← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 69

Sashe 19

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sakamakon kuwa irin yayan da za a samu ne. 1. AA +AA = AA, AA, AA, AA (Za a samar da 'ya'ya masu cikakkiyar lafiya.) 2. AA + AS = AA, AS, AA, AS, (Shi ma aure ne mai kyau, kuma babu matsala a lafiyar 'ya'yan da za a haifa, amma bai kai na saman ba.) 3. AA + SS = AS, AS, AS, AS, (Shi ma wannan auren ana iya yin sa, duk da akwai 'yar matsala ka an a kan 'ya'yan da za a haifa. Za su zama AS ne duka, ma'ana carriers) 4. AS + AS = AA, AS, AS, SS, (Akwai matsala, domin za a samu a ko 'ya mai cutar sikila) 5. AS + SS = AS, SS, SS, SS (Akwai matsala sosai domin kusan kaso tamanin 80% na 'ya'ya za su zama masu cutar sikila) 6. SS + SS = SS, SS, SS, SS, (Akwai matsala mai muni, domin dukkan 'ya'yan da iyayen sikila ne, za su are cikin tsanani da wahalar rashin lafiya..." A zafafe Mai Yasin ya katse shi, "Kai Iro ka kiyaye ni, kai yanzu mu za ka zaunar kana nusar da mu gaibu? Waye masanin gobe idan ba Ubangiji ba? Yanzu zurfin da ka yi a yahudancin har ya kai ka fara ja da hukuncin Ubangiji, kana yi masa shisshigi a kan halitar bayinsa? Wane ne kai ban da gajiyayye wanda fushin Allah ka ai zai iya tarwatsawa, wallahi ka dawo cikin hayyacinka, don ba abin mamaki ba ne yanzu Ubangiji ya mayar da kai ragon sallah. Sakarai dube ka a ido kamar mutumin kirki, amma dai kai an yi zindi in bayahu Inno da takaici ya gama cika ta, ta nuna masa hanya rai a ace ra ce. "Fice mini daga aki Iro! "Don Allah Inno..." "Na ce ka fita ko!" Ta katse shi a zafafe. "Shashasha, kai ni dai kam ban san addarar da ta saka na yarje maka ka yi karatun nasara ba tun asali, idan abin da ka fa a haka ne me ya sa ku duk ban haife ku a nakashe ba?" Inno ta fa a cike da masifa, babu yadda ya iya haka Baba Ibrahim ya fita jiki a sanyaye don ba haka ya so ba. Ko ka an auren Inno da Malam bai a Laraba da asa ba, saboda mutuminta ne tun zuwansa gidan yake faran-faran da ita. A cewarsa 'ya'ya da jikiokin Inno tamkar nasa haka ya auke su, dalili kenan da ya sa ya sake mamaye zuciyar Inno tun bai furta mata kalmar so ba. Laraba ganin Inno ta tafi akin Mai Yasin ya sa ta yi zaraf ta auki hijabinta ta nufi wurin mai daban-daban, a lokacin da ta je ya gama gashe mata zabin sun yi jar suya gwanin birgewa. Laraba ta basar kamar gaske ta ce masa. "Mai daban-daban Inno ta ce na tambaye ka, nawa ne ku in aikin naman sai a biya ka." Mai daban-daban ya washe baki cikin jin da in ganin Laraba tana sakar masa fuska ya ce. "Haba Laraba, yanzu saboda ni na fi kowa rashin kara sai na kar i ku in Inno don na yi mata aikin zabi, ai a kanki Laraba babu abin da ba zan iya sadaukar miki ba." Laraba ta fakaice shi ta an ta e fuska sannan ta ce. "Ashe haka kake sona ban sani ba Mai daban-daban?" Mai daban-daban ya mi a mata ledar da ya zuba zabin a ciki ya ce, "Tun farko dama ai ke ce kika i ba ni ha in kai Laraba, amma bakina ai ba zai iya furta irin soyayyar da nake yi miki ba." Laraba ta yi masa murmushi sannan ta tafi gida, sai dai fargaba ce fal a ranta tana tunanin me za ta ce wa Inno, idan ta tambaye ta a inda ta samo nama mai yawa haka. Tun da ta doshi kwanar layinsu ta ga wani matashin saurayi yana biye da ita, ita mamaki ma abin ya ba ta don idan aka cire Mai daban-daban babu namijin da ya ta a cewa yana sonta, saboda duka mutanen garin kallon marar hankali suke yi mata. "Yan mata, don Allah ki tsaya ina da magana da ke." Matashin ya furta yana shan gabanta, Laraba ta an ha e fuska kamar ba ta fahimci me yake son fa a mata ba ta ce. "Malam lafiya kuwa?" Sai da ya gyara gaban rigarsa ya saki murmushi sannan ya ce. "Tun azu da kika wuce na ji kin kwanta mini a zuciyata, to na ga bai da ce na tsayar da ke a can ba shi ya sa na biyo ki zan ga gidanku." Laraba ta an ma ale murya ta ce, "To gaskiya ni dai ina da masoya da yawa, amma ka san dai an ce mace allurar cikin ruwa ce. Kuma yanzu aike na aka yi, sai dai idan na kai aiken ka tsaya na fito." A fili ta lura da yadda matashin ya an tsora ta jin ta ce tana da masoya, amma da ya ga ta ba shi dama sai ya sauke ajiyar zuciya. Laraba zuciyarta al, don ita ma so take ta gwada yadda ta ga su Bushira yayyanta da suke uba aya suke yi kafin su yi aure ko ta ji abin da ake ji. A ofar gida matashin ya tsaya Laraba tana shiga cikin gida ta zura da gudu ta nufi sashen Inno, har a ranta tana fargabar kada ya gudu kafin ta shiga ta fito. A uwar akin ta ajiye ledar ta sake zurowa da gudu ta koma, sai da ta je soro sannan ta tsaya ta an daidaita nutsuwarta tana mayar da numfashi. " an samari na dawo!" Laraba ta furta tana wani kanne ido. Martanin murmushi ya mayar mata ya ce, "Barkanki da dawowa sarauniyata, ni dai sunana Habu kuma ba a auyen nan nake ba. Na zo ne daga ma otan garin nan, ban sani ba ko kin san gidan Malam Lado mai itace?" Laraba ta yi murmushi ta ce. "Wallahi na gane shi, sam-sam ba shi da mutumci. Sau aya na ta a tsinkar masa mangwaro ya kai arata har gaban mai gari, kawai dai na raga masa ne saboda na ga afa aya gare shi." Habu ya saka hanu ya rufe bakinsa ya ce, "Yayan mahaifina ne fa!" Cikin halin ko'in kula Laraba ta ce, "Ita gaskiya ai dama aci gare ta." Shiru ya yi yana tsoron kada ya sake wata maganar ta ce ta fasa son shi, don ya lura kamar ba ta rufa-rufa. Don haka ya basar ya ce. "Na tambayi sunanki an ce sunanki Laraba, amma Laraba ai ba sunan ainahi ba ne." Laraba ta yi fuskar tausayi ta ce, "Sunana Aminatu, sunan mahaifiyata na ci kasan tana haihuwata ta mutu. Ana kirana da Laraba ne saboda ranar Laraba aka haife ni, ga kuma sunan Innata da na ci." Cike da tausayawa ya yi wa mahaifiyarta addu'a, sannan suka ci gaba da hira duk da mafi yawan hirar da Laraba take yi masa shirme da shirirta ne, amma haka kawai ya ji tana birge shi. Tun da ya shawo kwanar layin hasken fitilar motarsa ta haske su Laraba da ke tsaye a ofar gida, suna hira ita da Habu tana ta she a dariya. Ransa ba aramin aci ya yi ba, cike da acin rai ya ja dogon tsaki har sai da matarsa Nabila da ke gefe ta kalle shi ta ce. "Baby lafiya?" Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Nothing!" Shiru suka yi har suka arasa ofar gidan, sai da ya fita ya bu e gate ya koma cikin motar ya shiga da ita cikin harabar gidan, sannan ya yi hanyar fita a zafafe. Saboda ya lura koda Laraba ta gan shi babu wani tsoro ko shakku a tattare da ita. "Baby ina za ka je kuma?" Nabila ta furta, don ta lura da sauyinsa. "Get inside, i am coming back righ now." Bai jira cewarta ba ya fice. Shiru ta yi tana nazari, haka kawai ta ji irjinta ya buga da wani tunani ya fa o mata. Cikin sauri ta ce. "No! It can't be happen!" Ta bu e motar ta auko lapcoat inta da jaka ta rataya sannan ta shige sashensu. "Shiga gida!" Dr Fadil ya furta wa Laraba a tsawace, ta wani kwa e fuska ganin zai yarfa ta a gaban saurayi ta ce, "Zance fa nake yi Ya Fadil." an zaro ido waje ya yi jin abin da Laraba ta fa a masa babu ko shakku. "Idan na sake magana ranki zai aci." Laraba ta fara hawaye rai a ace ta ce, "Wallahi Ya Fadil ka fiye shiga ha ina, kai lokacin da kake soyewarka wa ye ya hana..." Marin da ya sauke mata ne ya sa ta katse ragowar kalamanta, gefen bakinta ya fashe ganin irin ancin da ya yi mata ya sa ta fashe da kuka tana fa awa cikin gida da gudu. "Haba Malam wannan wane irin abu ne haka? Mene ne aibu a maganganun da ta yi da za ka mare ta..." A fusace Dr Fadil ya auke Habu da mari, ya nuna shi da yatse cike da masifa ya ce. "Dama ku ne irin 'yan iskan samarin da suke hurewa ananan yara kunne ko? Idan na sake ganinka a ofar gidan nan, sai na karairayaka na watsar a asa." Daga haka Fadil ya shige gida ya bar Habu ri e da kunci, wafa ya yi ya ja afafuwansa ya bar ofar gidan, a ransa yana jin idan sama da asa za ta ha e ba zai daina zuwa wurinta ba saboda soyayyarta ta yi masa mummunan kamu. A harabar gidan Laraba ta yi zaman 'yan bori ta fasa ihu, kamar wacce ake walewa idanu. Mutane suka shiga fitowa daga angare- angare ciki har da su Inno, takaici ne ya cika Fadil ya yi tsaye ya har e hannuwa a irji yana kallonta. "Ke Laraba lafiya kike ihu da daren nan kamar wacce ta taka 'ya'yan shai anu?" Inno ta fa a a ru e. Laraba ta sharce majina da an kwalinta fuska sha e-sha e da hawaye ta ce. "Ba Ya Fadil ba ne ya koro
Chapter 19 · 0% Book details