← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 64

Sashe 56

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa taci gaba da tafiya musu cikin son juna da yarda da amincewa da junansu da kuma zaman lafiya mai dorewa, har yanzu jabir yana koyar da ita abubuwan da suka shafi addini, gashi kullum tana zuwa makarantar islamiyya inda take kara samun wani karatun,

Kimanin wata uku da yin barinta tasake samun wani juna biyun nan aka koma gidan jiya aka fara laulayi da kwadayi,

Karfe uku na dare ta farka daga baccin da take yi, ido ta bude tafara neman jabir, acan wurin da ya kebe domin sallarshi ta hangoshi yana karatun alqur'ani, juyawa tayi tana fuskantarsa, alqur'anin ya rufe ya taso zuwa inda take kwance,

Agefenta ya zauna ya riko hannunta yana shafa kyawawan kananan kitson dake kanta,

"Abbu gobe ko fate faten tsaki zanyi da wake da alayyahu"

Tafada tana kallonsa, shima kallonta yayi yana murmushi,

"Fate fate? Nikuma me zaki yimin?" Ya tambayeta yana jan hannun rigar baccinta guda daya,

"Abbu kaima shi zaka sha" tace dashi bayan ta rike hannunshi,

"Wallahi abbu ko idan ka tsinka min hannun rigata ba yarda zanyi ba" tafada tana turo masa baki,

"Me zakiyi binti? Ramawa zakiyi?"

Dariya tayi ta riko hannunshi duka cikin nata, "hanaka fate fatena zanyi"

Dariya yayi ya dagota kacokan ya dorata ajikinshi, "to yanzu ba zaki koma baccin ba?"

"Abbu muyi hira ni nagama bacci"

"To ai ni kin san irin hirata indai irin wannan lokacin ne" ya rada mata acikin kunnenta,

Sumar kanshi tafara shafawa "abbu wallahi indai na haifo baby marar gashi to kaine"

"Kedai binti, ni ai duk Sati sati nake yin aski da ace bana aski da tuni yanzu sumata tafi taki yawa"

"Hum um" tafada cikin shagwaba,

Bakinshi yakai saitin nata tagoce tana cewa "um um abbu"

"Ehh binti" yace da ita yana murmushi,

Kwanciya tayi ajikinshi suka ci gaba da nunawa junansu so.

Washe gari da safe kitchen ta shiga ta shirya fate faten tsakinta takoma dakinta ta zauna atsakiyar gadonta tafara sha, dakin nata jabir ya biyota ya sameta tazuboshi a filet tanata sha da cokali,

"Binti tsabar rowa shine zaki gudo nan ki zauna"

"Ba rowa bace abbu"

"To menene?" Ya tambayeta yana kokarin hawa kan gadon,

"Gashi abbu musha"

Hannu yasa yafara diba yana ci,

"Binti bakin nan naki ya iya kwadayi tun jimawa"

"Kaima ai kwadayayyen ne abbu" tafada tana murmushi,

"Naji, nayarda"

Sai da suka koshi dam sannan yashirya domin tafiya office, part din bahijja ya shiga domin yi mata sallama, daure da towel ya ganta ta fito daga wanka tana kokarin karasawa gaban mirror,

"Binti nafito, sai nadawo?"

Juyowa tayi tana kallonsa yasha black din dafaffen boyel da hularshi yayi kyau sosai,

"Abbu kayi kyau, adawo lfy, Allah ya baka sa'a ya saka maka albarka adukkan al'amuranka"

Gareta ya karasa ya rungumeta yayi mata kiss agoshi sannan ya amsa da,

"Amin bintina,Allah yayi miki albarka, me zaki dafa da rana?"

"Fate fatena zansha yana nan dayawa na ajiye"

Hannunta ya kama ya rike yan yatsunta, "to shikenan nima ki rage min kinji"

Kai ta daga, sakinta yayi ya juya yafita yana murmushi, itama da murmushin ya tafi yabarta akan fuskarta tana mai jin wani sabon sonsa yana sake shigarta.

K'arfe 8 nadare yana kwance adakinsa akan gadonshi gabanshi da laptop yana lallatsawa bahijja ta shigo hannunta dauke da hijab jikinta kuma riga da wando ne yan kanti,

"Abbu gari da sugar nake son sha, kazo ka rakani muje mu siyo tare"

Juyawa yayi ya kalleta, "gari?" Ya tambayeta,

"Uhm abbu"

Laptop din ya rufe ya tashi zaune, yana karewa jikinta kallo,

"Muje, amma binti yau kuma ki rasa abinda zakisha sai gari da sugar?"

Hannunshi ta rike bayan tasaka hijabinta suka fara tafiya,

"Amma dai abbu ai ba laifina bane"

Ganin ta rakwarbabe masa fuska yasashi fara rarrashinta, suna tafe suna hira har sukaje wani shago abayan layinsu, tsayar da ita yayi ya karasa da kanshi shagon ya siyo mata garin kwano daya ya dawo suka koma gida,

Suna zuwa ta dauko Kofi ta diba ta zuba ruwa tasa sugar da madara tafara sha jabir yana zaune yana kallonta, bata iya yi masa maganaba har sai da ta kammala shanye garinta tukunna,baki ta turo masa,

"Abbu kuma meye kaketa kallona?"

Jikinshi ya matso da ita "binti wannan cikin naki ya saki kinyi kyau ne, matsalarshi daya ya mayar dake lazy mai dankaren kwadayi"

Kwantar da kanta tayi akan kirjinshi tana dariya, "shi kuma abbu gashi yanzu ya zama wani kala"

Hancinta yaja yana murmushi.

Kullum haka take fama da kayan kwadayi, yau wainar fulawa tayi ita ta wuni tana ci har dare,

Tsakar dare tana tsaka da bacci ciwon ciki ya tadata daga baccin kafin wani lokaci har jini yafara zuba daga jikinta,

Fitowar jabir kenan daga bathroom ya iyo alwala yazo ya risketa acikin wannan halin ba tare da bata lokaci ba yacire mata yar rigar baccin da take jikinta ya saka mata kaya ya dauketa yafita da ita lokacin har ta fita hayyacinta,kasancewar darene mal idi driver baya nan dan haka da kanshi yayi driving ya kaita asibiti suna zuwa aka karbeta likitoci suka fara kiciniyar hana cikin dake jikinta fita sai dai kaddara ta riga fata domin kafin wani lokaci har cikin ya karasa zubewa,

Bahijja tasha wuya sosai azubewar wannan cikin amma jabir sai kwantar mata da hankali yake yi yana bata hakuri sannan yana nuna mata cewar ta rungumi wannan jarrabawar da Allah ya aiko mata da ita domin doctors din sunce bawata matsala ce da itaba kawai dai kaddara ce,

A wannan karon ma jabir bai sanarwa da kowa ba har aka sallamesu a asibitin suka koma gida, komawarsu kuma keda wuya bahijja tafara yi masa kuka mai cin rai,

Hakurin dai yaci gaba da bata har ta hakura itama ta dangana kamar yadda taga shima yayi ita kam har mamaki jabir yake bata domin bata taba ganin mutum mai tawakkali irinshi ba, duk abinda Allah ya aiko masa karbarsa yake yi da hannu bibbiyu, bai taba nunawa Allah gajiyawarshi akan wannan jarrabawar ba, ganin haka ya sanyata itama daukar kaddarar suka ci gaba da zamansu cikin aminci da kaunar juna.

Bayan faruwar haka babu dadewa ta sake samun wani cikin amma kuma wannan tun yana wata daya da yan satittika shima ya zube tunda sukaje asibiti aka bata gado dr din ya kira jabir office dinshi yafara yi masa jawabi kamar haka:

"Agaskiya ayanda muke zargi matarka tana shan magungunan zubar da cikine in banda haka yaza ayi ace tayita samun miscarriage har sau uku, gaskiya kasaka ido sosai akanta sannan ka dauki matakin da ya dace"

Jabir jin jikinsa yayi ya mutu yayi sanyi amma kuma acan kasan zuciyarshi wani irin tafarfasa yaji tanayi ga wani uban bacin rai da ya ziyarceshi lokaci guda.

Shiru kawai yayi yaci gaba da sauraron bayanin da dr din yake yi masa,

"Yanzu gobe idan Allah ya kaimu zamu iya sallamarku ku koma gida amma gaskiya kasaka ido sosai akan matarka domin duk yadda akayi itace ke zubar da cikin da take samu"

Tashi jabir yayi batare da yace komai ba ya mikawa dr din hannu ya fita ya nufi resumption domin bazai iya shiga dakin da bahijja take ba lokacin saboda bacin ran da yake tare dashi,

Tunani kawai yake yi aranshi me yake yiwa yarinyar nan da har ya sata kin hada jini dashi, shin me yake tare dashi da har take kyamar jininshi, sanin bashida amsar wadannan tambayoyin ya sanyashi mikewa yafara zagaya farfajiyar wurin,

Har gari ya waye bai samu nutsuwa ba yana nan dauke da takaicin abinda likitan nan ya sanar dashi,

Sai da ya danne zuciyarsa sannan ya shiga dakin da bahijja take kwance duk ta dan rame daga daren jiya zuwa yau kadai, bai iya yi mata magana ba asalima ya kasa koda kallon fuskarta,

"Abbu zan sha tea" shine abinda ya jiyota tana fada cikin kasalalliyar murya,

Bai bata amsa ba ya juya ya fita, minti kadan sai gashi ya dawo hannunsa dauke da kayan shayi da tea flask domin ya tura akawo musu dama,

Zama yayi ya hada mata tea din ya mika mata, dakyar ta iya tashi ta kafa kai tafara sha,

Har tagama jabir baiyi mata magana ba,

"Abbu kace su sallameni mu tafi gida, bana son wannan wankin cikin wallahi da wahala"

Tafada tana ajiye cup din dake hannunta,

"Dama wannan time din sunce ba zasu yi miki ba amma ai bai kamata ki tsorata ba tunda kece kika jawowa kanki" yace da ita tareda mikewa ya fice, Gida yayi tafiyarshi batare da ya sanar mata ba,

Mamakine ya kamata sosai saboda jin abinda ya fada, sam takasa fahimtar inda zancen nashi ya dosa, tana nan zaune har dr ya shigo ya sake dubata ya bata sallama, shiru shiru babu jabir sai da rana tayi sannan mal idi driver yazo ya dauketa yakaita gida, ba karamin mamaki tajiba lokacin da taje gidan ta tarar jabir baya nan yayi tafiyarshi office,

Duk da jikinta babu kwari haka ta daure ta gyara gidan tayi girki amma koda jabir ya dawo bata samu fuska awurinshi ba, abincin ta kai masa amma yanda ta ajiye masa haka ya tashi ya barshi yayi wanka ya ficewarsa,

Duk tabi ta damu da sauyin da tafara gani daga gareshi,tana zaune tana nazarin abinda ya fara faruwa agareta tsakaninta da jabir har ya dawo misalin karfe 9:30,bai kulata ba ya wucewarsa cikin daki yayi wanka yayi shirin bacci ya kwanta, jin shiru bai fitoba ya sanyata binshi cikin dakin,

"Abbu bakada lafiyane?" Ta tambayeshi tana kokarin zuwa kusa da ita,

"Kar ki zauna min adaki, kikoma dakinki bana son damuwa" yafada ahankali yana kokarin juya mata baya,

Kuka tafara "abbu dan Allah idan wani abun nayi maka kayi hakuri, abbu dan Allah kafada min laifin da nayi maka, wallahi bazan iya kwana ni daya adakina ba"

Jin kukan da take yi masa yake yi har acikin ranshi, shi kansa yana tunanin ta yanda zai iya ganin wannan daren ba tare da bintinshi ba amma kuma radadin ciwon abinda tayi masa shine bazai barshi ya iya kwana da ita adaki daya ba ayau,
Chapter 56 · 0% Book details