← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 64

Sashe 9

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakace kullum take faruwa da safe yana shiga part dinta amma daga nan baya sake komawa da haka har ta cika one week agidan, yau tun da safe ma ta kirata awaya take sanar da ita tana nan zuwa ita da yan tawagar ta domin gudanar da addu'o'in zaman lafiya _(peace prayer)_ sai da taji gabanta ya fadi amma babu yanda ta iya, zama tayi sukuku har wurin _1_ sai _2:30_ su ma suka zo ita da jama'arta wanda sun doshi su goma ciki harda _pastor_ wasu dauke da ganguna dakyar mai gadi ya kyalesu suka shigo nan ma ta shiga ta fito da ita cikin riga da wando ta kawota waje inda mutanen ke tsaye suna jiranta nan masu ganguna suka saki kida na yan mintuna sannan aka tsagaita pastor ya shiga yin addu'o'i bayan an kammala masu kida suka dora daga inda suka tsaya nanfa gida ya cika da kida jin haka yasa ummu al'amin lekowa cikeda tsoro nan ta hango abinda ke faruwa,

Cikin sauri ta dauki wayarta ta shiga kiran jabir yana dagawa tace "Abu al'amin wacce irin amarya ka auro ne? Gashinan yanzu sunzo sun cika gidan nan da kide kide, duk unguwar nan ta kaure da kida kuma an san daga gidan nan kidan nan yake fita yanzu wanne irin kallo mutane zasu yi maka?"

Cikin rashin fahimta yace "wanne irin kida? Kida ta kunna?"

"Masu kidanne suka zo har gida suke yi, idan ka saurara ma zaka iya jiyowa sautin kidan" cikin sauri ya kashe wayar ya dauki hularshi ya fito yana kiran idi driver,

Mintuna kadan sai gasu a unguwar, lallai kam gaskiyar ummu al'amin domin tun daga bakin gate yake jiyo sautin kidan gashi almajirai da yara har sun tattaru a kofar gidan suna son ganin abinda ke faruwa amma mai gadi ya hanasu shiga, cikin sauri mai gadi ya bude musu gate suka shiga nan idonsa ya hango masa goodness tsugunne an lullubeta da wani farin kyalle ga wani mutum tsaye da koko a hannunsa idonsa a rufe yana addu'a yana watsa mata ruwan akanta sauran mutanen wurin suma duk sun rurrufe idanuwansu,

Cikin sauri ya fito daga cikin motar ya nufi wurinsu, ganinsa yasa masu gangar dakatawa, sam bai iya masifa ba domin fadan ma bai samu muhallin zama awurinshi ba amma yau dai kam zuciyar maza ta baci hakan yasani komawa gefe dan ganin yanda zata kaya,

Cikin zafin nama jabir ya finciko mutumin wanda ke rike da kokon nan take kokon ya fadi ya tarwatse, kafa yasa ya shure goodness wacce ke tsugunne take ta hantsila ta fadi, _"what's kind of this madness?"_ yafada da karfi hakan yasa ma saurin bude idonta tareda sauran mutanen da idanuwansu ke rufe,

"Agidana za azo ana yimin shirka? So kuke mutane su daina ganin mutuncina? Kida agidana? To ni ba za ayi min shirka acikin gidana ba, baza a yimin bidi'a agidana ba, idan kafurcinku za kuyi ku tafi can inda kuka saba yi kuje kuyi kayanku amma ba anan ba"

Cikin masifa ma ta dubeshi "dama baka san irin matar daka aura bane? Kayi kadan ka hana yarinya gudanar da addininta da al'adarta kanaji? And kazo kana kiranmu da hauka, to you didn't seeing madness har sai kayi kokarin hanata addininta" ma tafada tana huci sauran mutanen wurin kuwa sai zare ido suke yi yayinda goodness ta fashe da kuka,

Cikin tsawa ya dubi mutanen wurin _"get out from my house"_ da sauri suka fara tattare nasu ya nasu suka nufi hanyar fita yayinda ma ranta ya baci ya baci ta kalleshi

"Tunda baka da mutunci yata ba zata zauna da kaiba, ke kuma goodness now you have find a good lesson in your life, wannan shine abinda na jima ina fada miki and you refuse to understand me, dama nasan you will face some challenges if you married a Muslim saboda ba zai barki kiyi addininki yanda ya kamata ba, he can't allow you to worship your God peacefully and successfully, yanzu gashi kin gani with your own eyes tun ba aje ko ina ba he starting disgracing us, and ya kunyatani on the faces of my people, amma its not his fault, laifinki ne kece kin jawo min da kika nace sai kin auri hausa man"

Tana kaiwa nan taja jakarta tayi gaba, yayinda goodness ta sake rushewa da kuka, ko kallonta bai yi ba ya juya yanufi sashensa zuciyarsa a bace, yana shiga ummu tana shigowa domin akan idonta komai ya faru,

"Abu al'amin kayi hakuri dan Allah naga ranka ya baci sosai, dama amaryar yare ce?"

Hular kanshi ya cire yana kallonta "yare ce asalima bata salla ba musulma bace" ya bata amsa,zaro ido tayi

"Au bata salla? To Allah ya sawwake" tafada tana jijjiga kai lallai sai yanzu ta gano dalilinsa na rashin ziyartar dakin amaryar ashe bata salla shikuma mutum ne mai tsananin kyankyami kuma ko ba haka bama shi bashida yawan bukatar mace yanda yake da sanyin nan haka sha'awarsa ma take a sanyaye dan ko ita sai yayi kimamin sati 3 koma fiye da haka ba tareda ya nemeta ba ita kuma kunya tana hanata nuna masa tana bukatarsa sannan tana jin bai kamata a matsayinta na mace tana kai kanta gareshi ba,

"Bari nayi wanka" yafada tareda wucewa cikin bedroom dinshi kallo tabi bayansa dashi, "shiyasa kullum baka rabuwa da mura domin ko wacce rana kana yin wanka sama da sau 5 narasa wannan son wanka naka wanne irine" tafada tana murmushi.

Goodness kuwa tana durkushe inda aka tafi aka barta tana faman kuka dakyar ta tashi ta nufi part dinta ta shige cikin daki ta kwanta taci gaba da gursheken kuka can taji yayarta anty Bilkisu ta fado mata hakan yasa tayi saurin daukar wayarta ta kirata, tana dauka tasake fashewa da kuka cikin rudewa anty Bilkisu tafara tambayarta meya faru cikin kuka tafada mata ta kare maganar da cewa _"ma want to interrupt my marriage,yana daf da ya sakeni tunda dama ba bawai yana sona bane kawai yabi umarnin mahaifinshi ne ya aureni"_ tafada tareda fashewa da kuka, hakuri anty Bilkisu ta shiga bata sannan tace gobe zata zo gidan tunda yanzu yamma tayi, ajiye wayar goodness tayi taci gaba da faman kuka.

_*Ummi Shatu*_👌🏻

[10/28, 9:27 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/26, 9:23 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_35-36_

~~~Tunda suka gama waya da anty Bilkisu ta kwanta take faman dankarar kuka har dare ya tsala haka ta zauna in banda kuka babu abinda take yi nan da nan kanta ya fara ciwo kamar zai fashe gida dari kukan taci gaba dayi har bacci ya sureta ba ita ta tashi ba sai da gari ya waye, tana nan nade akan gado har wurin karfe _9_ gaba daya komai ya jagule mata saboda tasan yau GM bazai shigo part din taba tunda ta bata masa rai, hakan ce kuwa ta faru bai ko kalli sashenta ba ya fita ya tafi office.

Wurin karfe _10:30_ anty Bilkisu tazo gidan, dakyar ta iya tashi taje ta bude mata kofa suka shigo ciki nan anty Bilkisu tabita da kallo duk fuskarta tabi ta kukkumbura gashi idonta yayi luhu luhu kuma yayi ja kamar gauta, cikin bedroom dinta suka karasa suka zauna a gefen gado,

"My sister what's happening? Kinga yanda fuskarki tayi kuwa? Me yayi zafi haka?" Anty Bilkisu ta fada tareda kamo hannunta ta rike,

"Anty ma want to finish my marriage, and tasa mijina yanzu yana jin haushina kuma dama can ba sona yake yi ba, bai taba sona ba and now ma makes him so upset, jiya tazo ita da pastor suna yimin addu'a har ya dawo ya samesu" tafada idonta yana zubar da hawaye,

"Calm down my sister, ni dama ban so kika biyewa ma har tazo gidanki yimiki addu'a ba, saboda kinga mijinki musulmi ne kuma malami wanda mutane suke girmamawa faruwar hakan na iya jawowa raguwar kimarsa a idon mutane, amma don't put it into your mind,saboda abun zai dameki, kiyi hakuri har ya huce kinji tunda naga you are lucky bashida fada sosai mutunne salihi, he's a nice person"

Bayan hannunta tasa tafara goge idonta wanda yayi sharkaf da hawaye ta kalli anty Bilkisu "thank you anty amma ya zanyi masa ya huce? Fushinsa na damuna, he's upset makes me to fell unhappy"

Murmushi anty Bilkisu tayi "kiyi hakuri zai huce ahankali kinji,yanzu kitashi kije kiyi wanka nasan daga ganinki kwana kikayi kina kuka ko abinci baki ciba"

Tashi tayi taja towel ta shiga bathroom ita kuma anty Bilkisu ta shiga kitchen ta shirya musu breakfast ta ajiye a falon ta kunna tv tana kallo acan kasan ranta kuma tana yiwa yar uwarta sha'awar wannan gida data samu dama haka Allah yake ikonsa akan bayinsa, tana nan zaune har goodness ta fito cikin riga da wando, wandon pink ne rigar kuma baka mai gajeren hannu, zama tayi suka karya suna ci suna hira, babu laifi damuwar dake ranta ta dan ragu domin anty Bilkisu ta dage wurin yimata wasu bayanai na yanda zata zauna da mijinta harma da kishiyarta, wuni guda sukayi tareda anty Bilkisu sai yamma ta tafi.

Tunda anty Bilkisu tatafi damuwar da take ciki ta sake dawo mata alamun bude gate taji dan haka tayi hanzarin mikewa taje gaban window ta tsaya, akan idonta motarshi ta shigo driver yayi packing ya fito ya bude masa shima ya fito, kamar kullum dai yana sanye cikin farar shadda gazna mai tsadar gaske kansa yasa hula, daga nesa ta hango fuskar nan tashi mai mutukar kyau, kansa tsaye ya wuce part dinsa, tsayawa tayi ta kurawa compound din gidan ido har na tsawon wani lokaci kafin daga baya ta nufi cikin dakinta ta kwanta, kamar wacce aka mintsina sai kawai ta fashe da kuka, kuka tayi kamar wacce aka aikowa da mutuwa, nan ciwon kan dake damunta ya dawo mata sabo fil, kafin wani lokaci zazzabi ya rufeta mai zafin gaske.
Chapter 9 · 0% Book details