← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 69

Sashe 16

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ciwo Baba Sale ya ce, "Kai Labaran kada ka fa a mini maganar banza da wofi, ban da aska da tasha jinin an Bishir ka isa na tako wurinka neman abinci ne? Ka fa a mini ko nawa ne zan biya ka, ka sayar mini abincin nata." Labaran ya buga tsalle kamar mai shirin tashi sama, saboda yadda kishi ya tirni e shi ya ce. "Ba askar kaciya ba Allah Ya sa abba-tuwa ce a kansa, wallahi ba zai ci abincin Rahina ba. Yanzu ni kake kallo ka ce na sayar maka da abincin Rahina? Ko kasan sayar maka da abincin nan daidai yake da na sayar maka da wani tsagi na daga baiwar da Allah ya ba ta?" Haush ya sake mamaye Baba Sale sai kawai ya zuciya zai fa a gidan, da sauri Labaran ya suri wani aton itace. Ganin haka ya sa Baba Sale ya fice, shi kuma ya rufa masa baya yana fa "Jama'a ku tare ga ba in kwarto mai lasisi nan." Baba Sale yana fa awa cikin gida ya danno ofar ya saka sakata, Labaran ya yi bugun duniya bai bu e masa ba. Ganin yadda Mahmud ya yi zuru yana nazari ya sa Mudassir ya ta o shi ya ce. "Wai me yake faruwa ne?" Mahmud ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi Mudassir na ha u da wani iftila'i a cikin wannan auyen, ina cikin damuwa kuwa matu ar Mai gari ya gano ni." Mudassir ya bi shi da kallon mamaki don a iya saninsa da Mahmud, wannan ne zuwansa garin na farko, saboda har yana kan hanya shi ya dinga yi masa kwatance. A tsorace Mahmud ya kwashe duk abin da ya faru tsakaninsa da Laraba ya ba shi labari, tun bai rufe baki ba Mudassir ya dinga she a masa dariyar eta. Haushi ne ya kama shi, ya dube shi rai a ace ya ce. "Ka ma mayar da ni an iska wato ga mahaukaci ko?" Cikin dariya Mudassir ya girgiza masa kai ya ce, "Wallahi a garin wannan tsoron naka watarana sai ka halaka kanka. Yanzu kai Mahmud aljanu ne za su kai ka su baro? An ma kuwa aljanar gaske ce? Ace aljanu su nemi ya yanka musu zabi su tafi da su? Gaskiya akwai ayar tambaya." Jiki a sanyaye Mahmud ya ce. "Wallahi a wannan dajin ba na jin za a samu bil'adama a cikinsa, kai ganin idona na fahimci ba mutum ba ce. Yanzu tun da ka ce dole mu gabatar da kanmu wurin mai gari sai dai ka wakilce mu." "Kai ka san yadda mutanen auye suka auki mai gari kuwa? Ai dole sai mun ha u mun gabatar da kanmu ya san da zamanmu a garinsa, wallahi yadda ka ci ubansa shi ma haka zai ci na ka idan ya gano ka." Mudassir ya furta yana gimtse dariyarsa. Wata dabara ce ta fa o wa Mahmud ya saki murmushi a fili ya ce. "Mu je gidan da ka ce za mu sauka, na san yadda zan yi da su." Mudassir ya shiga kwatanta masa hanyar, suka sauya akalar hanyar zuwa wani an madaidaicin gida mai aki biyu wanda babu kowa a cikinsa. Mudassir ne ya auko mukulli ya bu e musu ofar suka shiga da kayansu, a kan wani anin gas da Mahmud ya taho musu da shi suka ora ruwan wanka. Sai da suka yi wanka suka sha ruwan tea da Mudassir ya dafa musu, sannan ya ce su shirya zuwa wurin mai gari. Mahmud shadda ya saka fara al, ya auko hula ya saka. Sai kuma ya saka face mask a fuskarsa idonsa yana sanye da glass. Mudassir kuwa ya saka ananan kaya sun yi kyau sosai, duk hanyar da suka bi sai abi su da kallo ana ganin 'yan birni sun shigo garin. Lokacin da suka arasa ofar gidan mai gari shiru suka ji shi kamar babu mutane, a ofar gidan suka tsaya duk da Mahmud ya rufe fuskarsa amma gabansa fa uwa yake kada Mai gari ya gano shi. "Salamu alaikum!" Mudassir ya yi sallama yana zura kai soron mai gari. Shiru suka ji ba a amsa ba, da yake akin Mai gari a soro yake yana jin duk abin da suke fa "Na yi mamaki da na ji ba a amsa sallamar ba, azu fa da na zo a kan idona ya shiga gida." Mahmud ya furta a hankali, shi kuma Mai gari jin haka ya sa cikinsa ya sake ka awa, don ya yi tunanin hukumar kare ha in aljanun ce ta sake turo wakilanta. Yana daga cikin akinsa gumi ya shiga keto masa, wani an matsakaicin matashi da ya zo wucewa ganin su Mahmud a tsaye ya ce. "Wai Mai gari kuke nema?" Mudassir ya gya a masa kai, don yaron ya yi musu magana da biyu ne saboda ya birge abokansa da ke can labe suna kallonsu. Ko babu komai dai ya san ya yi wa 'yan birni magana. "Idan kuka yi magana bai amsa ba, yana nan cikin akinsa ku wasa masa." Yaron ya furta yana niyyar wucewa, Mudassir ya ce masa. "Don Allah zo ka shiga ka yi mana sallama da shi, ka ce ba i ne suka zo akwai muhimmiyar maganar da suke son tattaunawa da shi." Gaban Mai gari ya sake fa uwa, nan take jikinsa ya shiga karkarwa. Jin furucin saurayin da kuma ba in da suke ofar gidan, ya sa shi sake firgicewa musamman da ya kallo auren akinsa ya karye ba shi da damar rufewa duk abin da zai faru sai dai ya faru da shi. Doguwar rigar shaddar jikinsa ya cire, ya zame dogon wandonsa daga shi sai gajeren wando. Don haka ya wala afafuwa ya saita bakin ofa, cikin shirin ko-ta-kwama. Don ya ci alwashin sai dai ya fice a guje amma ba zai zaune hukumar kare ha in aljanun ta sake hukunta shi. Musamman da ya san idan suka ritsa shi a akin babu mai watarsa sai Allah.. Cikin murna yaron ya shiga soron gidan Mai gari yana sallama, ya arasa bakin ofar akin zai yi magana sai ji ya yi Mai gari ya fito a guje ya baje shi a asa. Ya tattakura ya fita da gudu, a daidai lokacin, yaron ya fasa ihu saboda zafin buguwar da ya yi. Su kuma su Mudassir ganin yanayin da Mai gari ya fita a guje su ma sai suka rufa masa baya suna gudu, don a tsammaninsu wani abin ne ya koro shi daga cikin gidan. Saboda yadda Mahmud ya fi tsorata shi ne yake biye da Mai gari, hularsa da glass insa sai da suka yi kusa tsalle uku sannan suka fa i a asa. Abin da ya sake aga hankalin mai gari, yadda ya ga duk waigen da ya yi sai ya ga su Mahmud suna biyo shi a baya. Don haka ya tattakura ya ce. "Jama'a ku kawo mini auki, hukumar kare ha in wancan jinsin za su halake ni." A madadin a samu wasu su fahimci maganar Mai gari, sai dai duk majalisar da suka wuce su ma sai su rufa musu baya saboda tun da suke ba su ta a ganin Mai gari da gajeren wando yana gudu ba. Sai da Inno ta bari jikin Malam ya sarara masa da zafi, sannan ta sake aikawa aya bayan aya ta kira iyalanta. Tun da suka shiga akin suka fahimci ran Inno ya gama aci, Malam kallo aya ya yi wa Yaya Inu ya ji gabansa ya fa i, don haka ya sauke kansa asa. "Gaba aya na tara ku ne domin na yi muku godiya a kan cin mutumcin da kuka yi mini. Ba malam kuka wula anta ba, ni kuka wula anta. Idan har saboda na ce za mu yi aure da Malam ne kuka yi haka mu zuba ni da ku, a yau ba sai gobe ba zan yi wa Malam Liman magana bayan sallar Magriba a aura mana aure." Gaba aya shiru suka yi Baba Ibrahim ya ya ce, "Har ga Allah Inno ni ban san abin da ya faru ba, hasali ma ba na gidan a lokacin da abin ya faru." "Dama ni ban ce kai ba ne Iro, jikina yana ba ni Inusa ne saboda na yanka zakarunsa na dafawa malam." Malam da ya tuna garga in Yaya Inu ya yi sauri ya ce, "A'a Inno ba na jin Inu zai aikata mini haka." Inno ta sake ba wa Malam ha uri, ta kuma ba su umarnin da su ba shi ha uri tare da biyan ku in sadaki dubu hamsin. Babu yadda suka iya haka suka ba shi ha uri sannan suka fice. Suna fita Inno ta aika aka kira mata Malam Liman, bayan sun gaisa ta kawo ku i ta dam a masa na sadaki. Ta yi masa bayanin duk abin da ya faru, Malam Liman ya yi mata Allah sanya alheri sannan ya tafi. Bayan sallar Magriba kuma aka aura auren Inno da Mai Yasin a kan sadaki naira dubu hamsin. Lokaci aya gari ya auka a kan maganar auren Inno, ba inciki ya mamaye su Baba Ibrahim. "Magana ta gaskiya hankalina bai kwanta da wannan mutumin ba, na auka maganar auren nan za ta kwana biyu har na yi musu gwajin jini saboda muhimmancinsa. Gaskiya duk kun jagula al'amarin nan." Baba Ibrahim ya furta cike da takaici. "Uwar me gwajin zai yi ne da ka addabe mu da zan can nasara, da tun can da ake yin aure babu gwajin me ya faru da mutanen baya? Ko shi Baffa lokacin da zai auri Inno an yi musu gwajin ne? Kai ni ba wannan ne agabana ba, fargabata kada tsohon nan ya sake gangancin ta o garkena." Yaya Inu ya fa a. Baba Ado ya tuntsire da dariyar eta ya ce, "To garkenka kuma ai sai dai kar a kuma, ba ka ji labarin Inno ta sa an fita da matashin ragonka ba? azu nan fa aka wuce musu da shi wai Ali mai tsire ne ya gasa musu..." Tun bai gama magana ba Yaya Inu ya sha o wuyansa jikinsa yana rawa ya ce. "In ji uban wa?" Baba Ado ya zame hannunsa yana ci gaba da yata dariya, jikin Yaya Inu ne ya
Chapter 16 · 0% Book details