zai yi kuka ya ce. "Billahillazi la'ilaha'ilahuwa ban ta a aikata wannan anyan aikin ba. Ni fa shi ya sa nake tantama, magana ta Allah a ce duk dangina babu zabiya sai yanzu zan haife ta. Wallahi tun ban kai ku wurin hukuma ba, Abu ki auke yarinyar nan ki kai ta wurin ubanta. Da ma ni da ke babu kare bin damo." Hankalin Abu ya tashi, saboda babu abin da yake aga mata hankali irin ta yi ido biyu da ansanda. Duk da tana da gaskiya, amma haka gumi ya shiga karyo mata, ta arasa ta auki jaririyar cikin arfin hali da barazana ta ce. "Au haka ka ce ko? To kafin ka kai mu wurin hukuma, ni da kai na zan fara kai ararka. Ka san dai ko lokacin 'yan matancin na kai ne mutumin da nake kulawa. Don haka babu wani uban yarinyar nan, idan ba kai ba. Ai na sha fa a maka ka daina satar kwana kana kirana turakarka amma sai ka ce ba haka ba. Ka dinga ko a ni kana ce mini matar so, ni kuma ina jin da i domin na a ta ran su Indo nake biye maka. Sai yanzu za ka ce ba ka san zancen ba, za ka yi bayani a gaban uliya." Tana gama fa ar haka ta yi waje fuu! A fusace. Hansatu ta gyaran aurin an kwalinta, irin aurin ture ka ga tsiya ta ce. "Kai yau Allah na gode maka da ka nuna mini wannan rana. Ayyiriri! Shagali wan dina. Ai gara da ta tafi da 'yarta don wallahi ba zan ri e gayyar tsinuwa ba, yarinya an same ta a tsine ta rayu a ciki cikin tsinuwa sannan a ce za a dire mana ita. Haka kawai muna zaune a kawo mana annoba cikin zuri'a ta kwashe mana albarkatun cikin gida." Daga haka ta wuce cikin akinta, su Indo ma haka. Yaya Inu jiki a sanyaye ya nufi akinsa yana nazarin ba in cikin da Zainab ta dasa masa. A angare aya yana fargabar abin da zai je ya dawo, saboda shi dai ya san bai ta a kusantar mace tana jini ba, satar kwana dai kam ya san yana yi babu adadi musamman idan mace ta ata masa rai. Don ya rama abin da ta yu masa sai ya kira wata macen da ba girkinta ba, musamman Abu ta kwana a akin. Babban tashin hankalinsa, ya yi mata barazana da hukuma kamar yanda ya san tana tsoron 'yansanda amma ya lura ko a jikinta. Zaune yake ya yi shiru yana kallon an Bishir da jijiyoyin jikinsa suka gama yin laushi, ya ja riga ya share hawayensa. Yana jin ina ma yana da ikon dawo da ciwon shalelensa kansa, da tuni ya dawo da shi. "Mai gida zaman nan naka fa ba zai kai mu ba, a ce yanzu tun da aka yi wa yaron nan shayi ba za ka fita kasuwa ba. Ita zara fa ba ta barin dami, don Allah ka tashi ga magungunanka can na ha a maka su." Baba Sale ya ja majina ya ce, "Haka ne Uwale, amma gani nake idan na fita kamar wani abu zai faru da shi. Ban ta a ganin kaciyar da ta lalace haka ba, ki duba fa ki ga yadda take yin ruwa. Yaron nan duk kuzarinsa ga shi nan ba shi da kata us." Ita kanta Uwale arfin hali take yi, don tana nuna rauninta ta san abin da mijin na ta zai yi sai ya fi haka, don haka ta shanye hawayen idonta ta ce. "Haka ne, amma ko ka zauna in ma abin da Allah Ya addara shi zai faru. Shi kuma idan mun ga ba ta daina ruwa ba, sai mu sake kiran wanzan mu yi masa bayani. Tun da maganin wurinka ma bai sa ta ame ba." A sanyaye Baba Sale ya mi e ya shiga aki, ya auko wani aton buhu da ke cike da magunguna. Ya arasa gaban an Bishir ya ce, " an Bishiriri ni zan fita nema." an Bishiri da ya yi lugub, saboda yadda yake jin jiki ya kalle shi da shanyayyun idanunsa ba tare da ya amsa masa ba. Da yar Baba Sale ya iya aga afarsa ya fita Uwale tana biye da shi. Suna fita Fadil yana fitowa bayan sun gaisa ya wuce ya shiga motarsa da ke gefensu. "Au Mai gida na manta ba ka bayar da maganin Shamsiyya ba, kada sai ka tafi ta aiko." Uwale ta furta. Buhun ya bu e ya ebo wasu matsakaitan magunguna a cikin jarkoki guda hu u, sannan ya auko wata aramar roba mai auke da man shafawa na magani ya mi a mata. Ya ago jarkokin guda biyu, ya nuna mata wurin da aka yi bayanin maganin a jikin takardar. "Wannan ki ce mata sai ta ci abinci za ta sha, maganin sanyin mara ne. Kuma sau biyu ake sha safe da yamma, duk lokacin da za ta sha murfi biyu za ta sha saboda yana da arfi sosai." Ya sake auko ragowar roba biyun da yake ba iri aya da wa ancan ba ne ya ce. "Wannan kuma idan ta tashi biyu za ta raba shi, ta sha rabin roba yau gobe ta sha rabi. Shi kuma wannan man zafi ne, na ciwon bayan da ta ce tana yi ne. Za ta dinga shafa shi a bayanta safe, rana da dare. Amfaninsa iya baya ne. Kar ta ji afa ko gwiwa tana yi mata ciwo ta shafa, ba zai yi mata aiki ba. Duka dai bayanan maganin suna jiki, na san kin fahimta abin da ba ta gane ba sai a bari na dawo, saboda ba na son na ba wa mutum magani ya sha ba daidai ba a samu matsala." Duk bayanin da Baba Sale yake yi Fadil yana cikin mota yana jin sa, ba aramin birge shi ya yi ba. Don haka ya fito ya arasa wurinsa cike murmushi ya ce. "Am Baba Sale na ji duk bayan in da kake yi mata, kuma AlhamduLillah ka birge ni matu a. Saboda yadda na ji kana bayanin magungunanka daki-daki cikin a'ida, ta yanda ba zai haifar wa mutane matsala ba." A she e Baba Sale ya dubi Fadil ya ce. "Kai yaro da me ka auki masu magungunan gargajiya? Jahilai ka auke mu ko yaya? Ka ebo tsila-tsilan afafuwanka kamar wailayen lawashi za ka yi mini iyayi." Kunnuwansa Fadil ya ri e ya ce, "Allah Ya huci zuciyarka ba haka nake nufi ba, ka yi abin da ya dace ne shi ya sa na yabe ka. Sa anin wasu masu magungunan da suke sayar da magani babu dosage, mutum ya sha yadda ransa ya so babu a'ida." Baba Sale ya ta e baki ya ce, "Da ka auka maganin asibiti ne ka ai yake da galihu? Masu magungunan ai wasu suna suka tara, kamar yadda a cikin likitocin akwai muna likita. Kai dube ni nan. Sana'ata ba irin ta sauran masu magani ba ce. A yanzu ma idan na samun jari, babban wuri zan bu e na huta da gararanba a titi. Sai na sake inganta su, don ina da burin har jami'an lafiya zan zuba tun da ni dai ka san summun bukumin ne, zo na kashe ka da turanci ban sani ba ballantana na san harkar gwaje-gwaje." Fadil ya saki murmushi, ya yaba masa sosai da sabon tsarin inganta maganin da ya auko, har zai tafi ya waigo ya ce. "Na ji Daddy ya ce an yi wa yaron nan