← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 64

Sashe 18

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akan dining table ta jere masa su ta koma kan kujera ta zauna tana kallon yadda yake yin sallarsa a nutse har tana iya jiyo kira'ar karatun da yake yi cikin sanyayyiyar muryarshi gashi ko wanne harafi dalla dalla yake furtashi,

Tana nan zaune ya idar da sallar ya fara zikirin da ake yi bayan kowacce sallar farilla, yana gamawa ya daga hannayenshi sama ya fara kwararo addu'o'i, zuru tayi da ido tana kallonsa har ya gama ya tashi daga kan abun sallar.

Juyowa yayi ya kalleta, yayinda ita dinma shi take kallo,

"Welcome sir"

"Ya, gida? Ya zaman kadaici?" Ya tambayeta lokacin da ya wuce domin kunna tv, huda tv ya kamo ya tsaya yana kallon programme din da suke yi mai suna _learn how to correct your Qur'an recitation_,channel din ya bari ya koma kan kujera ya zauna wacce take nesa da ita.

"Sir ga abinci can ko na kawo maka nan?" Tafada cikin sanyin murya,

Kunyar gwasaleta yaji yace "eh kawo min nan" tashi tayi ta nufi dining table dan debo abincin, nan yabi bayanta da kallo yanda ko wanne bangare na jikinta ke juyawa yayinda take tafiya ga uban hips kaya guda kamar ita ta ajiyewa kanta gashi tanada mazaunai tubar kalla,

Ahankali ta kawo abincin gabansa ta ajiye ta koma kan kujerar ta zauna, faratanta ya kalla sai ya gansu a yanke ba irin zako zakon nan bane nan ya danji alamar cewar zai iya cin cooking din nata,

K'asa ya sauko ya dan zuba abincin baifi cokali biyar ba ya saka dan soye soyen agefe, ya dauki cinyar kaza guda daya, ahankali ya fara tsakurar abincin yana ci, kallonshi kawai take tana mamakin inda al'amin ya gado surutu domin shi mal jabir sam bashida yawan magana ga sanyi kamar me komai nasa a sanyaye,

Wayarshi ya dauka ya fara laluben number din ummu, tana shiga ta dauka kamar dama jira take,

"Abu al'amin ka tafi ka barni da kewarka"

"Kiyi hakuri, ai nakusa kawo al'amin"

"To ya ka sauka? Ina antyn al'amin?"

"Gata nan lfy lau, sai munyi magana anjima"

Katse wayar yayi ya dan kalli goodness kadan yace "ummu al'amin tana gaisheki"

"Ina amsawa ta fada idonta akan tv" zama tayi har ya kammala cin abincin sannan ta kwashe kwanukan ta nufi sashenta,

Shirin kwanciya tayi tabi lafiyar gado daga nan bata iya tashi ba saboda ayyukan da tasha sai wurin karfe 11 nasafe wannan dinma al'amin ne ya tasheta tana tsaka da bacci,

"Anty wake up, ki tashi kiyi min wanka"

Idonta ta bude guda daya "my boy zo muyi bacci kabari idan natashi sai inyi maka"

"Nidai ki tashi kiyi min wanka" dole babu yadda ta iya haka ta tashi taja hannunsa zuwa cikin bathroom ta hada ruwan zafi tayi masa wankan, akwatin kayansa ta dauko daga falo tasa acikin dakinta ta dauko masa kayan da zata saka masa, riga da wando yan kanti, tana gama shiryashi ta tuna da ba tayiwa abbunshi breakfast ba,

"Al'amin kai da wa kuka zo?"

"Abbuna ne yaje ya dauko ni"

Hannunshi taja zuwa cikin kitchen ta kunna wuta ta fara shirya abin karyawa, sanye take da rigar bacci iya gwiwarta, kanta babu dankwali rigar tata kalarta kalar ruwan hoda,

Dankali da kwai ta soya ta dafa ruwan zafi ta zubawa al'amin nasa ta dauki na abbun nashi ta fita bayan ta daura zani a saman rigar tata, lokacin da ta shiga part dinshi yana zaune da kaya agabansa yana waya, tiren kayan ta ajiye ta juya zata futa, da hannu yayi mata alamar ta tsaya.

Zaman jiransa tayi har ya gama wayar, gaisheshi tayi ya amsa fuskarsa babu yabo babu fallasa, jakar gabansa ya miko mata
"Ungo kayanki wannan na cikin ledar kuma Ummu al'amin ce ta bada akawo miki"

Amsa tayi tace ta gode sannan ta fita ta koma wurin al'amin tarar dashi tayi yanata kokarin kunna tv nan ta tsaya ta kunna masa ta kamo masa spacetoon arabic tashar cartoon ta larabci ta shiga wanka,

Tunda al'amin ya dawo taji gidan gwanin dadi, tsarabar da aka kawo mata ta dauko ta duba kayane masu kyau musamman ma dogayen rigunan da jabir ya sai mata gashi kayan baccin da ummu ma ta bayar a kawo mata suma sun hadu, cikin drawer taje ta ajiye kayan ta fito ta koma kitchen ta dora abincin rana.

Zama tayi awurin al'amin suka fara wasa, biye masa tayi kamar wata sa'arshi har abbunshi yazo kiransa dan su tafi masallaci,

"Anty ke meyasa bakya salla?"

Ya soko mata wannan tambayar wacce bata zata ba daga ita har abbunshi sai da suka yi mamaki,

"Ka tashi kaje kayi alwala kazo mu tafi salla kar ashiga muna nan"

Dagudu ya wuce bathroom dinta yayi alwala yazo ya dale hannun abbunshi suka tafi, yayinda suka barta da tunani lallai al'amin wayo ne dashi wato har ya lura da ita bata salla kenan.

Wunin ranar tayi shine tareda al'amin shi kuma jabir yana sashensa, sai bayan sallar isha lokacin sun dawo daga masallaci ta kama hannun al'amin suka je part dinsa, yana zaune yana karanta wani littafin larabci,

Anesa dashi suka zauna suka fara kallon tv,

"Anty kece tom nine jerry" al'amin ya fada yana dariya,

"Ni ba tom bace" ta bashi amsa,

"Lah anty tsaya kiga keken wasa na da abbuna ya kawo min" kwasa yayi da gudu ya shige bedroom din abbunshi Jim kadan sai gashi ya fito akan keken yana dariya,

"Anty zo ki hau mu tafi"

Dariya tayi ta kalleshi "wa zaka dauka a wannan keken naka? Zan tafi na barka yanzu ni kallo zanje nayi, sai ka taho" tashi tayi ta fita shi kuma yaci gaba da wasa da kekenshi har ya gaji ya sauka yaje kan cinyar abbunshi ya kwanta.

Karfe 10 ya dauko shi akan kafadarsa ya nufi part din goodness lokacin tana zaune a falo tana kallon Nigerian film,

"Gashi zo ki karbeshi yayi bacci" yafada a hankali, tashi tayi taje ta mika hannu zata karbeshi, hannunsa taji ta kama wurin karbar al'amin din, kankame abbunshi yayi idonsa a rufe,gashi ita kuma an matse mata hannu ajikin hannun abbunshi sai wani irin shock take ji ajikinta,

"Al'amin jeka wurin anty ka kwanta maza"

Dakyar ya yarda yasaki abbun nashi ta juya dashi ta kaishi cikin dakinta ta kwantar dashi, ta dawo falo taci gaba da kallonta. Haka zaman nasu ya kasance har na tsawon sati daya lokacin mal jabir ya koma aiki ya fara zuwa office,

Bayan ta yiwa al'amin wanka ta shiryashi ya tafi falo ya zauna ya fara yin game (tvgame),bathroom ta shiga domin yin wanka, daga cikin dakinta ta fara yiwa al'amin magana,

"Al'amin you should stay there, don't enter this room, don't come inside this room, did you hear me?

"Na'am anty" ya bata amsa domin shi komai sai dai yace na'am amma ko eh bai fiya fada ba,

Labulen dakin ta gyara ta shiga wanka tabar kofar toilet din a bude ba tare da ta rufe ba,

Mal jabir ne ya shigo ya samu al'amin yana game a falo "ina antyn ka al'amin?"

"Abbu tana daki" ya fada yaci gaba da yin game dinsa ta super Mario,

Kansa tsaye ba tare da tunanin komai ba yasa kai cikin dakin tareda kara wayarshi a kunnensa ya fara kiran secretary dinsa na office,

Yana shiga ya bude baki kenan da niyyar ya yi magana awaya ya hangota tana wanka nicked, kofar bathroom din a bude,

Duk jikinta kumfa ta jiyo kamshin turarensa cikin sauri ta karo kofar amma ina ya rigada ya ganta,

"Goodness wannan sakarcin fa? Ya zaki bar kofa a bude kuma kina wanka idan al'amin ya shigo fa?"

Kwara ruwa tayi ta dauraye jikinta ta fito,

"Sir nafada masa wanka zanyi, ni bana rufe toilet wallahi tsoro nake ji"

Juyawa yayi "natafi office sai na dawo"

Ficewa yayi ya tafi yana mamakin sakarci irin nata,yayinda ita kuma takoma gaban mirror don shiryawa. Sai yamma wurin 5 sannan ya dawo, sashensa ya wuce kai tsaye, anan ya samu goodness ta ajiye masa abincinsa a shirye akan dining,

Dagudu suka fito ita da al'amin suka nufi part dinsa yana kallonsu ta window, daidai kofar falon al'amin ya riketa ya wuce da gudu yana yi mata gwalo, a bayan kofa ta labe dan tasan zai sake fitowa yanzu yanzu,

Tashi jabir yayi dan zuwa wurin driver dinsa saboda yana son aikinsa cikin gari ya siyo masa watermelon,

Yana zuwa saitin kofar taji alamun tafiya da saurinta ta fito ta cafkoshi, caraf ta cafko hannun jabir,

"Sorry i thought al'amin ne"

Baice da ita komai ba ya wuce yayinda ita kuma ta shiga ciki tana neman al'amin din.

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/5, 12:25 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_51-53_

~~~Lokacin da ya wuce da sauri ta shige falonshi neman al'amin, hangoshi tayi hannunsa rikeda littafi yana karantawa da karfi,

"Lah yadkulul jannata lammamun, annamimi bazai shiga aljannah ba, rawahul bukari wa muslim, bukari da Muslim ne suka rawaito,

"Hey al'amin you dey hear"

"Anty abbuna ne yake koya min karatu"

"To maza ka iya before he come back"

"Na'am anty"

Cigaba da karatunshi yayi ita kuma tana zaune akan kujera tana sauraronsa har abbun nashi ya shigo hannunsa rikeda ledar kankana,

Mika mata yayi dan ta je ta yanyanka, amsa tayi ta fita taje kitchen dinta ta samu filet mai fadi ta dauki wuka ta fere kankanar tayi mata yanka mai kyau heart design,

Fork ta dauka tasa wani filet din daban ta rufe ta tafi kai masa, shi aduk yayan itatuwa yafi son kankana saboda yasan ko musulumci tana da amfani ajikin mutum,

Agabansa ta ajiye farantin kankanar ta koma saman kujera ta zauna, budewa yayi ya dauki fork din ya fara sha, matsawa kusa dashi al'amin yayi ya zubawa kankanar ido na tsawon yan sakannin da basu wuce biyu ba,

"Lah abbu kaga anty ta rubuta maka i love you acikin kankanar"

Wata dariya ce ta tahowa mal jabir wacce ta kusa sakashi kwarewa, cikin sauri ta kalli al'amin kafin tayi magana yaci gaba,

"Abbu dama kullum kullum sai naji anty tana cewa i love you abbun al'amin"

"Al'amin when did you started telling untruth?"
Chapter 18 · 0% Book details