Sashe 19
Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Anty wlh ba karya nake ba kullum idan kina bacci ina jinki kina fada"
Shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta, shidai abbun nashi jinsa yake yana kallonsa bai iya cemasa komai ba saboda ya kula wayon al'amin yawane dashi,
Tashi tayi ta fice ta koma sashenta ta kunna kallo ta zauna domin shi jabir kullum daga labarai sai sunnah tv sai huda tv yake kunnawa ita kuma ba kallonsu take ba dan haka ta kunna Nigerian film dinta ta soma kallo.
Karfe 9 da yan mintina al'amin ya shigo lokacin tana kwance tana kallon film din _lover boy_,
"Anty i am sleepy, ki kaini inyi bacci"
Mikewa tayi "woh al'amin your problem neva finish oh oh"
Hannunsa taja zuwa cikin dakinta taje ta kwantar dashi ta kunna masa fan ta juya da niyyar fita maganarshi ta dawo da ita,
"Anty abbuna ma dey love you"
"Oh God, al'amin kayi baccinka pls"
"To anty sai da safe" komawa yayi ya kwanta ita kuma ta fita daga dakin aranta tana tunanin ai jabir ba ya sonta baya kaunarta kawai dai yana zaune da itane a matsayin zaman kaddara, tunda duk ta gama ganin alamun hakan a tattare dashi,
Kallon film dinta taci gaba dayi har wurin 11 alokacin jabir ya turo kofa ya shigo cikin falon, kallonshi tayi kansa babu hula yana sanye da jallabiya kalar ruwan madara,
Tamkar wani dan saurayi haka taga ya zame mata domin ko kadan baiyi kama da magidanci ba indai ba wanda ya sani ba babu wanda zai kalleshi yace yana da mata harda yaro,
Dan yatsanta tasa acikin bakinta tana kallonshi,
"Abokin wasan naki yayi bacci ne?"
"He dey sleep inside my bedroom"
"Oya take this"
Wata bakar leda ya mika mata mai dauke da wani ganye aciki kamar ciyawa,
"Sir what's this?"
"Ki dafa min yanzu amma kisaka Lipton aciki, lemon grass ne"
"Ok sir" tashi tayi shikuma ya shiga bedroom dinta inda al'amin yake kwance yana bacci, addu'o'i yayi masa ya shafa masa ajikinsa sannan yaja blanket ya lullubeshi ya fito,
Part dinsa ya koma, yana zuwa ya shiga wanka. Cikin mintuna kadan goodness ta gama dafa masa shayin ta dauka ta nufi sashensa, a falo ta ajiye masa amma baya ciki hakan yasata karasawa kofar dakin nasa ta murda ta leka daidai lokacin ya fito daga bathroom daga shi sai gajeren wando wannan shine karo na farko da ta taba ganinsa ahaka.
Cikin sauri taja kofar tana fadin "i sorry sir"
Ji tayi yaja kofar ya bude da sauri ta sauke idonta kasa harda saka hannuwanta biyu ta rufe fuskarta,
Murmushi yayi acikin zuciyarsa yace "lallai ma yarinyar nan ba gwara ni ba akan ke tunda ke kullum barin kofa kike abude idan zaki yi wanka"
Ciki ya koma ya ziro doguwar riga ya fito har lokacin idanuwanta arufe suke da tafukan hannunta,
"Have you add sugar inside that thing?"
"No sir" tafada tana bude idanuwanta, "ok let me check i think i have a little honey here"
Wata drawer yajawo wacce ke ajiye acikin falon nashi, kwalbar Zuma ya dauko amma babu ta kare ko ba afada ba yasan al'amin ne ya shanye sauran,
"Go and bring sugar pls" yace da ita,
"Ok" fita tayi taje sashenta ta dauko masa kwalin sugar guda daya ta kawo masa yana nan zaune inda ta barshi yana goge kunnensa da abin goge kunne,idonsa a lumshe yace ta ajiye sugar din, ajiyewa tayi ta fita ta koma part dinta.
Washe gari da safe bayan ta shirya al'amin ta gama hada abin karyawa tayi wanka, abincin jabir ta dauka ta tafi sashensa ta kai masa, lokacin da ta shiga baya falon yana bedroom dinsa ya shiga wanka,
Part dinta taje ta zubo musu break din ita da al'amin suna ci yana bata labarai tanata dariya, suna kammalawa ta shiga kitchen ta fara kiciniyar hada abincin rana, jallop din cous cous tayi niyyar yi, kayan miya ta zuba a turmi dan jajjagawa, daga falo tana jiyo hayaniyar cartoon din da al'amin yake kallo,
Turmin ta dauka ta kai corridor ta ajiye, anan dama take duk wani abu da ya shafi daka saboda shi wurin ba tiles bane siminti ne,
Jajjaga kayan miyan ta fara sai daf da zata gama wani cukurin attaruhu ya taso ya fantsalo mata a fuskarsa nan yayi tsalle ya watsu cikin idanuwanta,
"Ahhhhhhhhhh! My eyes, al'amin come and give me hand, come and aid me pls, pepe done enter my eyes oh oh"
Shiru taji wannan ya tabbatar mata da cewar al'amin ya fice daga falon,
"Oh God! My eyes, my eyes! Laluben hanya tayi dan taje ta wanke fuskarta, tana kokarin shigowa falo jabir ya shigo cikin shirinsa tsaf na zuwa office,
Ganinta yayi idanuwanta arufe kamar wata makauniya tana neman hanya, "goodness what's happen?"
"Sir my eyes, Pepe done enter my eyes"
Tafada tana dafa bango, wani karo tayi da dan karamin stoll din dake ajiye gefen kujera ta tafi tagal tagal zata fad'i cikin zafin nama yayi saurin tarota ta fada kirjinsa,
Wani irin yanayine ya ziyarcesu gaba dayansu wanda ba zasu iya fassara shi ba, "where are you going now?"
Ya tambayeta tana rik'e acikin kirjinsa"
"Sir i dey go bathroom to wash my face"
Bai sake magana ba ya juya da ita ya nufi cikin bedroom dinta da ita har lokacin yana rik'e da ita akan kirjinsa, wani kamshi mai dad'i take shak'a daga cikin jikinsa wanda yau taji ya banbanta da sauran da tasan yana shafawa,
Cikin bathroom ya kaita ya dauki hannunta guda daya ya dora ajikin fanfo ya kunna mata, cikin sauri ta fara wanke fuskarta,
"Sir pls give me soup" tace dashi tana mutsuttsuka idonta,
Sabulun yana kusa da ita amma bata ganshi ba, dauka yayi ya dora mata akan hannunta, karb'a tayi ta soma gogashi akan fuskarta,
"Washhh this pepe want to blinded my eyes"
Juyawa yayi ya fita daga bathroom din har yaje tsakiyar dakinta ya jiyota tana fitowa,
"Sir bai fita ba wlh it dey inside my eyes especially this one" ta nuna idonta na dama,
"Sir pls hure min, yana ciki"
Yana nan tsaye cak har ta karaso gabansa, kanta ya d'ago ya bude idonta daya yasa bakinsa ya fara hure mata, tabbas dagaske take ga kwayar cikin attaruhu nan guda daya acikin idonta yana gani, nan yaci gaba da huhhure mata amma fur kwayar attaruhun nan taki fita ita kuma goodness ji take kamar za tayi hauka dan zafin da take mata acikin idonta,
Hannunta yaja ya zaunar da ita abakin gado yaci gaba da hure mata idon, gaba daya idonta yayi ja bau kamar me yin afolo,
Dakyar kwayar nan ta fice ta can gefen idonta, dan yatsansa yasa ya cirota murza idon taci gaba dayi domin wani radadi yake mata,
"Kin ganta" ya mika mata yatsansa dan ta gani,
"Abbu na ashe kaima kana son anty na ko?"
Suka jiyo maganar al'amin daga bakin kofa, da gudu ya karaso ciki, "sannu anty, abbu me kayi mata take kuka?"
"Al'amin babu abinda nayi mata yajine ya shiga idonta shine na cire mata"
"Ya salam, sannu anty, taso muje falo ki kalli cartoon" hannunta yaja ta tashi tabishi, murmushi mal jabir yayi yabi bayansu, kyalesu yayi ya tafi office saboda yaga hankalinsu ya tafi kan wasan yaran da suke kallo a tashar mbc 3,sai da taji saukin idon nata sannan taje ta karasa girkin amma har alokacin tana jin zafin yajin ga wani irin ja da idon yayi tasan dama dole ne zai zame mata eye ache.
Misalin karfe 5:30 mal jabir ya dawo gida, sashenta ya fara zuwa amma basa ciki, nan yayi tunanin to ko suna cikin falonsa, can dinma da yaje basa ciki, mamaki ya yi to ko ina yaran nan suka tafi?
Agurguje ya shiga yayi wanka ya fito sai alokacin yajiyo hayaniyar su abayan part dinsa,ta window ya lekasu, goodness sanye cikin green din t shirt da blue din jeans idonta daure da bakin k'yalle tana neman al'amin, wanda ke tsaye a bayanta sai faman ja mata riga yake suna dariya amma ta kasa kamashi,
Murmushi yayi na jin dadi domin al'amin ya sake sosai da goodness saboda yadda ta sakar masa fuska takoma yarinya karama kamar age mate dinshi yasan ba dan goodness ba da tuni al'amin ya addabeshi ya kaishi wurin ummunshi amma yanzu ko zancenta baya yi iyakaci su gaisa a waya,
Kaya ta taka ta saki yar kara "oh God"
"Anty ba oh God ake cewa ba, annabi ya kasance idan wani abun da yake k'i ya faru agareshi sai yace Alhamdulillahi ala kulli halin, idan kuma na farin ciki ya zo masa sai yace Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihatu, anty kema kiyi koyi da annabi sai ki samu lada"
"Thank you al'amin zanyi nima"
Sakin labulen window din yayi yakoma cikin falo yaje ya zauna akan dining ya zuba cous cous din data dafa ya dan ci, bayan ya gamane ya tashi ya zagaya baya inda su goodness ke wasa ita da al'amin,
Lokacin da ya karasa wurin yanzu al'amin dinne fuskarshi adaure da kyallen ita kuma goodness sai dariya take yi masa itama tana rama abinda yayi mata dazu,
"Welcome sir" tafada tana jan rigar al'amin,
"Abbu na kadawo? Har kai zan kama yanzu ba iya anty kadai zan kama ba"
"Thank you, al'amin nikuma daga zuwana za ace harda ni?"
Dagudu al'amin ya taho,cikin sauri goodness ta matsa tabar wurin,
"Abbu in dai na kamaka to kai za adaurawa"
Da sauri ya matsa ya koma jikin karfen tanki ya tsaya, ita kuwa goodness tana bayan wata kujerar karfe dake ajiye awurin, bayan karfen tankin ya nufa ganin haka yasa goodness fara yiwa malam jabir dariya ta hanyar toshe bakinta da hannunta,
Fitowa yayi da niyyar sauya waje, caraf al'amin ya rikeshi yana cewa "yes na kama wani tsakanin anty ko abbu"
Cire kyallen yayi yana ganin abbunsa ya fara dariya,
"Abbu yanzu kai za adaurawa"
"Ya na iya al'amin tunda na kawo kaina, nidai kawai tsautsayine ya fito dani har nazo wurinku"
Karbar kyallen yayi ya daure fuskarsa ya fara lalubensu, da gudu al'amin ya arce yayi bayan dakin abbunshi ya tsaya, ita kuma goodness ta labe agefen karfen tanki,