← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 64

Sashe 28

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuskar nan tashi mai kyau ta zubawa ido tana kallo ko kiftawa bata yi, kamarsu daya sak da al'amin danshi sai dai shi al'amin din yafi shi hasken fata domin ummunshi ya dauko a haske amma baya ga haka komai na al'amin irin nashine,

"Oh my al'amin am missing you" tafada ahankali,

"Abbu bani aron wayarka" ta fada tana daga kwance, ahankali ya jiyo ya kalleta tareda maimaita sunan aranshi "abbu" yafada acikin zuciyarshi,

"Me zaki yi da wayata?" Ya tambayeta, "pls abbu i want to hear the voice of my lovely son al'amin" ta fada cikin shagwaba, daga kai yayi ya kalli agogo karfe _10_ saura yan mintuna,

"Yanzu al'amin yayi bacci amma gashi ki kira kiji" mika mata wayar yayi ta mika hannunta ta karba ta fara neman layin ummu al'amin din amma wayar akashe, ta dade tana kiran wayar amma bata samu ba dole ta hakura ta mika mishi,

Kallonsa tayi tace "abbu kayi min addu'a ina son zanyi bacci"

Dago kanshi yayi ya kalleta,

"Wacce irin addu'a?" Ya tambayeta tare da mayar da hankalinsa kan laptop dinshi,

"Irin wacce kayi min jiya, ban taba yin bacci cikin nutsuwa kamar wanda nayi jiya ba"

"Kawo hannuwanki inyi miki" ya fada ahankali, zaune ta tashi ta matsa kusa dashi ta hada hannuwanta wuri daya ta mika masa tafin hannuwan nata, addu'o'in kwanciya bacci ya karanto yana tofa mata acikin tafin hannunta har ya kammala ya dubeta,

"Ki shafe jikinki"

"Thank you abu al'amin" ta fada tana shafe jikinta kamar yadda yace, hakan data fada sai ta tuno masa da matarshi Salma wato ummu al'amin.

Kwanciya ta koma tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi har bacci ya dauketa, sai da ya kammala abinda yake yi sannan ya tashi yaje toilet ya dauro alwala yakoma inda ya keb'e domin gudanar da ibadarsa ya fara sallar nafila.

Can tsakar dare goodness ta farka daga bacci tafara dube dube domin taga gadon wayam babu jabir, acan gefe ta hangoshi yana salla, jijjiga kai tayi ta koma ta kwanta tana mai jinjina rikon addinin da jabir yake dashi, sai wurin _3_ ya hawo gadon ya kwanta har lokacin goodness idonta biyu tana kallonshi, addu'o'in kwanciya bacci yayi kafin ya kashe wutar dakin,

Minti 10 atsakani taja jikinta taje ta shiga jikin jabir kamar yadda tayi jiya, cikin barci ya rungumeta tareda k'ankameta ba tare da ya sani ba, tamkar zasu mayar da junansu cikin cikinsu haka suka yi.

K'arfe _5:30_ ya samu ya farka bakinsa dauke da salati,mamaki ne ya kamashi jin yadda shi da goodness suka makalkale junansu kamar wasu tif da taya, hannuwanshi yasa masu mutukar taushi ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya shiga toilet, bin bayansa da kallo goodness tayi aranta tana mai burin inama zasu dawwama ahaka ita da jabir.

Tun kafin ya dawo daga masallaci ta koma sashenta tayi wanka ta shirya ta shiga kitchen ta hada abin karyawa ta dauka ta kaiwa jabir nashi sashensa sannan ta dawo dakinta tafara gyara kayan sawarta tana shisshiryasu cikin sif,

Stool din madubi ta dauko ta taka tahau dan ta dora wani akwatin kayanta asama, cikin tsautsaye ta goce ta fad'o, gefen kunkuminta sai da ya bugu da gadonta, tashi tayi kokarin yi amma ta kasa dan haka ta ci gaba da zama awurin har jabir yashigo yace mata ya tafi office.

Tunda ta buge agefen kunkumimta ta baya take tafiya dakyar tana dingishi, da haka ta samu tayi duk wasu ayyukanta har yamma tayi jabir ya dawo, ganinta tana yin dingishi ya sashi tambayarta abinda ya sameta, bata boye ba ta sanar dashi,

"Ok dauko Robb acikin dakina sai ki shafa awurin bayan kin gasa gun da ruwan zafi" ya fada yana kallonta,

"No abbu" ta fada tana mak'e kafadarta,

Bai sake cewa komai ba ya tashi yafita ya tafi salla sai da ya dawo yana zaune akan gado hannunsa kuma rikeda littafin _sahihul bukhari_ ta shigo tasha kayan baccinta doguwar riga fara sai faman kamshi take zubawa,

Kan gadon ta hau ta kwanta tana gyara hular kanta, mikewa jabir yayi ya ajiye littafin hannunsa akan drewar din gadon ya shiga toilet, ruwan zafi tafasasshe ya taro acikin karamin baho ya dauko towel karami wanda yake goge jikinshi dashi idan yayi wanka,

Tana kwance ta yi rub da ciki tana fuskantar bango yazo inda take,

"Oya tashi" yafada ahankali,

Tashi tayi babu musu ta juyo tana kallonsa ganinshi da kayan gashi ya sanyata mikewa da sauri domin guduwa, robar ruwan zafin ya ajiye ya yi sauron rikota babu zato ta fado jikinsa ta baya nan ya rungumeta baiyi wata wata ba ya dage rigar dake jikinta nan take farin pant din dake jikinta ya bayyana, da saninsa ya sake dage rigar domin yana son ganin kalar bra din da ta saka, itama fara ce sol,

"Hmmmm to match akayi kenan, komai white, that's good" ya fada acikin zuciyarshi, jin tana kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata ne ya sanyashi dawowa daga duniyar tunanin da ya lula, towel din ya tsoma cikin ruwan zafi ya dauko shi yana tiriri gashi harda ruwan ajiki ya manna mata akan kunkuminta,

"Abbu, pls da zafi ka bari" ta fada arude, bai kulata ba ya sake tsoma towel din ya ciroshi ya dora mata akan wurin gashi idan ya dora baya daukewa har sai ya huce, haka yayi ta mata har sai da ya tabbatar gurin ya gasu sannan ya kyaleta,tashi tayi tana goge gumin da ya feso mata agoshinta dan azaba idonta kuma yayi rau rau tana son yin kwalla,

"Ungo Robb shafa awurin, ko ba zaki iya ba na shafa miki?" Ya fada yana bin lukuta lukutan cinyoyinta da kallo,

"No abbu zan iya" tafada cikin sauri tareda amsar Robb din, toilet ta shiga ta shafe wurin da Robb amma ba karamin dadi taji ba saboda har taji saukin ciwon da wurin yake yi mata,bude kofar toilet din tayi ta fita aranta tana jin dadin yadda jabir wani lokacin yake sakin jiki da ita har yayi mata wasu abubuwan masu kama da na masoya gashi yanzu ya sake shiga ranta sosai dalilin kwana da ta fara yi dashi a gado daya,

Yana zaune yana jona laptop dinshi a charge ta fito tana kawar da fuskarta, ta gefen ido ya dan kalleta yayi murmushi wanda shi kadai yasan yayishi, ya gane nufinta na shiga toilet wato dan kar yaga jikinta ne ya sanyata yin haka, bakinshi ya tabe aranshi yana cewa,

"Na nawa kuma? Jiki kam ai nagama gani yarinya sai dai ki kiyayi gaba kuma" idonshi ya lumshe ya tuno manyan cinyoyinta da ya gani dazu, juyawa yayi ya kalleta lokacin da take kokarin hawa kan gadon,

Gyara zamanshi yayi ya dauki laptop dinshi ya kunna ya dorata akan gadon ya fara lallatsawa,

"Abbu addu'a" ya jiyo muryar goodness tana fada masa cikin wani salo na daban,

Kamar yadda yayi mata jiya yau ma haka yayi mata ta shafa ta kwanta, amma kuma bacci yaki daukarta son jabir ne kawai ke azalzalar ruhinta, tana son amon muryarshi domin idan yana yin magana har ji take kamar dodon kunnenta zai suma da dadin muryarshi.

Fiyeda minti talatin ta shafe tana kallonshi yanata rubuce rubucenshi acikin laptop gashi ita kuma baccin yaki zuwar mata, tashi tayi zaune ta saisaita muryarta tace,

"Abbu kayi min labari, bacci yaki daukata yau" ta fada tareda jan wani dan guntun tsaki, kallonta ya dago yayi,

"Ni ban iya labaran duniya ba sai dai labarin da alqur'ani yazo dashi idan kina so sai in baki" ya bata amsa,

"Yes ina so" ta fada tana gyara pillow dinta domin kwanciya, laptop dinshi ya rufe ya ajiyeta agefe ya juyo yana kallonta.

_*Ummi A'isha*_👌🏻

[9/21, 8:45 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE...!*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_71-75_

_*Wannan babin nakune kyauta wad'anda suka yi mafarkin wani haske adaren shekaran jiya da daren jiya, ina fata daren yau babu mafarkin wani haske,ina sonku fiye da yanda kuke son wani haske, masu mafarkin wani haske nagaisheku kyauta gashi kunada yawa balle na zayyano sunayenku,asha karatu lafiya.*_

~~~Laptop dinshi ya rufe ya ajiyeta agefe ya juyo yana kallonta, "kika ce kina so?"

Kai ta d'aga sannan ahankali tace "yes i like it"

Dan kishingida yayi yana mai fuskantarta, "zan fara da baki k'issar d'aya daga cikin annabawan da Allah ya aiko zuwa ga al'umma, yanzu ki zabi guda acikinsu sai na baki labarinsa ina nufin kissarshi"

"To ai ban sansu ba" ta fada tana shafa fuskarta da hannunta,

"Eh nasani amma zaki sansu yau, ki zaba acikin guda ukun nan, annabi Adam, annabi musa, annabi Yusuf,wanne kike son na baki k'issarsa aciki yanzu?"

Kallon fuskarsa tayi tana murmushi, "annabi Adam"

Gyara zama yayi ya fuskanceta sosai ya fara bata kissar annabi Adam tun daga halittarsa har zuwa kan halittar matarsa hauwa'u da zaman da suka yi a aljanna har zuwa kan lokacin da suka ci ganyen itaciyar da Allah ya hanesu,

Idanuwan goodness a lumshe suke ta nutsu tana sauraren sautin muryar jabir yana bata labari, yanda take jin labarin gani take kamar a tv take kallo gashi tamkar jabir zabo kalmomin da yake fada mata yake yi, labarin gaba daya ya tafi da ita, musamman ma daddadar muryar jabir da take sauraro,

"Zan barki haka sai gobe zan k'arasa miki" ya fada yana kallonta,

"No abbu kar kayi min haka, pls ina son jin abinda ya faru dasu bayan sunci ganyen itaciyar, pls abbu"

Dan murmushi yayi da dukkan alamu bukatarsa zata biya tunda gashi tana da interest akan k'issar da ya fara bata,

"Sanadiyyar cin wannan itaciyar da nana hauwa'u tayi shine mata suke yin jinin al'ada domin lokacin da ta hadiyi ganyen take jini ya fara fita daga jikinta, shine sauran mata suka yi gadonta suma suke zubar da wannan jinin lokaci zuwa lokaci, shi kuma annabi Adam bai hadiye ba, nan gaba daya sutturar dake jikinsu ta bar jikinsu, Allah ya sauko dasu daga cikin aljannah"

"Oh God" ta fada tareda dafa goshinta tana runtse idonta,

"Sun koma kuma?" Ta tambayeshi,

"Sun koma domin Allah mai yawan yafiya ne ga bayinsa"

Murmushin farin ciki tayi, "gaskiya abbu labarin nan da dadi, kai da waye ya baka shi?"
Chapter 28 · 0% Book details