← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 64

Sashe 15

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda goodness ta kwanta bacci bata tashi ba sai da gari ya waye tamgararu rana ta fito, zaune ta tashi ta kalli jikinta take abubuwan da suka faru jiya suka fara dawowa cikin kwakwalwarta tun zuwansu club da promise har dawowarta gida hatta marin da jabir yayi mata duk sai da ta tuno,

"I can't pardone you promise, you kid me, you have cheating me, you deceive me promise, i can't forgave you" wasu zafafan hawaye ne suka shiga sintiri akan kumatunta, sai da tasha kukanta ta koshi sannan ta tashi ta shiga cikin dakinta, wanka tayi bayan ta fito ta shirya cikin doguwar riga pink colour mai gajeren hannu rigar roba ce dan haka ta kamata sosai, kitchen ta shiga ta dora ruwan zafi.

Shi kuwa mal jabir da bacin ran abinnan ya kwana dan haka koda gari ya waye bayan ya shirya yayi breakfast daukar al'amin yayi suka tafi gidan mahaifinsa wato takwaran al'amin din,

Lokacin da suka je yana zaure yana zaune yana lazimi, da gudu al'amin yaje ya dale shi yana dariya, jiyowa shima yayi yana dariyar yana cewa "ja'iri dama nasan babu wanda zaiyi min wannan aiki sai kai, yanzu kuke tafe?"

Karasowa jabir yayi ya zauna agaban mahaifin nasa tareda gaisheshi cikin girmamawa, bayan sun gaisa ne yake sanar dashi cewar zai sallami goodness ta tafi gida saboda ga irin abubuwan da take yi masa,

"Haba jabiru ina hakurin naka ya tafi? Ina tunaninka da basirarka suka tafi? Idan ka sallameta me akayi kenan? Bukatar tamu bata biya ba kenan tunda ka kasa zame mata *wani haske* acikin rayuwarta, kayi hakuri jabir ban aura maka wannan yarinya ba har sai da nayi bincike akanta, sannan duk wadannan abubuwan laifinka ne yasa suka faru,saboda ka kasa janta ajikinka, ka kasa sake mata fuska ka kasa bata damar da zata zauna dakai ta fuskanceka ka fuskanceta har ta fahimci menene musulunci har taji ya kwanta mata arai, duk ba kayi wannan ba, meyasa?"

"Malam insha Allahu zanyi kokarin kwatanta hakan"

"Kayi kokari ka kwatanta jabiru saboda ko dan lahirarka domin yarinyar nan tanada wani hakki na musamman a wuyanka muddin ka danne daya daga ciki saboda kaga ita bata salla to wallahi babu ruwan Allah dole ne ya tambayeka yanda ka gudanar da rayuwarka tareda iyalinka, muddin ka fifita daya akan daya saboda ita ba musulma bace to wallahi kasani ranar gobe kiyama zaka tashi gefen jikinka a shanye domin haka annabi yacewa sahabbai duk wanda suka ga rabin jikinsa ya shanye ranar alkiyama to karsu tambayi kowa shine Wanda baya adalci a tsakanin iyalansa, sannan ya kamata ka kyautatawa yarinyar nan domin annabi yace mafi alkairunku shine wanda yafi kyautatawa iyalansa amma ni nafiku alkairi saboda nafi kowa kyautatawa iyalai na,ka zauna da matarka da aminci taji dadin zama dakai ka sake mata fuska kayi wasa da ita kayi dariya da ita kayi mata duk wata hidama wacce zata ja ra'ayinta zuwa gareka"

Ajiyar zuciya jabir ya saki tabbas yasan duk wadannan abubuwan da Malam ya fada gaskiyane kuma tun farko hakan ya kamata ace yayi amma bai yi ba,

"Nagode Malam Allah ya saka da alkairi kuma in sha Allahu zanyi aiki da abinda ka fada min"

"Allah yayi maka albarka, agaida iyalin"

Tashi jabir yayi yana kallon al'amin "to za mu tafi ko anan zan barka wurin malam?"

"A'a daukeshi ku tafi dan ba zama zaiyi ba kana tafiya zai tada rikici yace shi abbunshi shi umminshi"

Mikewa al'amin yayi yana dariya "ni abbuna zanbi"

Sallama suka yiwa malam suka tafi, Gida suka koma suna shiga part din goodness yayiwa tsinke al'amin yana biye dashi, acikin dakinta ya iskota ta takure a karshen gado,

Har bakin gadonta yaje ya zauna abunda yayi mutukar bata mamaki,

"Goodness nazo ne domin muyi wata magana dake, abinda kikayi jiya banji dadinsa ba domin kin wulakantani kin wulakanta kanki a idon duniya, alcohol haramunne a musulunci duk da cewar nasan ke a addininku halal ce, tunda farko ban san kina shan alcohol ba da zan yi miki gargadi akanta domin ba ashanta agidana, sannan zancen zuwa church ni bazan hanaki zuwa ba but zaki rinka zuwane once in a week, amma daily service babu shi yanzu i have called up it at all,did you get me?"

"Yes sir but am so sorry, honest to God i have Neva take alcohol before, i swear jiyama deceiving dina suka yi suka bani but it will neva happen again" ta fada tana goge fuskarta,

"Don't worry i pardoned you,but you have to maintain it next time"

Tashi yayi ya juya ya fita yabar al'amin azaune awurinta, jin baya fushi da ita yasata sakin jikinta ta kamo hannun al'amin suka koma falo,

"Clever boy" tafada tana murza hannunsa,

"Anty farcenki yayi tsawo dayawa ki yanke ranar juma'a"

"Meyasa sai ranar friday? Yanzu ma sai in yanke my boy"

"A'a anty abbuna duk ranar juma'a yake yanke farcensa dana tambayeshi sai yace min yanke farce ranar juma'a tana daya daga cikin sunnonin ranar juma'a"

"Nagode my boy nima ranar juma'ar i will cut my pinger nails"

"Yawwa anty kinga nima zan samu lada saboda annabi yace duk wanda yayi nuni da aikin alkairi to zai samu kwatankwacin ladan wanda yayi aikin"

Baki ta rike tana kallonsa yanda yake magana kamar abbunshi har lumshe idanuwansa irin nasa ne,

"Al'amin waye annabi? Naji komai sai kace annabi yace kaza yace kaza"

"Anty annabi shine annabi Muhammad (s.a.w),dan Abdullah, yazo da addinin musulunci, Allah ya aikoshi ga dukkan mutane baki daya, kuma shine na karshen annabawa, shugaban manzanni, mutum bazai taba zama cikakken mumuni ba har sai ya soshi kuma ya yarda dashi"

"Okey i understand now, nagane al'amin thanks for the explanation, let me go and cook indomie for us"

Tashi tayi ta shiga kitchen kafin ta fito shi kam al'amin ya koma wurin ummunshi.

Indomie ta dora tana aikin tana rera wakarta "am waiting my love love, no body can love it the way i do, am waiting my love love"

Jiyo sautin wayarta da tayi a falo yana tashi yasata kwallawa al'amin kira,

"My son pls help me with my phone" tafada da karfi, daidai lokacin mal jabir ya shigo cikin falon, sake kwallawa tayi da karfi,

"Al'amin can't you hearing me? I said make you bring me my phone"

Daukar wayar yayi ya bita cikin kitchen din, daga inda take tsaye tana zuba indomie din acikin tukunya ta miko hannu dan ta karba duk a tunaninta al'amin ne amma kuma ta jiyo sanyayyen kamshinsa sai dai duk da haka bata kawo shi bane domin a iya saninta yanzu yana office babu abinda zai dawo yi agida, tsal ruwan indomie din ya fantsalo mata a fuska hakan ya sata saurin ja da baya da sauri tana fadin,

"Ohh God", jinta tayi ta fada jikin mutum ta baya nan ta sake tsorata ta jiyo da sauri take ta kara fadawa kirjinsa da sauri ya tareta,

"Oh sorry i didn't hear your step, banji lokacin da ka shigo ba"

"Oya take your phone, dazu nayi mantuwa acikin dakinki, bari na dauka" mika mata wayar yayi ya juya ya fita tana biye dashi har cikin dakinta,

A inda ya tsaya dazu anan ya fara dube dube,

"Sir me ka yar?" Ta tambayeshi tana kallonsa ta bayanshi kasancewar ya bata baya,

"Bari gashi ma nagani" nuno mata wani dan karamin key yayi wanda daga gani na safe dinsa ne wato drawer din office dinsa Wanda yake ajiye documents masu muhimmanci,

Bashi hanya tayi ya juya ya fita, "adawo lafiya" ta fada tana kallonshi,

"Allah yasa" ya fada ahankali tare da ficewa, komawa kitchen tayi taci gaba da hidimominta.

Karfe _5_ daidai ya taso daga office ya dawo gida, sashensa ya shiga anan ya iske ummu da al'amin suna zaune acikin babban falonsa,

Mikewa ummu tayi ta amshi jakar dake rike a hannunsa tana yi masa sannu da zuwa yayinda shi kuma al'amin ya tashi ya rungumeshi yana cewa,

"Sannu da zuwa abbuna, abbu na me ka kawo min?"

Kansa ya shafa, "al'amin ya kamata muje muyi aski nida kai anjima ko?"

Kansa ya daga "na'am abbu"

"Yawwa yarona, bari nayi wanka naci abinci sai muje"

Sakin hannun al'amin yayi ya shiga bedroom dinsa, a kofar daki suka yi clashe da ummu, hannunta ya riko "me kika tanadar min?"

"Komai my dear" tafada tana zare masa hular dake kanshi,

"To nagode bari nayi wanka"

Rakashi cikin dakin tayi sannan ta fito ta kyaleshi.

Karfe _6_ ya kama hannun al'amin suka fita domin zuwa aski, part din goodness yayi niyyar zuwa kafin su fita, adai dai kofar falonta yaji ana kiransa a waya hakan ya sashi tsayawa domin amsa wayar yayinda shi kuma al'amin ya wuce cikin falon,

Al'amin na shiga ya sameta kwance tana kallo, sadadawa yayi yaje ya rufe mata ido duk a zatonshi wai bata ganshi ba,

Murmushi tayi ta kyaleshi, tana ji ya dauki bakin dankwalinta dake ajiye agefe ya daure mata fuska,

"Al'amin if i catch you ko? Hmm i know you are the one ai, bari natashi"

Dagudu ya zura bayan labule yana cewa "anty don't interrupt the game pls, ki nemoni gashi nan na gudu"

"I will find you now now al'amin" tafada idonta a daure, da gudu al'amin ya tafi bayan kujera ya boye, yayinda ita kuma ta fara lalubensa sai karo take ci da center table, kujera da kuma bango,

Jin an bude kofa ya sata saurin nufar wurin saboda ta zata al'amin dinne zai fice, jabir ne ya shigo ya bude baki kenan da niyyar kiran al'amin sai suka hada ido da al'amin din a bayan kujera inda ya boye, cikin sauri al'amin yayi masa nuni da hannu wai yayi shiru kar anty ta kamashi,

Jabir maganar ya hadiye ya tsaya yana kallon ikon Allah, da saurinta ta taho tana cewa "oh yes i will catch you now now al'amin, i have hear your match beside my door" ahankali ta nufi kofar gadan gadan tana mimmika hannu dan ta cafkoshi,

Tana zuwa ta mika hannayenta ta dadumo jabir wanda ke tsaye yana kallonsu, wata runguma yaji tayi masa, cikin sauri ta yi baya tareda sakinsa nan ta fara kokarin kwance daurin dake fuskarta,
Chapter 15 · 0% Book details