Sashe 23
Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai yanzu ya dade da fita bazai yi ta zama acikin falon ba"
"No sir, yana ciki bai fita ba idan munje zaka gani"
"Muje Nagani" yace da ita yayinda yayi gaba ta juya tabishi a baya, ta bayansa ta tsaya take tafiya ahankali har suka shiga cikin falon, al'amin yana bayanta ya sadada ya jefa mata kadangaren robar yace "anty gashi nan ajikinki"
Wata kara ta saki ta kankame jabir ta baya tana faman shassheka irinta wanda ya tsorata,
"Wasa nake anty" har lokacin bata saki jabir ba tana rike da rigarsa ta baya, ahaka suka shiga dakinta ya dudduba ko ina tana makale dashi har ya gama caje dakin ya dawo falo nanma baiga komai ba, kofar falon ta Baya yaja ya rufe ya jiyo yana kallonta yanda ta wani rikeshi tamau kamar wacce za akwace mata shi,
"To ki sake ni mana tunda kinga babu komai ai aciki dama na fada miki bazai zauna ba ya dade da ficewa, kuma ki daina barin kofar baya a bude kina rufeta dan ta nan zai rinka shigowa"
"Yes Sir" ta fada tana mai sake rike rigarshi al'amin kuma yana binsu yana yi mata dariya,
Bata sakeshi ba har suka fita daga falon duk ta yamutsa masa rigar sa, sashensa suka koma gaba dayansu, a falo ya barsu ya shiga bedroom dinsa yayi wanka ya sake kayan jikinsa daga shaddar dazu zuwa doguwar jallabiya fara, kansa babu hula ya dawo falon ya hau kan dining ya fara cin abinci jalop din shinkafa da kifi, yana ci yana kallon su sunata kiriniya suna yin puzzle game, sai da ya kammala sannan ya dawo inda suke,
"Goodness ki fara hadawa al'amin kayanshi domin nan da sati biyu zan kaishi wurin ummunshi"
Kanta ta dago zuciyarta babu dadi tace "to sir"
Shi kansa al'amin din yayi wani irin sabo sosai da goodness din wanda ya haifar da shakuwa sosai a tsakaninsu, kamar wadanda aka zarewa laka ajiki haka suka dawo.
Tun daga lokacin ta wankewa al'amin kayansa gaba daya ta harhada masa dukkan abubuwan da tasan nasa ne sa'arta daya mamanta ta kirata a waya tace ta sanar da mijinta zasu tafi okene nan da sati biyu tunda hakane tana ganin tafiyar tasu zata zo lokaci daya da tasu al'amin amma duk da haka tasan zata yi missing din al'amin sosai.
Lokacin da ta sanar da jabir maganar tafiyarsu okene ita da mamanta bai hanata ba saboda yana ganin itama zata samu damar rage damuwar da zata shiga na tafiyarsu shida al'amin, kudi ya bata _50_ thousands yace tayi duk wata hidimarta ta tafiyar domin daga can har Lagos zasuje ita da ma da yayarta Bilkisu.
Ranar da su jabir zasu tafi ta shirya al'amin tayi masa kwalliya cikin shadda fara riga da wando harda hula shi kuma jabir ya shirya cikin yadi kalar ruwan madara da hula itama milk colour, hatta takalminsa milk colour ne hannunsa daure da agogon azurfa fari,
"Al'amin zanyi missing dinka sosai, idan kaje ka gaida ummunka, ka zama good boy kamar yanda na sanka" tafada hawaye suna kokarin zubo mata,
"Nagode good anty, abbuna yace bazan dade ba zan dawo kuma yanzu tare zaku nayin wasa kafin na dawo" ya fada cikin surutunshi irin na yara,
Hannunta jabir ya kama "menene abin kukan? Sai kace wanda za a mutu? Kiyi hakuri pls, sai na dawo"
Yana gama fadin haka ya saki hannunta ya kama na al'amin suka fita zuwa harabar gidan tana tsaye tana hangosu har suka shisshiga mota, motar ta harba tabar harabar gidan.
Komawa tayi ta zauna tana kuka marar sauti domin ta shaku da al'amin sosai, yaron ya shiga ranta saboda basirarsa gashi komai nasa irin na mahaifinsa ne, haka ta zauna ranar kamar wata marar lafiya har dare yayi, koda taje makwancinta ma al'amin taketa tunawa musamman irin wannan lokacin idan tazo ta kwantar dashi sai taji yana addu'a,
_"Da sunanka ya Allah nake mutuwa, kuma nake rayuwa"_
Idan kuma Safiya tayi abinda yake fara fada shine _"Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rayani bayan ya karbi rayuwata kuma gareshi tashi yake"_ irin wadannan yan guntu guntun addu'o'in da yake yi duk ta rikesu, gashi wani abin burgewar ko bandaki zasuje idan zata yi masa wanka sai yayi addu'a kafin ya shiga hakama idan zai fito sai taji yana fadar wata kalma.
Haka ta kasance cikin kewar al'amin da jabir har bacci yayi nasarar yin gaba da ita, washe gari da asubar fari ta tashi tayi wanka ta shirya ta dauki jakar kayanta ta tafi gidan ma lokacin har Bilkisu yayarta ta karaso dan haka babu bata lokaci suka dunguma suka tafi tasha anan suka samu mota suka dauki hanyar okene.
Tun safe basu suka isaba sai bayan sallar isha, gaba daya goodness ta gama gajiya likis, basu jima da sauka ba jabir ya kirata, gaisawa kawai suka yi ya bata al'amin suka fara hira, sun jima suna shirmensu tana biye masa kafin suka yi sallama tun daga lokacin kullum sai jabir ya hadasu a waya ita da al'amin yayita bata labarin _madina_ da labarin ummunshi ko kuma abbunshi ya siyo masa kaza yau sunje wuri kaza.
Satinsu daya a okene suka tafi Lagos tunda suka shiga Lagos taga kayayyakin da suka burgeta na maza nan ta zage ta siyawa mr cool dinta domin ta dauki aniyar mayar dashi niga acikin gidanta, underwear na maza ta sissiya masa
Sannan ta sai masa short trousers kala kala wurin kala biyar ta koma ta kwaso masa body hug irin ta samari wacce tasan zata yi masa kyau mutuka sannan ta debar masa jeans,da hadaddun kayan bacci na maza masu ado na burgewa da bada sha'awa wanda tasan zasu karbeshi iya karba, akwati medium size sai da ta cikashi da kayan jabir,
_"no more wear any doguwar riga or jallabiya inside my house again my cool"_ta fada tana muskilin murmushi, kulewa suka yi acikin daki ita da yayarta tana mai sake bata wasu dabaru na kulawa da mai gida wanda ba duk macece ta sansu ba, zan kawo muku su a shafi na gaba.
_*Ummi Shatu*_👌🏻
[10/11, 2:52 PM] +234 701 117 6189: [9/12, 1:07 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE............!*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_61-63_
~~~Dabarun kulawa da mai gida wanda ba duk macece ta sansu ba yayarta ta fara bata, dafa kafadarta anty Bilkisu tayi tace da ita,
"My dear sister hak'ik'a nasan a zaman da kikayi ko kuma ki keyi agidan aurenki baki taba sanin mai ya kamata kiyiwa mijinki ko kuma ki aiwatar gareshi ba dan haka to ga shawarwari ko kuma ince hanyoyi guda goma sha biyar wanda suka kamata ace ko wacce mace ta sansu kuma ta kiyayesu domin samar da zaman lafiya tsakaninta da mai gidanta da kuma tabbatar da dankon kauna a tsakaninsu, ina so ki bude kunnuwanki sosai ki saurare ni da kyau domin fahintar karatun da zan koyar dake a halin yanzu,
Abu na farko da ya kamata ki sani kuma ki kiyaye shine daraja mijinki da kuma ganin girmansa da kimarsa, anan ina nufin kar ki kuskura ki fara kace nace da mijinki ta fannin zamantakewar auratayya kar wai dan kina ganin ya zama kamar abokinki ki rainashi, a'a anfi so mace ta zama tana bawa mijinta wani girma na daban acikin zuciyarta da kuma fili,
Na biyu kuma shine ki girmama iyayensa da yan uwansa tamkar yanda zaki girmama naki iyayen da yan uwan kar ki kuskura kiyi aiki da wannan karin maganar wacce hausawa ke cewa "'ba a iya musu ya dangin miji"',duk namiji yana son a girmama iyayensa da yan uwansa,
Abu na uku shine ki zama mai mutukar hakuri da juriya agidan aurenki domin zaman aure zama ne na hakuri da kawaici, ki k'i ji ki k'i gani sai ki zauna lafiya da mijinki,
Abu na hudu kuma shine kar ki zama d'aya daga cikin matan nan masu bayyanar da sirrin mazajensu da sirrin gidan aurensu ga kawaye ko kuma abokan gaisawa hakan haramun ne,
Sai abu na biyar shine ki kasance mai tattalin dukiyar mijinki ma'ana banda almubazzaranci da kayan miji, ki kasance mai tattalin dukiyarsa da kayansa domin kowanne namiji yana k'in jinin yaga yasha wahala ya nemo abu sannan an wulakanta,
Abu na shida shine kar ki zama mai yawan bin k'wakk'wafin mijinki, komai yake yi idonki da kunnenki akai, kar ki zama haka domin maza basu kaunar mace mai bin diddigin abubuwan da suke yi,
Abu na bakwai shine binciken wayar miji ko kuma abubuwan da ba su shafeki ba, kar ki zama mai yawan binciken al'amuran mijinki wanda bai saki aciki ba domin duk namiji baya son bincike da tuhuma,
Sai abu na takwas shine kula da abincin mijinki, ki zama macen data kware wurin iya girki domin hakan yana sawa miji yaji kin kara shiga cikin ransa,
Abu na tara shine ki zama macen da ta iya furtawa mai gidanta maganganu masu laushi da taushi, kar ki zama daya daga cikin matan da basu iya magana ba duk kalmar da tazo bakinsu sai su kwabawa mai gida ita,kar ki zama daga cikinsu,
Abu na goma shine kar ki yarda ki rinka daga muryarki sama da ta mijinki, akoda yaushe idan kina magana da mijinki to ya zamana muryarki ce a kasa tasa a sama,
Abu na goma sha daya shine ki zama mai iya kallon soyayya domin kallon da zaki yiwa mijinki ana so ya banbanta da kallon da zaki yiwa sauran mutane, idan kina kallon miji anfi son ki karkada idanuwanki ki sauya musu launi su koma tamkar kina jin bacci yanda zaki ja hankalinsa gareki,
Sai abu na goma sha biyu shine kula da tsafta, mata da yawa suna sakaci wurin kulawa da tsabtar jikinsu da ta muhallinsu, to agaskiya ya kamata su gyara saboda duk namijin duniya baya son mace k'azama yafi son kullum yaga gidanki a tsaftace jikinki a tsaftace,