← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 64

Sashe 20

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lalube yake tayi amma baiji ko daya daga cikinsu ba kamar basa wurin, al'amin ne ya sadado yazo yaja rigarshi ta baya ya kwalkwale da gudu, da aka sake jimawa kadan ya sake dawowa ahankali yace

"Abbu ga anty can agefen karfen tanki kaje ka kamata saboda ni ba iya kamani zaka yiba duk nifiku gudu"

Yana gama fadin haka yaja gefen rigarshi ya zura da gudu,

Shawarar al'amin yabi dan yasan bazai iya kamashi ba kam, gefen tankin yabi yana tafiya ahankali ganin haka yasa al'amin daukewa goodness hankali daga can inda yake yafara yi mata rada wacce bazata iya jiyo abinda yake fada ba.

Hankalinta ta mayar kansa tana tambayarshi da hannu wai me nene? Dariyar mugunta al'amin yayi mata saboda dama yayi hakane dan abbunshi ya kamata,

Juyowar da zatayi taji jabir ya taka kafarta daya, daurewa tayi batare da tayi motsi ba har zai juyawa ya wuce sai yaji alamun fitar numfashinta, kansa ya dan matsar nan ya tabbatar da cewa itace, cikin sauri ya fisgota da karfi, nan ta fada jikinsa wanda saura k'iris su zube su kai k'asa.

_*Ummi Aisha*_👌🏻
[10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/13, 5:16 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_Assalamu Alaikum masoya masu karanta wannan littafin na wani haske, ina mai baku hakuri na dan jina shiru da kuka yi kwani biyu da suka wuce hakan ya farune sakamakon abubuwa da suka sha kaina amma insha Allahu yanzu komai ya daidaita zaku rinka jina akoda yaushe har labarin ya kare, ina yi muku barka da sallah da fatan Allah ya maimaita mana amin._

_54-56_

~~~Cikin sauri ya fisgota da karfi, nan ta fada jikinsa wanda saura k'iris su zube su kai kasa,

Fuskarshi na daure da bakin kyallen ya fara yi mata magana a hankali cikin rad'a rad'a,

"Pls remove this thing from my face"

Daga kanta tayi ta kalleshi ya matseta sosai Wanda har tana iya jiyo bugun da zuciyarshi keyi ahankali,

Ahankali take jin saukar numfashinsa akan goshinta, dan motsi tayi ta fara kokarin kwace hannuwanta dake rike a hannunsa,

"To ka sakar min hannuna mana"

"Idan nasake ki guduwa zaki yi i know"

Sake take kafarta yayi, "ohhh..!"

Tafad'a ahankali, "ki kunce min daurin fuskata sai na sakeki"

"Sir you have match your leg on the top of mine"

Tafada tana sake k'ankameshi,

"Oh sorry" sausauta rik'on da yayi mata yayi ya dan sake hannunta kadan amma har lokacin yana rikeda su, ahaka ta kunce masa bakin kyallen dake fuskarsa,

Sakinta yayi, dagudu al'amin ya garzayo yazo ya dale abbunshi,

"Abbu nayiwa anty wayo nasa an kamata"

"I already know you are the one who plan this al'amin,but i will take revenge next time" ta fada yayinda take daura dan kwalinta,

"Sorry anty i know what i will do so that you can't take avenge"

Tsaye yayi yana kallonsu, sauke idanuwansa yayi akan al'amin yace

"Al'amin muje kayi alwala lokacin salla ya kusa"

Hannun goodness al'amin ya kama yana dariya "anty let's go"

Binsu a baya jabir yayi suna tafiya al'amin yana lilo ajikin goodness har suka je sashenta ya shiga ya dauro alwala ya fito wurin abbunshi suka tafi masallaci.

Yau ta Kama ranar juma'a, karfe 1 mal jabir ya taso daga office, lokacin da yazo gidan goodness ta yiwa al'amin wankan juma'a tana shiryashi,

"Anty fararen kayana zaki samun saboda ummu na duk ranar juma'a fararen kaya take samun kuma kinga ai abbuna ma duk kayansa farare ne saboda annabi yace mu yawaita dinka kaya farare"

"Tom bari nasaka maka wannan farar shaddar"

"Yawwa anty dama irinta abbuna ce, shima yana da irinta"

Yana tsaye a bakin kofa yana kallonsu har ta sakawa al'amin kayan,ajikinta taji alamun ana kallonta hakan ya sata saurin juyawa hada ido tayi dashi yasha farar shadda sabuwa kar, ya gyara sajensa da gemunsa fes sai zuba kamshin turare mai sanyi yake,

"Hmmm you are always cool, even your perform is like the way your are" tafada ahankali,

"Anty me kike fada? Da abbuna kike?" Al'amin ya fada yana mika mata hularshi dan ta saka masa,

"No bada abbunka nake ba da kaina nake, have you get me?"

"Na'am anty" hularsa ta saka masa ta dauki turare gaban mirror dinta ta feffesa masa,

"Anty baki bamu carpet ba"

"Zo nan da akwai abun salla acikin mota" ya fada yana gyara zaman agogon hannunshi, hannunsa yaja suka fita nan ta rakasu da ido, al'amin ba karamin kyau yayi ba shida abbunshi tamkar ta sacesu ta gudu dan kyau.

Da yamma tana corridor dinta tana wanke inner wears dinta al'amin yazo yana tsalle "anty nima zanyi wankin"

"No bari kar ka bata kayanka"

"Nidai anty zanyi" ganin zai dameta yasata tura masa bocket daya ya fara jagwalgawalawa,

Mal jabir ne ya shigo jin hayaniyarsu acikin corridor yasa shi binsu can amma falon k'ure yake da wakar akon cikin wakarsa ta _black girl_,

Yana zuwa corridor din ya kallesu "me kuke yine? Naji banji motsinku ba gashi kuma ina son fita"

"Abbu kayan anty muke wankewa kaga irinsu" bra daya da pant daya ya kwaso da gudu da niyyar kai masa dan ya gani, da sauri goodness ta rikoshi,

"Hy give me my kaya" karbewa tayi ta mayar cikin bokitin, wata uwar kunya taji ta rufeta yau kuma da wanne ido zata kalli abbunshi yaga bra da pant dinta alhalin ita kuma tanada kunyar wadannan abubuwan shiyasa ko a toilet bata shanyasu gudun kar yagani ko shi ko al'amin din,

"Bari naje wurin malam" yafada yana kallonta ta baya,

"Abbuna zan bika ko? Muje wurin malam"

"Adawo lafiya, agaida shi" tafada ba tareda ta juya ba, tana ji al'amin ya kwashi takalmansa ya bishi suka tafi, girgiza kai tayi yaro dai yaro ne.

Ranar Saturday da safe bayan ta shirya breakfast ta yiwa al'amin wanka, kitchen ta shiga ta dan gyaggyara shi saboda ta dan kwana biyu bata yi masa gyara na tsanaki ba, digirgire tayi ta bude drewar din sama tana zuba dinner set, cikin tsautsayi tana dora wani kofi ashe bai zauna ba, dawowa kofin yayi ya fadi akan babban dan yatsanta na kafa taratsatsa kaje ji ya fashe akan yatsan nata, take ya yankata kamar ansaka wuka an yanka gun kun san dinner set da uban nauyi,

Wata kara tasaka da karfi, da gudu al'amin yazo daga falo inda yake zaune yana kallon cartoon a mbc 3,

"Anty" ya fada tareda zaro ido, ganin jini yana malala a k'afarta ya sashi fashewa da kuka tareda juyawa da gudu yayi hanyar sashen abbunshi, yana zaune yana karanta jaridar _weekly trust_ al'amin ya shigo da gudu yana kuka yazo ya fara girgizashi ya rike hannunshi,

"Abbu jini da yawa a kafar anty... Abbu zo muje ka gani"

Ajiye jaridar yayi ya saka silifas dinshi yabi bayan al'amin wanda keta faman kuka, tsoro da mamakine suka kamashi a lokaci guda, to ko menene ya faru? Tambayar da yaketa nanatawa kenan acikin zuciyarshi,

Suna shiga ya ganta ta jawo kafar tana zaune akan kujera amma jini duk ya b'abbata wurin gashi tun daga kitchen din jinin yake zuba,

"What's happening? Goodness what's happen?" Ya tambayeta gamida bin jinin da kallo, kitchen ya leka anan ya hango kofin da ya fashe ga uban jini awurin,

Dawowa yayi inda take, yana kallon fuskarta yasan dauriya kawai take amma tana jin jiki saboda gaba daya naman wurin gashi nan awaje yana gani kai kadan ma ya rage dan yatsan ya rabe biyu,

"Am coming" ya fada ya juya ya fita, sashensa yaje ya dauko hydrogen acikin kwalba da farar audiga, har ya dawo al'amin yana kuka,

Hydrogen din ya dan tsiyayo acikin murfin kwalbar ya dauki audiga ya zuba akan dan yatsan nata, wani uban tsalle goodness ta daka ta sauko kasa ta kankame shi sosai kamar zata koma cikin cikinsa,

"Sir pls stop it, pls sir wlh da zafi" hawaye ta fara yi tana rirrike hannunsa tana kokarin janye kafarta,

Kallonta yayi nan yaji tausayinta tana sanye da rigar bacci _maroon colour_ mai siririn hannu da dan buje din wandon rigar iya cinyarta, kanta sanye da hula baka,

"Sorry kadan zan saka miki saboda jinin ya tsaya kinga har yanzu jinine yake zuba ko kina son jinin jikinki ya kare gaba daya?"

"No sir but pls don't put it again"

Hannunsa ta sake kankamewa, tana kuka, ga al'amin shima agefe yana nasa kukan, rikeshi tayi gam taki sakinsa har shi kansa sai da yayi mamakin karfinta ita kuma ganin haka ya sata mamakinsa har aranta tana cewa "ashe ma bashida karfi nafishi, he's not strong see him like a woman"

Bata karasa zancen zucin da take yi ba taji ya zame rikon da tayi masa yasa hannunsa daya ya rike hannayenta duka, auduga ya dauka ya sake zuba hydrogen ajiki zai saka mata,

Wani kuka ta saka "ohhh...! Sir i beg u pls don't put it, pls sir, pls, pls"

Kankameshi tayi ta cukwikwiyeshi tana kuka hawaye nabin kumatunta, "abbu ka kyaleta kar ka sake saka mata dan Allah" ya jiyo muryar al'amin yana rokonshi,

Biris yayi dasu duk da yasan akwai zafi amma haka ya danneta ya sake saka mata,

Shure shure ta fara har tana yaye rigar barcin dake jikinta ba tare da ta sani ba, birgima taci gaba da yi tana kuka, kallonta yayi duk ta kwaye rigarta takaita kirjinta, gaba daya cikinta yana waje dan har yana iya hango ash colour din bra din dake jikinta,

"Tashi muje chemist ayi miki dressing din wurin"

Jijjiga kai tayi tana kuka "no sir abarshi haka zai warke"

"Ba komai zasu yi miki ba kawai dressing ne tunda na rigada na wanke miki wurin"

Tashi tayi ta dingisa ta shiga dakinta yanzu jinin ya tsaya ya daina zuba, shi kam al'amin yana zaune gefe ya hada kai da gwiwa yanata kuka, gabanshi yaje ya kamo hannunsa,

"Al'amin daina kuka kaji, kaga antyn ma ai ta daina alamun ta warke"

"Abbu yau babu wanda za muyi wasa tare tunda anty bata da lafiya"

"Waye ya fada maka? Za kuyi wasa mana, ai ta warke"

Tashi yayi yana share hawayen fuskarshi, dai dai lokacin ta fito sanye da doguwar rigar da ya kawo mata tsaraba lokacin da ya dawo daga madina.
Chapter 20 · 0% Book details