← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 64

Sashe 36

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko sakacen hakorin ma kuka zaki yi masa?" Ya tambayeta yana mai sake tura tsinken matsematsin hakorinta,

Janyewa tayi ta matsa gefe "abbu barshi haka, idan nayi brush zai fita"

Tashi tayi ta kwashe sauran kayan ta fita taje bedroom dinta tayi brush ta sake shafa turare ta dauko wata arniyar rigar barci _coffee_ colour mai santsi wacce sai ta baya ma ake daureta da madaurinta, bata da wani girma dan iya gwiwa take sannan siririn hannu gareta,

Yar karamar hula ta dauka ta saka akanta takoma sashen jabir, acikin dakinsa ta sameshi zaune agefen gado gabanshi laptop ce a ajiye yana dubawa,

"Abbu daure min rigata ta baya nakasa daurewa"

Dagowa yayi yana kallonta, wani irin kyau yaga rigar tayi mata gashi tayi mata cif cif komai yaji,

Shagala yayi lokacin da yake d'aure mata rigar, saboda gaba daya gadon bayanta a bayyane yake gashi wasu zarirrika ne wanda suke a tagaban rigar suka taho har ta baya,kwata kwata ma ya kasa d'aurewar, idan ya d'aure sai ya kunce sai ya sake d'aurewa haka yayita yi har wurin sau goma, ita dai goodness tana zaune ta juya mushi baya tana jiran ya gama,

Dakyar ya iya hakura ya d'aure mata ya janye hannunshi daga jikinta,

"Abbu ina al'amin, shine ko yace yana gaisheni ko?"

Tafada tareda hawa kan gadon ta kwanta agefenshi daf dashi, domin har jikinta yana gogar nashi,

"Yace agaisheki mana, har da sako ya bani in kawo miki, sai gobe zan baki idan na bude kayan"

"Yawwa nagode, Allah sarki my boy i missed him so much"

Idanuwansa ya mayar kanta ya kalleta,

"Dazu da naje gidan malam yayi min maganarki, ina tayaki murna, barka da shigowa addinin musulunci, addinin gaskiya,ina yimiki addu'ar kasancewa acikinsa har karshen rayuwarki"

Hannunsa ta kama ta rike acikin nata ta lumshe idanuwanta,

""Abbu nagode, bayan tafiyarka nayi mafarkinka"

Hannun nata ya sake makalewa cikin nasa "meya faru a mafarkin? Me nayi miki? Fada min"

Murmushi tayi tafara shafar gashin da yake kwance a hannunshi, wani irin yammmmm! Yafara ji amma sai ya dake,

"Abbu ganina nayi acikin wani bakin daji mai tsananin duhu sai kawai nafara hango *wani haske* yana tahowa daga nesa har ya karaso kusa dani yana karasowa sai naga ashe kaine,kana zuwa sai ka kama hannuna muka yita tafiya har muka fita daga cikin wannan bakin dajin muka shiga wani wanda yake mai tsananin haske ga wani kamshi mai dadi yana tashi ga ciyawa koraye awurin sannan ga tsuntsaye sunata rera kuka mai dadi, ka bude baki kenan da niyyar fara yimin bayani sai nafarka, naji haushi ba kadan ba saboda naso ace naji abinda kayi niyyar fada min"

Hannunsa daya yasa ya rike dayan hannunta wanda take shafar gashin hannunsa dashi,

"Shigowarki addinin musulunci shine fassarar mafarkinki binti, hakika kafurci duhune yayinda musulunci kuma ya zama *wani haske* wanda ya haskaka dukkan komai"

"Hakane abbu, yanzu na tabbatar da duk abubuwan da ka fada min abaya"

"Dazu kikace min sau biyu kike yin jini awata?"

Idanuwanta ta rufe duk ya sakata taji kunya saboda yadda yake fadin maganar afili inama laifin ya dan sakaya yace period,

"Uhmmm?" Ya sake tambayarta, daga masa kai tayi batare da tayi magana ba,

"Yaushe da yaushe?"

Dakyar ta iya bude bakinta "farkon month da karshensa" ta fada cikin shagwaba ga wata uwar kunya data lullubeta,

Kin taba ganin dr akan hakan" ya tambayeta gamida murza yan yatsunta,

Kai ta sake dagawa batayi magana ba,

"Me yace miki?"

"Yace ba problem bane" ta bashi amsa har lokacin idonta arufe yake amma tana jinshi yana matsa yatsunta duka,

"Allah ya albarkaci rayuwarki binti"

"Amin abbu, kayi min addu'a inyi bacci"

Kansa ya rankwafar zuwa kusa da ita ya fara yi mata adu'o'in Wanda har lokacin tana rike da hannuwansa duka biyun, sai da ya kammala tofeta da addu'a sannan ya kalli idanuwanta wadanda suke a lumshe,

"To ki sakeni mana binti"

Murmushi tayi tasaki hannun nashi duka biyu acikin sloww motion ba dan taso ba,

Murmushi yayi ya koma yadda yake yaci gaba da aikinshi, sake matsawa daf dashi tayi bada jimawa ba bacci ya dauketa,

Ya jima zaune yana amsa fatawar mutane daban daban kafin ya rufe laptop din ya jiyo yana kallon goodness wacce take kankane ajikinsa domin lokacin da tayi baccin batare data saniba acikin barci ta sake shiga jikinsa dan harda zira hannunta acikinsa da haka har ya gama aikinshi tana zagaye dashi da hannuwanta,

Hannunta ya zare ahankali ya dubi lukuta lukutan cinyoyinta wadanda ta yayesu ba tare da ta sani ba, rigar yaja ya gyara mata yaje ya dauro alwala ya fito yazo gefenta ya kwanta yana mai karanto addu'o'in neman tsari daga dukkan abin k'i.

_*Ummi A'isha*_👌🏻

[10/2, 3:45 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_91-95_

~~~Bargo yaja ya rufa mata sannan shima ya dan rufe rabin jikinsa,shiru yayi yana tunani aranshi wanda kusan rabin tunanin akan goodness ne, hakika Allah shine mai yadda yaso aduk halin da yaso kuma alokacin da yaso,

Tun farkon haduwarshi da goodness lokacin data fara aiki a office dinshi har yau dinnan da suke tare a matsayin Ma'aurata duk sai da ya tino su acikin wannan dare,

Jinta yayi ta matso jikinshi tana mai kankameshi,ahankali yasa tattausan hannunshi ya dagota ya kwantar da ita ajikinshi gamida shafar kanta har bacci ya saceshi.

Tun kiran sallar farko ya tashi ya gyara mata kwanciyarta ya lullubeta yaje yayi alwala yafita masallaci,

Har k'arfe 6:30 bai dawo gidan ba alokacin goodness ta farka tunda taga dakin wayam tasan bai dawo daga masallaci ba, sashenta taje tayi wanka da ruwan dumi ta shirya cikin dan karamin wando tied iya gwiwarta da yar riga fara mai hannun shimi,

Sashen jabir tayi maza ta koma ta gyara masa cikin bedroom dinshi ta gyara falo har lokacin bai dawo ba domin wani lokacin har sai rana tafito yayi sallar walaha sannan yake dawowa,

Part dinta ta koma bayan ta kammala gyara sashen jabir, kitchen ta shiga ta dora abin karin kumallo,

Dankali da kwai ta soya sannan tayi farfesun hatta ta dafa tea da kayan kamshi,

Sai da ta gama shirya komai sannan ta nufi sashen jabir tasan lokacin kila ya dawo,

Akan doguwar kujerar falonshi ta ganoshi yana kwance da doguwar jallabiya fara ajikinshi, yanda yayi kwanciyar ba karamin kyau taga yayi mata ba domin ya harde duka hannuwanshi guda biyu akirjinshi idanuwanshi alumshe amma fuskarshi dauke da murmushi kamar wanda yake ido biyu,

Ahankali ta sadada ta je inda yake kwancen, hannuwanshi ta warware ahankali ta budesu tashiga cikin jikinsa ta kwanta duk da tanada masaniyar kujerar tayi musu kadan, matsuwa tayi sosai ajikinshi tana mai kallon kyakkyawar fuskarshi,

Kanta ta kwantar akirjinshi tana mai shafa kyakkyawan sajensa,

Hancinshi taja sannan ta dora dan yatsanta akan lebenshi na kasa, "ohh abbu badai kyau ba, Kanada kyau sosai, shiyasa al'amin shima ya zama mai kyau"

Kanta ta cusa acikin kirjinshi tana shakar kamshinsa mai dadi,bakinta tasa ta ringa jan botir din gaban rigarsa har sai da ta bubbudesu duka da hakorinta nan ta tura kanta cikin rigarshi tana sinsinar kirjinshi, ta dade ahaka har jabir ya farka, ganinta yayi tana makale dashi gashi duk ta bubbude masa botiran jikin rigarsa da bakinta,kallonta yayi yanda suke kwancen nan kamar wasu hanta da jini,fuskarta yafara karewa kallo yana kokarin gyara mata kwanciyarta acikin jikinshi,

Da saninta tayi wani juyi zata fada kasa,cikin sauri ya tarota ya rungumeta,

Bude idonta tayi dama ba bacci take ba tana jinsa,

"Dama ai rigimace tasaki zuwa ki kwanta anan tunda kin san wurin yayi mana kadan, ke kadai ma wurin kadan zaiyi miki balle mu biyu" ya fada yana kallon idanuwanta,

"Yanzu wannan wurinne yayi mana kadan abbu?" Ta tambayeshi tana kallonshi itama,

"Ehh tunda saura kadan yanzu kisha k'asa, ba dan natashi ba da sai dai kijiki akasa"

"Abbu duk lokacin daka tashi magana sai kace ni katuwa ce bayan banga ta inda nafika kiba ba"

"Haba yarinya, kinfini mana"

"Ta ina?"

Hannunshi yadora akan cinyarta,

"Wannan cinyar taki guda daya tayi ahada nawa duka biyu"

Hannunshi ta rike saboda sai taji kamar tafiyar tsutsa yake yi mata acinyar tata,

"Sannan kuma waye yace miki ki bude min botiran rigata?"

"Yi hakuri abbu bari in rufe maka dama can ba laifina bane, hakorina ne ya bude"

Hannuwanta ya rike, "yanda kika bude da baki to yanzunma da bakin zaki rufe"

"Yi hakuri abbu bazan iyaba"

Bakinta tasa tafara kokarin wai sai ta balle botiran amma ta kasa,

"Abbu bari naje na kawo maka abinci, tun dazu nagama"

Sauka tayi daga kan kujerar ta fita da gudu, binta da kallo jabir yayi yana girgiza kai, wato yarinyar nan yarinyace danya sharaf bata da maraba da yar 14 komai nata na yara take yi,

Tashi yayi yaje yayi brush ya fito lokacin har goodness ta kawo abincin tana zuba masa,

Akasa ya zauna yafara ci yana kurbar tea din,

"Abbu insa hannu nima muci tare?" Dagowa yayi ya kalleta tana tsotsar dan yatsanta wanda ta yanke jiya,

"Uhm" yafada atakaice saboda wani lokacin shi baya son surutu,

Cokali tasa tafara ci tanayi tana satar kallon bakinshi wanda yake motsi mul mul lokacin da yake taunar dankalin,

Ya rigata kammalawa dan haka tashi yayi ya shiga cikin dakinsa ya janyo jakar kayan da yazo mata dashi, anesa da ita ya zauna ya fara kokarin bude jakar,

Da sauri ta ajiye spoon din hannunta tadawo kusa dashi ta zauna tana murmushi,

"Ungo sakonki inji danki al'amin" mika mata chocolate yayi acikin wani babban kawali,

Cikeda doki da murna ta karba, "nagode, Allah Sarki al'amin dina"

Yana kallonta ta bude chocolate din tafara sha ya yi tunanin abin na wasane sai yaga sha kawai take babu kakkautawa kafin ya farga har tasha guda biyar tana kokarin bude ta shida,

Hannunta yakama yarike wadda take da niyyar budewar,

"Ke bakya gajiya da shan zakine? Wannan kayan zakin da kikesha sune suke sakaki rushing dinnan idan kina period, kar nasake ganin kinsha wannan chocolate din, mayarta cikin kwalin ki bani nan"

Langabar da kanta tayi cikin sigar shagwaba tace "ayya abbu kabarni nasha wannan din, daga ita bazan sake shan wata ba"
Chapter 36 · 0% Book details