← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 64

Sashe 13

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kam goodness aikinta take yi hankalinta a kwance har ta gama gyara ko ina na bangaren ta, kitchen ta shiga duk da ba wani yunwa take jiba sosai amma tana da bukatar tasha ruwan lipton, lokacin da ta shiga kitchen shikuma ya fito daga bathroom din dakinsa cumb ya dauka ya je gaban mirror ya fara gyara sumar kansa da gemunsa, daga kan da zaiyi ya hangota acikin kitchen tana kaiwa da komowa, kasa ci gaba da abinda yake yi yayi yaci gaba da kallonta har ta fice daga cikin kitchen din shi dai bazai iya fassara yanayin da yake jinta acikin ransa ba na so ko k'i, turaren right man ya fesa ya saka yar hula ya fito domin tafiya masallaci, part din ummu ya shiga ya kama hannun al'amin suka fita.

Karfe 9 da yan mintuna ya dawo gidan shida al'amin, part din ummu ya kaishi sannan ya fito ya shiga part din goodness wacce a lokacin take bararraje akan center carpet tana shan iska tana kallon wani Nigerian film, ahankali ya bude kofar ya shiga cikin falon, motsin da taji ya sata saurin juyowa, tsayawa yayi daga bayanta yayinda ta tashi zaune amma ta kasa juyawa ta kalleshi saboda nauyinsa da taji tana ji yanzu,

"Naji sakon ki awurin al'amin" ya fada da sanyayyiyar muryarsa, shiru tayi babu amsa,

"Ko ba kiji abinda nafada ba? Nace naji sakonki awurin al'amin"

Nanma shirun ta sakeyi sannan bata iya juyawa ta kalleshi ba,

"Sai da safe to" ya fada tareda juyawa ya fita, bayansa tabi da kallo tana murmushi ashe dai al'amin ya fada masa sakon, "hmm kana burgeni sosai, i like your style" tafada tana murmushi wanda ji take yi tamkar tabishi ta rungumeshi dan so.

Washe gari bata tashi da wuri ba saboda dare ta raba tana kallo sai wurin 2 ta kwanta, shiyasa ta makara, tana tsaka da bacci kamar a mafarki ta jiyo cool voice dinshi yana kiranta zumbur ta tashi tana mutsuttsuke idanuwanta da bayan hannunta tsabar gigita ta manta ma da kayan baccine ajikinta, karo suka yi a daidai kofar shigowa dakin nata shi ya sako kai da nufin shigowa ita kuma tasa kai da niyyar fita falo tana daga labule da niyyar fita taji ta ci karo dashi take ta jita acikin kirjinsa, wayar hannunshi ce ta silmiye ta fadi hakan yasata saurin durkusa dan dauko masa cikin rashin sa'a shima hakan yayi niyya take suka sake yin wani karon,

Mikewa yayi yayinda itama ta dago hannunta rike da wayar tashi, idonta a kasa ta mika masa wayar tana cewa

_"am sorry sir"_

Jikinta yabi da kallo wanda ke saye cikin wata hadaddiyar rigar barci armless, kalarta yellow marar nauyi tsawonta bazai wuce iya gwiwa ba da dan karamin wandonta iya cinya, kallonsa ya maida kan fuskarta har yanzu idonta kasa yake kallo takasa kallonsa, jin shiru bai amshi wayar ba yasata dagowa caraf suka hada ido dashi, manyan idanuwan nan nashi cikin nata, ahankali ta sauke idonta tabi kafarsa da kallo, takalminsa farine half cover, kamar kullum farin lallausan yadine ajikinsa da jar hula, kamshin turarensa na _explore_ da _right man_ sun taru sun bada wani daddadan kamshi na musamman, fuskar nan tashi tamkar ya shafa farar _powder_,

Hannunsa ya mika ya karbi wayar,"morning sir" tafada a hankali

"Morning, how was your night?" Ya fada ahankali, shiru tayi bata amsa ba, ganin haka ya sashi juyawa zai fita,

"Excuse me sir" cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba,

"Am hearing you" yafada yana kallon agogon azurfar dake daure a hannunsa,

"Sir zanje saloon ne anjima sannan ina son zuwa church in the evening"

"You can go" yafada tareda ciro 1000 ya miko mata ba tareda ya jiyo ba, da sauri ta karasa ta mika nata hannun da niyyar karbar kudin nan ta hado da yan yatsunsa biyu ba tareda ta saniba, wani shock taji cikin sauri ta matsa baya, bai sake cewa uffan ba ya fice ya barta tsaye tana kallonsa, gaskiya ita dai yana mutukar burgeta gashi yauma ya tafi ya bar mata sanyayayyen kamshinsa a cikin hancinta, juyawa tayi ta fada kan gado taci gaba da tunaninsa acikin ranta.

Wurin misalin karfe 12 tabar gida ta tafi shagon wata yar church dinsu mai suna blessing dama tun asali awurinta take yin kitso da saloon, gyaran gashi aka yi mata sannan aka jona mata attach nan ya zubo har gadon bayanta, ba atsaya a iya nan ba sai da aka yi mata gyaran farce gamida fenteshi sosai, sai wurin 3 suka gama ta dauki jakarta ta nufi church.

Karfe shida daidai ta taso daga church din ta nufo gidanta, lokacin da ta karaso an kusa shiga masallaci, sauka tayi daga kan machine din da ta hawo ta bude yar karamar jakarta ta mikawa dan acabar kudinsa ta juya ta nufi hanyar shiga gida, a kofar masallaci taga mutane wasu zazzaune wasu kuma na yin alwala, haka ta wucesu zata shiga cikin gidan, tana zuwa bakin gate taga wasu mutane su biyu da mal jabir yana tsaye yana yi musu bayanin da bazata iya gane ko na menene ba, kallo mutanen suka bita dashi har shi kansa jabir din sai da ya rakata da ido, tasha riga da wando ga gashi har gadon bayanta ko dan kwali babu akanta hannunta daya rike da Bible dayan kuma rikeda yar jakarta, tana wucewa daya daga cikin wadanda ke tsaye kusa dashi yace

"Malam wannan fa? Me zataje tayi agidanka kodai tayi batan kai ne?"

Shiru yayi tsabar takaice bai iya bada amsaba saboda yasan ko bai fada ba idan sun bar wurinshi dole ne suyi zancen amma yau yayi damarar takawa goodness burki akan wannan sakarcin nata, shi bazai yarda da wannan banzar dabi'ar ba.

Bayan ta shiga gidan part dinta ta bude ta shiga, ko zama ba tayi ba ta shiga wanka ta fito, three quarter da yar body hug tasa ta shiga kitchen ta dafa indomie ta debota ta kawo falo ta kunna tv taci ta koshi, kwanon ta ture ta mayar da hankalinta kan film din da take kallo a tashar _African magic_ mai suna _the present time_ hankalinta duk ya tattara akan wannan film din domin ganin tirka tirkar dake ciki, bude kofar da akayi ya sata bin kofar da kallo dan ganin waye zai shigo,

Shine ya shigo amma daga gani yana cikin fushi "goodness as from to day kar ki kuskura na sake ganinki da riga da wando a waje, are you crazy? Who told you wadannan kayan da kike sakawa na mutumcine? Kina son ki bata min sunane a garinnan ko me? Daga yau sai yau kar ki bari naganki da irin kayan dazu awaje, sannan its compulsory ki rinka daura head tied, wannan ai zancen banza ne kullum ki ringa fita gashinki awaje jikinki awaje, i can't tolerate this"

Tunda ya fara fadan bakinsa kawai take kallo wanda yayi tsananin bata sha'awa, "am sorry sir" tafada cikin kalar tausayi,

"Hold your sorry, sorry for yourself"

Juyawa yayi ya fita bai sake cewa komai ba, ajiyar zuciya ta saki tare da rike kanta "hmmm to plan for you how to love me is my headache now, problems neva finish in this house oh oh" tafada tana kallon agogon falon wanda ya nuna karfe 10 saura minti 5,tv din ta kashe ta tashi ta shiga dakinta ta kwanta yau duk yanda taso ta ga karshen film dinnan amma yanzu taji ya fita daga ranta gaba daya, juyi tayi tareda jan dan karamin tsaki,juyi tayi ta mika hannunta kan bedside drawer dinta ta dauki Bible dinta tafara dubawa, ganin bata gane komai yasata ajiyeshi ta tashi tafita taje ta rurrufe ko ina na part dinta saboda bata son gobe jabir ya shigo dan tasan haduwar ba zai yi mata dadi ba, dawowa tayi ta kwanta amma kuma ta kasa baccin akalla sai da takai karfe 1 kafin bacci yayi nasarar daukarta. Bata iya tashi ba sai karfe 11 nasafe lokacin kam tasan abu al'amin ya dade a office, sabgoginta ta shiga yi amma yau bata da niyyar zuwa church, tana falonta tana gugar kayan sawarta al'amin ya shigo hannunsa rikeda chocolate,

"My dear son i miss you so much, where did you hide?"

"Anty ummu na tace nazo na gaisheki" yafada yana kokarin bare chocolate din hannunsa,

"Oh al'amin clever boy, abbuna, ummuna, every one na your own ba?"

TV din da take kallo ya kalla, "anty zan kalla carton"

"Oya carry that remote and change the channel, al'amin ina abbunka?"

"Ya tafi office baije dani ba"

"Ayya sorry my dear, na kawo maka wani chocolate din ta kara akan naka?"

Girgiza kai yayi "abbuna ya siyo min jiya da yawa da yawa yace in tasha nawane ni daya"

Murmushi tayi tana son hirar al'amin domin yaron akwai kwakwalwar daukar abu gashi komansa irin na abbun shi ne shiyasa yaron ya shiga ranta, biye masa tayi yayita yi mata labari har tsawon wani lokaci kafin ya fice ya koma wurin ummunshi.

Zama tayi shiru bayan fitar al'amin taci gaba da gugar ta har yamma saida ta goge kayanta tsaf kafin ta tashi ta dora girki taci tayi wanka ta fito bayan ta shirya cikin wasu riga da skirt blue masu adon stones ajiki.

Falo ta dawo ta rufe kofar falon sannan ta nutse cikin kujera ta fara kallon channel din _music plus_ tashar zallar wakoki kawai ake nunawa, tana nan kwance har ta jiyo dirin motar jabir alamun ya dawo daga office, bata tashi ba taci gaba da kallonta har duhu yayi, tunani ta fara yi acikin ranta lallai ya kamata taje ta sake bashi hakuri tunda itace tayi masa laifi kuma gaskiya ya fada mata wadannan kayan da take sawa na iya janyo zubewar mutumcinsa a idon jama'a, da wannan shawarar ta zuciyarta ta aminta cewar anjima taje ta bashi hakuri.
Chapter 13 · 0% Book details