← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 64

Sashe 58

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*Ummi Shatu*_👌🏻

[10/26, 8:43 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

_126-130_

_(second to the last page)_

~~~Kowannensu fuskarsa dauke da alamun tambaya suke kallon dr tafida,

"Dr ya akayi? Wanne hali binti take ciki yanzu? Anyi nasarar cire karin daga mahaifarta?"

Wadannan sune jerin gwanon tambayoyin da jabir ya zayyanowa dr tafida alokaci guda,

"Dr kafada mana halin da my daughter take ciki" ma tafada cikin tashin hankali,

"Duk ku kwantar da hankalinku patient dina tana nan lafiya, anyi aiki cikin nasara amma sai nanda 4 sannan zata farfado"

Sai alokacin dukkaninsu suka samu nutsuwa, wata sanyayyiyar ajiyar zuciya jabir yayi domin hankalinsa da ba karamin tashi yayi ba gani yake kamar ya rabu da bintinshi kenan har abada,

Masallaci yatafi yaje yayi salla ya fito daga nan kasuwa suka wuce bayan ya biya ta bank ya ciri kudi,

Kayan dubiya irin wadanda wanda aka yiwa tiyata zai iya ci ya sissiyo mata da sauran kayayyaki marassa nauyi,

Sai da yakoma asibitin ya kaiwa su 'ma' kayan ya biya kudin aikin da aka yiwa bahijjan da kudin magungunan da za abata sannan yatafi gida domin yin wanka,

Agaggauce yayi wanka ya shirya ya fito tsaf cikin farin yadi mai laushi shara shara wanda ya bayyanar da farar vest din da yasaka, kamar yadda ya saba komai nasa fari yasaka tun daga kan agogonshi har zuwa takalmin kafarsa hularshi ce kawai light blue mai ratsin fari ajiki, turaren _Special oud_ da _muqalatul shaikha_ yayi amfani dasu ya feshe jikinsa dasu,

Lokacin da ya koma asibitin misalin karfe 5:30 na yamma yasan yanzu dai bintinshi ta farfado, da Anty Bilkisu yayi clash ahanya hannunta dauke da flask din abinci,

Ganin 'ma' da papa suna dakin da bahijjan ke ciki ya sakashi kin shiga domin shi mutumne mai alkunya da kara,yafi minti 10 atsaye awaje yana jiran fitowarsu,yana nan tsaye har papa ya fito ya sameshi,

"A'a malam jabiru ya kake tsaye anan? Ka karasa ciki mana ai ta farfado"

Papa yace dashi yana murmushi fuskarsa cikeda annashuwa,

"Allah ya kara bata lafiya" jabir yafada yana kokarin shiga cikin dakin,

"Amin, amin" papa ya amsa yakara gaba,

Kofar dakin ya bude ya shiga idonshi fes akan gadon da bahijja ke kwance mamanta tana gaban gadon tana tattare mata rigar da tasaka mata sannan tana kokarin gyara mata zanin jikinta gudun kar ya rinka gogar wurin da aka yi mata aikin,

Anty Bilkisu ce ta tura masa kujera ya zauna yana gaisar dasu, bahijja najinshi yana magana cikin wannan sanyin muryar tashi kamar marar laka ajiki,

Dauke kanta tayi tayadda ma ba zasu iya hada ido ba, ganin yadda take cikinta awaje, kasan cikinta awaje yasa jabir jin wani irin kishi yana taso mishi, yanzu shikenan wani ya kalle masa cikin bintinshi da mararta,

Fita anty bilkisu tayi 'ma' itama ta mara mata baya, suna ficewa ya tashi daga kan kujerar da yake ya nufi gadon da bahijja take kwance,

"Sannu bintina, ya jikin naki?" Yafada ahankali cikin sanyin muryarshi bayan ya rankwafar da kanshi kusa da fuskarta,

Idan gadon da take kai yayi magana to itama tayi magana, shiru tayi masa ta rabu dashi amma kuma yanda ya kusanto jikinshi da nata yasata cikin wani irin wahalallen yanayi ga wani kamshi mai dadi wanda yake fita daga jikinsa duk ya cika mata hanci,

"Binti...!" Yakira sunanta bayan ya kai hannunshi kan nata ya dafe,

"Binti duk fushin ne haka zaisa ki k'i yimin magana? Haba bintina"

Har lokacin bata tanka masa ba asalima runtse idanuwanta tayi dama kuma fuskarta ba saitin da yake take kallo ba,

Tana jinsa yana murza yan yatsun hannunta da nashi amma tayi biris dashi domin itama ta dau alwashin sai ta rama abinda yayi mata sai ta wahalar dashi tayadda dakanshi sai ya furta yana sonta,domin duk iya zamansu bai taba sanar da ita wannan kalmar ba,

"Bintina yanzu haka doctors dinnan suka gane min surar jikinki, suka kalle min halittarki"

Nanma shiru tayi bata tanka masa ba, babu zato taji ya sunkuya ya fara yiwa wuyanta da saman kirjinta zafafan kiss, sake runtse idonta tayi domin rabon da taji wannan yanayi tun kafin su samu sabani dashi, tana jinshi ya dage yanata sinsinar jikinta musamman ma wuyanta amma har lokacin taki ta kulashi.

Jin alamun za bude kofa ya sanyashi matsawa daga gareta ya tsaya agaban gadon,

Anty Bilkisu ce ta shigo itada wata nurse wacce take dauke da magungunan bahijja,

Yana tsaye yana jinsu nurse din tagama karanta dokokin abubuwan da za a iya bawa bahijjan ayanzu taci,

Juyawa suka yi suka fita yayinda ita kuma 'ma' ta shigo cikin dakin, gaba daya jabir nauyin 'ma' yake ji dan haka ya juya yafita daga cikin dakin sai da bahijja taji fitarsa sannan ta iya jiyo da kanta tana kallon mamanta amma har acikin ranta wani irin son jabir ne taji yana sake zagaya jinin jikinta.

Misalin k'arfe 10 jabir ya leka cikin dakin yayi musu sallama cewar zai tafi gida,tunda bahijja taji maganarshi ta kawar da kanta ta rufe idanuwanta, murmushi yayi ya fita yana mai jinjina fushi irin na bahijja in banda abinta waye yake fushi da mijinsa irin haka,

Koda yaje gida ma kasa bacci yayi sai tunane tunanenta da ya addabi ruhinsa, sanin wannan tunanin bazai barshi ya runtsa ba ya sanyashi tashi ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito yafara gudanar da ibada.

Washe gari da safe da misalin karfe 9 ya shirya ya fita domin zuwa asibitin, lokacin da yashiga dakin iya bahijja da anty Bilkisu yagani domin dama tun jiya da daddare mamansu da papa suka tafi gida iya bilkisu aka bari awurinta,

Azaune yaganta ta jingina da pillow anty bilkisu tana hada mata tea dan kadan acikin cup, batare data kalleshi ba ta amshi cup din tea din ta fara kurba ahankali,

"Baban al'amin tunda kazo to bari naje gida nadawo, dama su mama nake jira amma tunda kazo shikenan"

Anty Bilkisu tafada sannan tafara tattare kwanukan abincin da aka kawo musu domin tafiya dashi,

"To babu damuwa sai kin dawo" jabir yabata amsa yana latsa wayarshi,

Bahijja kam bata so haka ba amma babu yadda ta iya sannan badan bata son agane tsakaninsu da jabir ba da ta cewa anty bilkisu kar tatafi,

Fita anty bilkisun tayi tana fadin "nima ba zama zanyi ba,yanzun nan zan dawo wanka kawai zan iyo"

Tashi jabir yayi ya nufi gadon yana kara waya akunnenshi,

"Ummu al'amin ga antyn al'amin din"

Tajishi ya fada tareda zama akusa da ita ya kara mata wayar akunnenta yana rada mata ahankali cewar "ga uwar gidanki zata gaisheki"

Bata ko jiyo ta kalleshi ba tafara magana ahankali irinta marassa lafiya, kallonta kawai jabir yake yanda ta dauke kanta taki koda kallon gefen da yake ita ala dole fushi take yi dashi,

Wurinda aka yanka ajikinta ya kalla, "binti me dan tumbi" yafada aranshi domin tana da tumbi kadan, yana rike da wayar akunnenta tagama magana da ummu suka fara da al'amin,

"My boy nayi missing dinka, yaushe zaka dawo ne?"

Bai jiyo amsar da al'amin yabata ba yaji tace,

"I luv u too my boy"

Janye kunnenta tayi alamun tagama wayar, rufe wayar yayi yasaka acikin aljihunsa yajiyo yana kallonta amma ita kam sam taki kallon koda sashen da yake ma,

Kurbar tea dinta taci gaba dayi har ta shanye tafara kiciniyar komawa ta kwanta amma ta kasa, yana zaune akusa da ita yana kallonta sai kokarin kwanciya take amma kuma abin ya gagara,

"Binti kice na kwantar dake mana, kodan yanzu kin daina yimin magana ko?"

Yace da ita tareda kai hannuwanshi ya taimaka mata ya kwantar da ita, sai bata rai take tasha kunu ta bata rai, shi abin natama dariya yake bashi,

Jikinta ya matsa, hannu tasa ta tureshi ba tareda ta kalleshi ba tace,

"Kabari kar ka fama min ciwo na"

Asaman kirjinta ya dora kanshi yamika hannunshi daya ya kamo nata,

"Binti banida bakin da zan baki hakuri amma dai kiyi hakurin, kisani ni bana daya daga cikin mutanen da basa aikata kuskure, binti duk mutum tara yake bai cika goma ba shiyasa baya iya tsallake kuskure, annabi ne kawai mutumin da ya cika sama da goma akomai amma mu sauran mutane dukkaninmu masu aikata kuskure ne, binti ni ba waliyyi bane, ba ma'asumi bane ba kuma masanin gaibu bane, kisani duk ilimin mutum duk tsoron Allahnshi to yanada tawaya awani wurin shiyasa dole sai muna yiwa junanmu uzuri,

Bama ni ba kowanne mutum arayuwar nan dole sai ana yi masa uzuri domin komai kirkinsa da kamewarshi to wata rana sai yayi kuskure dan haka ina mai sake baki hakuri akan abinda ya faru saboda ba laifina bane ni banida masaniyar dalilin zubewar cikinki, dr ne ya sanar dani cewa kina amfani da kwayoyin zubar da cikine shiyasa kiketa samun miscarriage dinnan, but now tunda nagane gaskiya shikenan yawuce kuma kin san duk namijin da zai ji matarshi tana aikata irin wannan to dolene ransa ya baci..!"

Yanda yafara bayaninshi har ya diga aya bahijja bata ce mishi uffan ba asalima ayanda take dazu yanzun ma haka take, amma taji mamaki mutuka wai da jabir yace mata dr ne yace itace take zubar da cikin datake samu, wasu zafafan hawayene suka zubo mata domin ita anata tunanin ya za ace tana aikata wannan abun bayan bata taba haihuwa ba, gara shi jabir yanada yaro amma kuma duk da haka yana son yasake samun wani to inaga ita wacce bata da kowa,

Dago kanshi yayi yana kallonta duk jin ranshi yake yi ya sosu saboda ganin yanda take hawaye gashi ranta abace, hannu yakai yafara shafe hawayen nata,

"Menene abin kuka kuma? Ba nariga da nabaki hakuri ba? Haba binti kina so hankalina yatashi ne?"

Bata bude idonta ba amma dai ta daina kukan sai dai har yanzu fuskarta babu walwala, shidai jabir ya rasa abinda yarinyar nan ta taka domin sam taki yi masa magana sannan taki koda kallonsa,

Suna nan ahaka har nurse ta shigo dauke da spirit domin gogewa bahijja wurin da aka yi mata aikin,

Yana zaune agefenta nurse din tafara aikinta, runtse ido kawai bahijja take yi amma fa tana jin zafin yana ratsata har cikin jijiyar jikinta, hannunta ya sake kamowa,
Chapter 58 · 0% Book details