← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 64

Sashe 11

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tareda yayi mata magana ba ya dagota tsaye suka nufi wani office inda za adubata suna shiga likita ya fara checking dinta tareda yi mata yan tambayoyi anan yake tambayarta yaushe rabonta da abinci tace kwana 3,cikin sauri mal jabir ya kalleta ransa ya dan sosu domin hakkinsa ne na tabbatar da yanda al'amuranta ke gudana acikin gidansa, fada doctor ya fara yi akan danme zata zauna bata ci abinci ba alhalin kuma tana cikin yanayi na rashin lafiya,jikinta doctor din ya taba yaji yayi laushi dan haka yace gado za abata saboda sai anyi mata karin ruwa, female ward aka kaita aka jona mata karin ruwa, reception mal jabir ya koma ya fara kai kawo lallai abinda yayi bai kyauta ba sannan ai bai ma kamata yaga laifin goodness ba tunda ba itace takai kanta ba takanas mahaifiyarta ta biyota gidan domin yi mata addu'ar, wata faduwar gabace ta sameshi domin tunowa da wani hadisi da yayi wanda annabin rahma, annabi Muhammad (s.a.w) yake cewa _"dukkaninku masu kiwone, kowa za a tambayeshi dangane da kiwon da aka bashi, shugaba mai kiwone akan jama'arsa, mai gida mai kiwone akan iyalansa sannan mace itama mai kiwoce akan al'amuran cikin gidanta"_ tabbas yasan duk da cewa goodness ba musulma bace to tana da wasu hakkoki akansa wanda har yanzu ya kasa saukesu.

Awarsu uku acikin asibitin sai da aka kara mata ruwa leda biyu sannan aka sallamesu bayan an hado mata magunguna kaya guda, hannunsa rike da nata ya sata acikin mota suka nufi hanyar gida, maganar al'amin ce ta fado masa _"abbu ka siya mata chocolate itama tana shan chocolate kamar ni"_ gyaran murya yayi yace da driver ya biya dasu ta super market, wani sabon super market suka je da kansa ya shiga ya kwaso mata chocolates kala kala da sauran tarkacen kayan zaki sannan ya siyo mata take away ya dawo cikin motar inda take jingine idanuwanta arufe.

Mintuna kadan suka karasa gida, kayan da ya siyo mata ya debo tareda riko hannunta suka shiga falonta.

Akan kujera ya zaunar da ita ya ajiye ledojin dake hannunsa ya dan kalleta kasa kasa idanuwanta a lumshe ta jingina kanta ajikin kujerar da take zaune agaskiya kyakkyawa ce ta karshe kawai matsalar dan ba musulma bace shiyasa ya kasa ganin kyawun nata amma dan kyau tana da kyau na asali,

"Kici abincin sai kisha magani kin ji doctor yace ki daina zama da yunwa" yafada cikin cool voice dinshi,

"Ok thank you" tafada har lokacin idanuwanta a lumshe suke,

"Ina zuwa" yafada tareda juyawa ya fita, idonta ta bude tabi bayansa da kallo har ya fice daga cikin falon, zamewa tayi ta kwanta akan doguwar kujerar tareda lumshe idanuwanta.

Yana fita part din ummu al'amin ya shiga, samunta yayi tana shirya al'amin da alama wanka tayi masa, yar karamar jallabiya ta yara fara ta saka masa tareda fesa masa turare,

"Ummu idan kin gama abunda kikeyi kije ki duba yarinyar can ashe bata da lafiya sosai bamu sani ba" ya fada yana shafa kan al'amin,

"Allah sarki, to bari nagama naje, Allah ya bata lafiya" tafada tana gyarawa al'amin wuyar rigarsa, dagudu al'amin ya fita ya nufi part din goodness, yana fita ta kamo hannun sa ta rike cikin nata,

"Meke damunta? Ko laulayi ne?"

Kai ya girgiza mata "bana tunanin haka kawai zazzabi ne ke damunta, bari naje nayi alwala naga lokacin salla ya kusa"

Sakin hannunsa tayi tana murmushi "to adawo lafiya" fita yayi daga sashen ummu ya nufi nasa.

Da gudu al'amin ya shiga falon goodness lokacin tana nan a kwance kamar yadda take dazu, ganinsa yasata tashi zaune ta cire hijabin jikinta tana murmushi,

_"sannu anty, yas'alul lahil azim, rabbul arshil azim an yashfiki"_ yafada tareda zama akusa da ita,

"Al'amin who taught you this?" Tafada tana jansa jikinta,

"Anty abbu nane ya koya min, itace addu'ar da ake yiwa marar lafiya, indai mutum bashida lafiya aka yi masa wannan addu'ar to yana samun lafiya da izinin Allah"

_"thank you soo much my dear son, my God bless your life"_

Zaune ta tashi ta janyo ledojin da mal jabir ya ajiye mata ta ciro take away ta ajiye a tsakiyarsu itada al'amin,

_"oya chop"_ ta mika masa spoon, girgiza kai yayi,

"Alhamdulillah Anty, nakoshi"

"To ungo ledar chocolate maza dauki kayita sha kaji good boy"

Chocolate din ya dauka ya fara sha yana kallonta, hannun hagu tasa tafara cin abincin da spoon, cikin sauri ya rike hannunta,

"Anty bakiyi bismillah ba kuma kin sa hannun hagu"

Mayar da cokalin tayi hannun damanta ta kalleshi "al'amin kenan waye yace maka ba acin abinci da left hand?"

"Abbu nane kullum kullum idan zanci abinci sai yace min sai nayi bisimillah kuma kar naci da hannun hagu saboda akwai wani sahabi da yake cin abinci tareda annabi lokacin sahabin yana dan yaro sai annabi yake cemasa yakai yaro ka ambaci Allah, kaci da damanka sannan kaci gabanka"

Murmushi tayi _"wow al'amin you are such a brilliant boy and talent,komai naka irin na mahaifinka ne like father like son, you take after your father, wow this is wonderful thing oh oh, oya ci gaba da bani labari kana shan chocolate"_

Kafin yayi magana ummu ta bude kofa ta shigo idonta akansu domin ta dade a bakin kofar falon tana sauraren hirar da suke yi.

Cikin murmushi ta karasa ta zauna tana kallonsu,

"Uwa da d'a" ummu tafada tana murmushi,

_"welcome anty"_ goodness ta fada itama tana murmushin domin yaune rana ta farko da fara ganin ummun duk zamanta agidan domin bata samu fuskar shiga wurin kowa ba agidan asalima bata taba shiga wani wuri baya ga part dinta ba acikin gidan,

"Sannu ashe bakida lafiya, ayya sorry" ummu ta fada tana kallonta domin yanzu ta danji sassaucin tsanar da tayi mata acikin ranta saboda ta fuskanci tana son danta al'amin sosai kun san kuma bahaushe yace uwar d'a mahaukaciya ce duk mai kaunar danta to itama tana kaunarsa,

"Thank you anty, nagode nagode"

Mikewa ummu tayi "Allah ya kara sauki,bari nakoma saboda inada aiki"

"Ayya anty come and chop please" goodness tafada tana mika mata abincin gabanta,

"No thank you am ok" ummu tafada tareda juyawa tafita, har bakin kofa goodness ta rakata sannan ta dawo wurin al'amin dake zaune yanata bare chocolate yana sha dan yasha akalla zata kai guda goma, zama tayi kusa dashi tana kallonsa,yaron komai nasa irin na abbunshi ne amma yafi babanshi surutu sosai amma baya ga haka kamarsu daya sannan wani abun burgewar ma ya dauko halayyar abbun nashi,

_"my boy don't full your stomach with this zak'i zak'i"_

Dagowa yayi ya kalleta "anty ai ban koshi ba kuma kece kikace nayita sha har na koshi"

Dariya tafara yi harda rike ciki "oh dama so kake sai ka koshi sannan zaka bar shan chocolate din?"

"Na'am anty" ya bata amsa yana murmushi tareda bude manyan idanuwansa irin na mahaifinshi yana shirin sake wata maganar abbunshi ya bude kofa ya shigo,

Tsumu goodness tayi tareda saurin sunkuyar da kanta kasa, kallonta ya danyi ya kalli al'amin wanda shima shi din yake kallo,

"Al'amin lokacin salla yayi maza tashi kaje kayi alwala kazo muje masallaci"

"To abbu" al'amin ya fada tareda tashi da gudu ya fita, yana fita ya jiyo ya kalleta har lokacin kanta a sunkuye yake tana kallon abincin dake gabanta gashi ta kasa ci gaba da cin abincin, duk jikinta jinsa take ya takure,

"Kinsha maganin?" Ya tambayeta a hankali,

"No, yanzu zansha idan nagama cin abinci" ta bashi amsa

"Ki tabbatar dai kinsha kar kiyi wasa da wannan magungunan, Allah ya kara sauki" yana kaiwa nan ya juya ya fita, lokacin al'amin har ya fito daga part din ummu ya iyo alwala.

Bayan fitarshi ta saki ajiyar zuciya "hmmmm i like u my cool" tafada ahankali tareda tashi tsaye ta kalli window nan ta hangoshi yana rikeda hannun al'amin suna kokarin fita, sai yanzu ta samu damar kallonsa domin dazu da ya shigo kasa kallonsa tayi, ya sake wanka ya sake jallabiyar jikinsa daga kalar ruwan kasa zuwa kalar ruwan madara da yar karamar hula itama ruwan madara, ayanda ta lura bai fiya saka kananan kaya ba daga jallabiya sai manyan kaya amma duk da haka bai hana kyawunsa fitowa ba, komawa tayi ta zauna bayan taga fitarsu, yanzu fes take jinta saboda taga alamun ya huce ya daina fushin da ita dama kuma ciwonta yanada alaka da fushinsa, abincin ta kammala ci tasha magani ta tashi ta shiga bedroom dinta ta kwanta, kamshin turarensa take ta ji ajikinta tamkar itace ta fesa turaren ajikinta, rigarta ta sinsina har yanzu kamshin yana nan kamar yanzu ne ya jinginata a jikinsa.

Wayarta ta dauka ta kira anty Bilkisu suka gaisa sannan ta kira babanta shima ta gaisheshi, gabanta yana faduwa ta kira ma domin itama ta gaisheta, dakyar ma ta daga wayar cikin fada tace

_"goodness kin daina zuwa church ne? Rabonki da church kin jima ko kin canja addini ne?"_

"No ma, banida lafiya ma yanzune na samu sauki amma may be gobe zan zo tunda gobe sunday"

Kwafa ma tayi cikin bacin rai tace,

_"thank you goodness for what your husband have done to me last time, but i want remind u,you promised me that you will not change and fellow his religion, dan haka ina mai gargadinki be very carefull with him, kar ki bari ya yaudareki ya jaki cikin addininsa"_

"Am so sorry ma about what he has done, sannan ma tun jimawa nafada miki son da nake yi masa bazai saka na bi addininsa ba, kiyi hakuri ma it will neva happen again"

"Don't worry my daughter its pass, but you make sure gobe kin zo church kinji"

"Zanzo ma, thank you my sweet mother"

Kashe wayar tayi tana murmushi aranta tana tunanin hali irin na ma, ita dai a duniya bata son addininsu abbun al'amin, da wannan tunanin bacci ya dauketa.
Chapter 11 · 0% Book details