← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 64

Sashe 14

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin karfe 9:30 ta nufi part dinsa wannan shine karo na farko da zataje sashensa domin bata taba shiga kowanne sashe agidan ba baya ga nata, kofar falon ta murda ta shiga babban falo ne wanda yasha kayan alatu amma gaba dashi ma wani falon ne dan madaidaici, ahankali ta tasamma falon sai dai tana saka kai ta hangoshi rungume da matarsa ummu al'amin suna soyewa nanfa gabanta ya fara dukan uku uku zuciyarta ta shiga harbawa da karfi da karfi, dan karamin bakinsa dake sakata cikin wani yanayi ta hango yana cusawa cikin na matarshi sai juyi yake da ita tamkar wata yar baby kasancewar a tsaye suke, wasu zafafan hawaye ne suka shiga sintiri akan kumatunta wanda ita kanta bata san ko na menene ba, kamar wanda akacewa bude idonka yana budewa ya hangota tsaye tana kallonsu kafin yayi yunkurin sakin ummu har ta juya cikin sauri ta fice daga falon, tana tafe tana hawaye tamkar wacce aka aikowa da mutuwa, zahiri yau ta yarda jabir bai sonta ko kadan domin tunda tazo gidansa bai taba nuna yasan da ita ba amma yanzu jibi irin soyayyar da yake nunawa matarsa wacce yake so, kukane ya kwace mata ba tareda ta shirya ba lallai wannan shi ake kira da SON MASO WANI.

A bangaren malam jabir kuwa tun da yaga fitarta sai baiji dadiba domin yasan kowacece dole sai taji bacin rai musamman ma ita da bai taba gwada mata so ba, sai da ya samu nutsuwa sannan ya fara tunaninta, yasan dan so tana sonshi to amma shi rashin musuluncin da bata yine kawai ya hanashi nuna mata so.

Kwana tayi tana kuka ga damuwa da tayi mata yawa dan kowanne lokaci idan ta rufe idanuwanta shi kawai take gani yana romancing din Ummu, kuka tayi mai isarta sannan ta iya hakura amma akoda yaushe bakinsa da take muradi take ganowa cikin na ummu, bacci barawo ne yayi nasarar saceta da misalin karfe 5 nasafe amma 9 tana yi ta farka a furgece, wanka ta shiga tayi ta fito duk ranta babu dadi, zuciyarta ta cika da kunci, tana daure da towel tana shafa mai taji knocking tashi tayi taje ta bude, ganinsa tayi tsaye yana rikeda hannun al'amin, bata iya cemusu komai ba ta juya zata wuce dakinta,

"Good morning anty" ta jiyo muryar al'amin, juyowa tayi ta kakaro murmushin dole tace,

"Morning my dear son"

Kallo mal jabir yabita dashi daga gani tana cikin damuwa amma yayi damarar share mata hawayenta a daren yau duk da ba wai yana sonta bane kuma yasan bazai iya sakin jiki ba domin kyankyami gareshi,

"Anty nima kinga za muje unguwa nida abbuna"

"Adawo lafiya my son" tafada ta shige cikin dakinta, kallon kofar dakin jabir yayi to wannan me kenan? Ko itama fushin take yi dashi?

"Goodness" ya kira sunanta a hankali,

Fitowa tayi batare data amsa ba,

"Babu abinda kike bukata?"

"Babu" tafada atakaice tareda juyawa ta koma cikin dakinta,

Hannun al'amin yaja suka fita daga cikin falon suka nufi inda mal idi driver ke jiransu.

Goodness dai wuni tayi cikin bacin rai abunku da wanda baya salla, tana ganin 3 tayi ta dauki bible dinta ta tafi church,koda taje church dinma tana tare da damuwa gashi yau ma ba tajeba morning service taje, zama tayi jugum tayi tagumi bata farga ba hawaye suka fara bin kumatunta,

"Hello goodness what's happening?" Ta jiyo muryar promise tsohon saurayinta, cikin sauri tafara goge hawayen dake fuskarta gudun kada yagani amma kuma ya rigada ya gani, tsugunnawa yayi agabanta yana kallonta,

"Goodness what's wrong with you?" Yafada yana kallon fuskarta,bible dinta ta dafe ta kalleshi amma ta kasa magana to ma me zata ce masa shin zata fada masa cewar mijin data aura baya kulawa da ita ko kuma za tace masa mijinta baya sonta? Ganin bata da amsar bashi yasata yin shiru domin shi idan yaji wannan maganar ma dariya zai yi mata tunda ta kishi a baya gashi yanzu kuma tun ba aje ko inaba tafara korafi, hannunta taji promise ya kama ba tayi kokarin hanashi ba domin tana cikin damuwa dayawa,

"Goodness i know kina cikin damuwa because i saw your face symbolised this, but you know am your true lover i can't hold my hands watching you feeling unhappy, so yanzu ki taso muje wurin birthday party din Moses kinga after idan aka tashi sai ki tafi gida by that time i know you can get some relief"

Kallonsa tayi ta mike suka tafi duk ranta a jagule, wani dan madaidaicin club sukaje inda ananne za a gudanar da party din,

Kujeru suka samu suka zazzauna suka fara kallon yanda bikin partyn zai gudana, nan kuwa aka fara gudanarwa ita dai goodness bin kowa take da kallo amma ta dan ji sauki acikin zuciyarta, suna nan zaune anata chasu har gari yayi duhu, tashi promise yayi yace

"I dey come goodness, make i go and bring us some cool minerals"

"Ok but don't be long pls kaga ina son nakoma gida in the right time"

"Don't worry dear yanzu zan dawo" yafada tareda juyawa yana murmushin mugunta domin shi kadai yasan muguntar da ya shiryawa goodness wadda ita bata san da ita ba, wurin da ake bayar da drinks yaje aka zuba masa juice mai sanyi acikin cups guda biyu, ahankali ya zaro wata yar karamar roba daga cikin aljihunsa ya bude ya zuba abinda ke ciki acikin daya daga cikin juice din ya mayar robar ya rufe ya sata cikin aljihunsa.

Goodness na zaune tana jiransa sai dan waige waige take, nan ta hangoshi ya taho yana zuwa ya mika mata wanda ya tsiyaya wannan abun aciki, hannu tasa ta karba ta dan fara kurba ahankali ji tayi lemon yayi mata dadi domin har wani tsami tsami yake yi kamar anhada da lemon tsami amma kuma ta kasa tantance yanayin taste dinshi,

"Promise what's kind of sweet juice is this?" Ta tambayeshi tana lumshe ido,

"Kedai ki sha sai akaro miki" ya fada yana murmushin mugunta, shanye juice din tayi take tafara jin hajijiya tana daukarta gashi ta fara ganin mutanen wurin bibbiyu bibbiyu,

"Hey promise make you carry me and bring me back to my house" tafada cikin maye,

"Now now kuwa" yafada yana dariya, hannunta ya rike ya jata zuwa waje, da motar Moses yayi amfani ya sakata aciki ya ja ya fita daga club din yayinda ita kuma goodness ke cikin yanayi na maye domin sai shirme take yi irin na wanda ya bugu.

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[10/28, 9:29 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/1, 11:02 PM] Ummi A'isha👌🏻:

*WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_42-44_

~~~Gidanta ya nufa da ita domin bashida niyyar yin raping dinta domin a tunaninsa ba budurwa bace yanzu tunda tayi aure, a kofar gate din gidan ya sauketa ta debi takalmanta ta rike a hannu ta dauki bible dinta da jakarta, ga dan kwali shima ta rike a hannu tana layi,

"Hey promise thank you, till we meet tomorrow in the church"

Tafiya tafara yi tana layi tana harhada hanya,

Wani mugun bugu take yiwa gate din gidan kamar zata karyashi wanda har sai da mal jabir ya fito daga sashensa ya tsaya a compound din gidan dan ganin waye me yin wannan bugun kofar,

Dagudu mai gadi ya zo ya bude mata domin dama bayan gida ya dan zagaya, ganinta cikin maye ya sashi bata hanya,

"Don't worry dear, am not angry... Don't worry baba" ta fada cikin magana irinta bugaggu,

Takalminta da jakarta da Bible dinta da dan kwalinta a hannunta ta makale wasu a hammatarta tana tafe tana hada hanya,

Cikin razani mal jabir ya bita yasha gabanta kallo daya yayi mata ya gane acikin maye take "innalillahi wa inna ilaihir raji'un" shine kawai abinda ya iya furtawa tareda cakumar wuyan rigarta yana karewa jikinta kallo,

Sanye take cikin riga t shirt mai dogon hannu da skirt ta jeans blue,

"Have you drunk alcohol? Am asking you, tell me the truth" yafada yana jijjigata,

Wata dariya ta saka ta kalleshi ta kai hannunta kan fuskarshi tana shafawa, fusgarta yayi ya figeta yayi sashenta da ita shidai mai gadi yana tsaye yana kallonsu,

Kankameshi tayi ta gefensa tana dariya "am lucky, you are good looking, i love you soo much" haka taketa furtawa har ya shigar da ita falonta bayan ya bude kofar,

Tureta daga jikinsa ya shiga yi yana kallonta,

"Goodness me kika sha? Ki fada min abinda kika sha, alcohol kika sha?" Yafada da karfi wanda shi kansa bai san lokacin da ya koyi magana da karfi irin haka ba,

Gemunsa taja "i love you my dear, you are such a nice....!"

Tsawa ya daka mata "shut up your mouth, you better tell me what...!"

"Shhhhh" tafada tareda dora yatsanta akan bakinta "keep silent"

Hannu tasa ta shafo kumatunsa zuwa lips dinsa "i like you i swear, am in love"

"Goodness bakida hankaline ne? Ki fada min abinda kikaje kika sha" yafada cikin fada

"Alcohol nasha..!" Bata karasa rufe bakinta ba ya dauketa da mari tareda hankada ta kan kujera ya juya ya fice domin no need ya tsaya yaci gaba da westing din time dinshi a banza akan shirmenta.

Yanda ya fita ya barta haka ta zauna har wani bacci mai nauyi ya dauketa.

Yana zuwa dakinsa ya dafe kansa tareda zama a gefen gadonsa, wannan wacce irin rayuwa ce ya samu kansa aciki? To ko dama yarinyar nan bata gari bace? Ya tambayi kansa, tashi yayi ya fara zagaye dakin shi bai san da wacce kalma zai fassara wannan abun ba, yarinyar nan zuwanta cikin gidansa duk ta zubar masa da kimarsa wacce jama'ar gari ke kallonsa da ita,

Yanzu in banda kaddara taya za ace ansha giya agidansa? Bayan duk halaccin da yayi mata ya kyaleta take zuwa church daga gidansa hakan bai wadatar ba har sai ta hada da shan giya? Ya zama dole ya rabu da yarinyar nan tun kafin ta shigar dashi cikin wani hali,tabbas a gobe zai sallameta ta tafi gidansu tun kafin mummunar halayyarta ta shafi iyalan gidansa, _bathroom_ ya shiga yayi alwala ya fito yazo kan dadduma ya fara sallolin nafila kamar yadda ya saba gudanarwa ako wanne dare.
Chapter 14 · 0% Book details