← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 64

Sashe 8

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Danta ta dauka ta saba a kafada ta fice acikin falon ba tareda ta jira amsarshi ba, idan da sabo ta saba da wannan halin nashi na rashin mayar da amsa shi komai wahala yake masa domin bashida zafi ko kadan sanyinsa yayi yawa,

Tana fita ya shiga dakinsa ya shige toilet ya yi wanka ya fito ya hau kan gadonshi ya kwanta yana tunani acikin zuciyarshi,

"Ya dace naje na kwana a dakin yarinyar nan to amma ni bazan iya ba saboda inada kyankyami shiyasa tun farko banyi murna da auren nan ba, tayaya zan auri macen da idan na kusanceta ba zatayi wanka ba, idan tayi period tagama ba zata yi wanka ba, idan tayi fitsari ba lallai ne tayi tsarki ba"

Yafada acikin zuciyarshi duk kuwa da yasan cewa tana da wani babban hakki akansa, kwanciyarshi yayi tareda yin baccinshi, sadaf sadaf ummu al'amin ta leko cikin dakin nasa ta window dinshi ta hangoshi yana bacci a hankali ta sulale ta koma side dinta dama tun lokacin data kwantar da al'amin ta dawo ta labe tana son taga fitarshi amma sai taji shiru wannan ya bata tabbacin cewa bazaije dakin amaryar ba yau.

***

Washe gari da safe misalin karfe 9 goodness ta farka daga naunauyan baccin da tayi ta bi dakinta da kallo da alamun babu wanda ya shigo, taba baki tayi ta mike ta cire gown din jikinta ta daura towel ta shiga bathroom wanda shima ya tsaru kamar ba bayi ba, wanka tayi ta fito tazo ta shirya ta saka jeans da t shirt, jeans din blue rigar kuma pink mai gajeren hannu an zana cartoon guda biyu ajiki an rubuta _don't tell my momy_ turaren rocking girl tayi amfani dashi ta dauki wayarta ta fita falo anan ta fara kokarin hada kayan kallonta ta jojjona komai ta kamo wata channel ta music vox Africa sannan channel din suna saka Nigerian films, wakar p square ta fara saurare cikin wakarsa ta _you are my African queen_ volume ta kara yadda zata rinka jiyowa har a kitchen, tashi tayi ta shiga kitchen ta kunna electric stove ta dora ruwan zafi, kamshin turarensa kawai ta jiyo taji ta rikice tuni zuciyarta ta fara harbawa da karfi numfashinta ya ci gaba da fita da sauri da sauri,

Cikin diriricewa ta nufo kofar kitchen din ta leko yana tsaye ya bawa kofar kitchen din baya yasha farin yadi mai santsi da bakar hula hannunshi rikeda remote yana rage volume din data kure,

Tamkar marar gaskiya ta karaso cikin falon, cikin faduwar gaba tace,

"Good morning sir"

Batare da ya jiyo ya kalleta ba ya amsa gamida ajiye remote din yace "akwai abinda kike da bukata?"

"No sir, but banida brush da maclean" tafada muryarta tana rawa,

"Ok za akawo miki" yana kaiwa nan yayi gaba abinshi ba tareda ya jiyo ba kallo tabi bayanshi dashi tana murmushi har yafice, cikin kitchen ta koma tana murmushi amma har lokacin gabanta bai daina faduwa ba, ruwan zafin data dora ta tarar da ya kusa konewa saura kadan, saukewa tayi ta debo acikin cup komai na bukata gashi nan acikin wani dan karamin store, kayan tea ta debo ta koma falo ta hada tea din ta fara kurba tana yi tana kallon wani Nigerian film mai suna _love avenge_ nutsuwa tayi taci gaba da kallon film din har ta shanye ruwan tea dinta domin babu bread.

Tana nan zaune har wurin azahar sai lokacin ta tashi ta shiga kitchen ta dafa indomie guda biyu ta dawo falo taci ta kwanta nan wani barcin ya dauketa sai yamma lis sannan ta tashi, cikinya wayam take jinsa hakan ya tilasta mata shiga kitchen ta sake dafa wata indomie din ta fito ta zauna taci rabi ta rufe sauran ta shiga wanka lokacin _6_ saura kwata, yar doguwar riga tasa marar nauyi ta dawo falo dirin tsayuwar motar da taji ya sata lekawa ta window din falonta, hangoshi tayi yana fitowa daga cikin mota daga gani agajiye yake, al'amin ya taho da gudu ya rungumeshi, leda taga ya bawa al'amin yana nuno masa part dinta amma da alama sako zai kawo mata, da gudu al'amin din ya taho wurinta shi kuma Malam jabir ya nufi sashensa, burum taji al'amin ya bude kofa ya shigo,

"Gashi inji abbuna, gashi inji abbuna"

Juyowa tayi ta amshi ledar tana cewa "thank you good boy, my regard to your abbu" da gudu ya juya ya nufi dakin abbunshi yana zuwa ya tarar dashi tsaye shida ummu,

"Abbu tana gaisheka, kaji abbu,"

"Al'amin naji" yafada yana cire hular kanshi, juyawa ummu tayi ta fita tana tabe baki aranta tana cewa "fi'ilin banza danma dai har yau bai kwana a dakinki ba" tana fita al'amin ya rufa mata baya da gudu, shikam jabir dakinshi ya shiga yaje yayi wanka yafito ya sanya jallabiya ruwan madara yasaka dogon wandon jeans aciki ya saka yar karamar hula irinta larabawa ya dawo falo ya zauna zaman cin abinci.

Ita kuwa goodness lokacin da ta karbi ledar da al'amin ya kawo mata zama tayi ta bude ledar brush tagani guda biyu da macleans guda biyu manya sannan da ultra pad guda biyu suma, murmushi tayi ta dauki ledar ta kaita dakinta ta sake dawowa falo ta kunna tv tafara kallo tana nan zaune ta hangoshi hannunsa rikeda na al'amin yana sanye cikin jallabiya wacce tayi mutukar yi masa kyau ahankali ta tashi taje jikin window taci gaba da kallonsa yana tsaye yana yiwa watch man magana wanda bata iya jiyo abinda yake fada amma tana hango bakinshi mul mul yana motsi wani azababben sonshi taji yana ratsata kafin ta ankara har yaja hannun al'amin sun fita daga gidan, _"wow you look so good my cool"_ tafada tana murmushi.

_*Ummi Shatu*_👌🏻

[8/26, 9:00 AM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_33-34_

~~~ _"wow you look so good my cool"_ tafada tana murmushi tareda lumshe idanuwanta tana mai hango kykkyawar fuskarshi mai dauke da dan karamin bakinsa wanda yake tsananin bata sha'awa,

Matsawa tayi daga jikin window din taje ta zauna akan kujera tayi jugum tana kallon tv wacce itace take zame mata abokiyar hira akoda yaushe, tana nan zaune har _9_ tayi lokacin ta jiyo bude kofar gate tasan ko ba afada mata ba shine ya dawo cikin sauri ta tashi taje ta leka window nan ta hangoshi rikeda al'amin a kafadarshi sannan ya kara waya a kunnenshi da alama call yake amsawa, tana tsaye tana kallonsa har ya shige part din farko, sai da kulewa hangenta sannan ta iya barin jikin window din ta koma falo ta karkashe kayan kallon ta wuce cikin dakinta, kan gadonta ta fada ta rungume _pillow_ tana tunanin mijinta da kyar bacci yayi nasarar daukarta.

Washe gari da safe bata tashi da wuri ba sai wurin _8:30_ dan haka wanka kawai tayi tasa mini skirt da yar body hug baka mai hoton lips ajiki yasha jan baki ja an rubuta _cute_,memory din wayarta ta cire ta jona ajikin _DVD_ dinta ta kunna wakar Akon cikin wakarshi ta _I like your style baby_ ita dama can mayyar jin music ce domin yana sanyata nishadi shiyasa yake burgeta, volume ta kure karar sautin ta cika cikin falon har tana iya jiyowa daga cikin dakinta, dama tunda ta tashi part dinta yana rufe ko kofar falo bata budeba,

_bedroom_ dinta ta shiga ta fara gyarawa ta dan goggoge shi sannan ta shiga dayan _bedroom_ din ta shareshi sama sama domin shi babu abinda ya batashi dan bata taba kwana aciki ba, fitowa tayi ta shiga kitchen shima ta dan kintsa shi sannan ta fito da mooper a hannunta da bokiti tana dan rawa tana bin wakar _"i like your style baby, heyy baby, ohhh bab.....!"_ cak taja ta tsaya jikinta ya fara rawa zuciyarta ta shiga harbawa cikin sauri sakamakon ganinshi da tayi tsaye ya dafa kujerar falon guda daya yana kallonta, ita fa sam bata ji alamun motsin bude kofa ba kai _in fact_ ma ita ko bude kofar ta yau ba tayi ba amma ai tunda maigida da gidansa bai kamata tayi mamakin ganinsa ba amma dai duk da hakan _"am very astonishe"_ tafada cikin zuciyarta,

Cikin sauri ta yar da _mooper_ din ta dire bokitin omon dake hannunta taje ta dauki remote ta rage volume din ta juyo tana cewa _"good morning sir"_
Falon yake bi da kallo sannan ya amsa gaisuwarta yana sanye cikin lallausan farin boyel yasha hula ja mai ratsin fari ajiki, hatta takalmin kafarshi farine _half cover_ yana latsa wayar hannunshi kirar _Galaxy E8_ kamshin turarenshi kamar kullum yana barazanar rusa kwakwalwarta.

_"morning"_ yafada yana kara wayar a kunnenshi cikin sanyin muryarshi ya fara magana,

"Wa alaikumus salam, ka turashi yaje kawai ni bazan samu damar zuwa ba, a'a yanzu office zanje zamuyi waya"

Kashe wayar yayi acikin ranshi yana cewa "mayyar jin kida kodai yarinyar nan tana da aljanune?" Ta gefen ido yadan kalleta tayi tsumu tsumu gabanta sai faduwa yake, acikin ranshi baiji dadiba dan ya fahimci kamar tsoronshi take ji, ba tareda yace komai ba ya nufi kofa zai fita "adawo lafiya sir" "yawwa" yabata amsa a takaice abun mamaki sai da ya murza key sannan ya bude kofar, to da ko ta ina ya shigo? Ta tambayi kanta, bokitinta da mooper taje ta dauka tazo taci gaba da mopping dinta tanayi tana rawa tana bin wakar da take saurare ta _before in love_.
Chapter 8 · 0% Book details