← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 64

Sashe 35

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa yayi ya fita baice da ita komai ba, nan tasake komawa toilet tayi wani wankan ta fito, shiryawa tayi cikin riga da wando na jeans baki rigar kuma light green mai gajeren hannu,

Abincin da ta shirya ta dauka ta nufi sashen jabir, yana zaune yana waya dasu al'amin da ummu, abincin ta ajiye ta tasashi agaba kamar zata shige cikin cikinsa, abin har dariya yaso bashi gashi ta wani kafeshi da ido duk motsin da bakinsa yake yi akan idonta ne,

Wayar ya mika mata yaja abincin ya zuba ya fara ci yana sauraren hirarta itada al'amin wanda gaba daya yarintace aciki,

Har yagama cin abincin bata gama wayar da al'amin din ba, lemon kwakwar da tayi yasha madara dan haka ba karamin dadi yayiwa jabir ba, sai da ya shanye rabin jug amma abincin kadan yaci,

Kan doguwar kujera ya koma ya zauna ya kamo huda tv yafara kallon wani program da suke yi alokacin mai taken _Da'awah workshop_,

Yana jin lokacin da goodness tagama wayar ta ajiye,guntun abincin da ya rage acikin filet tasa hannunta zata ci sam ta manta da yankewar da tayi dazu a yatsanta, tana saka hannunta taji yaji ya ratsa wurin, babu shiri ta zubar abincin ta zabura tayi inda jabir ke zaune,

Tana zuwa tasaka kuka tare da zama akan cinyarsa,

"Abbu yaji..."

Hannun ta mika masa tana kuka,

Rike hannun nata yayi baiyi wata wata ba yasa dan yatsan abakinsa ya fara tsotse mata shi,

Kanta ta kwantar acikin kirjinshi tana jin wani sanyi har cikin ranta,

Tsotsar dan yatsan nata yaci gaba dayi yanayi yana hura mata iskar bakinshi a wurin, acikin zuciyarsa kuma yana tuna rak'i irin na mata su mata babu wuya sun yiwa abu kuka komai kankantarsa.

In banda haka menene abin kuka dan yaji yashiga wurin da ta yanke,

Cusa kanta cikin jikinshi take tayi tana shakar kamshin turarensa na _beautiful touch_ wanda ya cakudu da kamshin _special oud_ ita dai arayuwarta tana tsananin son jabir domin jin sonshi take har acikin jinin jikinta yana yawo,

Mak'aleshi tai tayi shikuma sai tsotsar yatsan nata yake yana hura mata iska awurin, gaba daya ta gama shagala sai kamshinsa take shaka mai mutukar dadi, hakika babu abinda yafi kamshi dadi ajikin mutum musamman ma Ma'aurata amma wasu mazan sam tsafta bata damesu ba harma wasu matan suma duk samma kal, ya kamata arinka kulawa da tsafta domin tana daga cikin imani inji fiyayyen halitta, sannan turare abune da yake kara soyayya, duk lokacin da mutum ya kasance mai mu'amula da turare to kowa zakaga yana burin zama kusa dashi amma idan sabanin hakane to mutane basa kaunar hada wurin zama dashi,

Tana ta yan tunane tunanenta idonta a lumshe bata san lokacin da bacci ya dauketa ba shi kansa jabir bai san tayi baccin ba kawai dai yaji shiru ta daina kakkamashi sabanin dazu data rinka kankameshi tamkar zata koma cikin cikinsa,tana faman cuccusa kanta acikin kirjinsa,

Yana rikeda hannun nata acikin tattausan hannunsa wanda yafi na baby pherty Xarah laushi, dan yatsan abakinshi ya dago manyan idanuwanshi ya kai dubansa gareta nan yaganta tana bacci abinta,

"Wuh binti case, komai kuka kike masa, hydrogen kuka, pepe kuka,ruwan zafi kuka, zan so naga ranar da zaki je maternity" ya fada ahankali kamar da wani yake maganar, koda yake matanfa kenan,ya ayyana hakan aranshi,

Zare dan yatsan nata yayi daga bakinshi ya zameta daga jikinshi ya kwantar da ita akan doguwar kujerar ya tsaya yana kallonta yana tunanin anya kuwa idan tayi kwakkwaran juyi ba zata fado ba,

"Kai ai yarinyar ce ta fiya lukutanci yanzu idan nace zan kaita daki wuya zansha, kila ma ta tashi tai tayi min rikici" ya fadi hakan acikin zuciyarshi,

Rabuwa yayi da ita ya shiga cikin _bedroom_ dinshi yayi wanka yasha manyan kaya, dafaffen boyel light blue riga da wando harda babbar riga, hularshi samfarin dinkin zannabukar itama light blue,agogon da ya daura na azurfa ne kirar kamfanin _Gucci_ ,kamar koda yaushe turare masu dadin kamshi da sanyi ya fesa, yasaka takalmi half cover light blue ahankali ya fito daga cikin dakin nasa idonsa akan goodness wacce take mike tana faman bacci,

Sadaf sadaf ya fice daga falon domin yasan idan har ta tashi cewa zata yi sai tabishi,

Fita yayi shida mal idi driver, shagon aski ya fara zuwa bayan ya fito kuma ya nufi gidan mahaifinsa,

Acikin babban falonshi ya sameshi zaune yana hutawa amma hannunsa kuma rike yake da carbi yana ja,

Bayan yan gaishe gaishe ne Malam yake ce masa,

"Kaga abinda nake fada maka ko jabiru? Yanzu gashi ta sanadiyyarka musulunci ya samu karuwa, dama shiyasa tun farko nace kayi hakuri wannan yarinyar *wani haske* ce agareka kamar yadda kaima kake *wani haske* acikin rayuwarta, sanin kankane duk mutumin da yayi sanadiyyar da wani ya shiga musulunci yanada rabo mai girma, rannan kawai ina zaune sai ga yarinyar nan tazo min da magana mai dadi cewar zata karbi musulunci, agaskiya nayi farin ciki kuma dan Allah jabiru ka zauna da yarinyar nan zama na amana, tunda yanzu kasan dole zata fuskanci matsalar rayuwa dalilin shiga musuluncin da tayi, sannan kuma yanzu ta amshi sunan mahaifiyarka, wato BAHIJJA, nasan ta sanar dakai komai"

Tunda Malam yafara wadannan bayanan jabir sakin dan mitsitsin bakinshi yayi yana kallon malam domin bashida masaniyar duk wadannan abubuwan, haba lallai biri yayi kama da mutum tunda dazu lokacin da ya tarar da ita tana bacci tana farkawa da salatin annabi ta fara,bayan haka kuma lokacin da zata karbi pad awurinshi ce masa tayi yau bata salla,sannan lokacin da yana madina tafada masa cewar yanzu ta koma bahijja sai dai shi sam bai yarda ba ashe dagaske take, wani farin cikine marar misaltuwa ya soma shigarsa ga wani yanayi da ya samu kanshi aciki, kyakkyawar fuskarta ya shiga hangowa acikin zuciyarsa,

"Jabiru lafiya?" Malam ya tambayeshi jin yayi shiru bai bashi amsa ba,

Sai alokacin ya dawo cikin hayyacinshi,

"Lafiya lau malam, Allah ya kara girma, Allah yasa ta shiga musuluncin kenan har abada kuma Allah yasa ta mutu akansa"

"Amin jabiru",nan Malam yayita saka masa albarka yana yi musu kyakkyawar addu'a shida iyalansa, awurin malam yayi zamansa bai koma gida ba har wurin 9 nadare.

***

Tunda jabir ya fita ya barta take bacci sai daf da magrib ta iya tashi, bude idonta tayi taganta akan kujera,

Tunowa tayi da abinda ya haddasa mata barcin, wani murmushi tayi tana mai kallon dan yatsan nata wanda jabir dazu yayita tsotsa kamar ya samu sweet, "tabbas maganar Anty Bilkisu ta zama gaskiya" tafada cikin zuciyarta domin itace ta bata wannan sirrin cewar awurin mijinta ta zamto yar karamar yarinya tamkar yar 14,sannan ta dimamci shagwaba kamar yar yaye hakan zai sa miji ya mace akan kaunarta,

Yanzu gashi tun ba aje ko inaba har tafara ganin amfanin shagwaba,murmushi ta sake yi akaro na biyu ta tashi taje wurin abincin da tabari dazu bata ci ba, dauka tayi taci ta koshi sannan ta kwashe kwanukan ta nufi sashenta aranta tana tunanin yadda akayi jabir yabar gidan batare da taji motsin fitarsa ba,

Sabon wanka tayi ta hade cikin wata doguwar riga ja mai siririn hannu, tattauran gashinta ta kama ta tufke tanayi tana tsaki domin duk ya yi under grow, dolenta tasaka masa relaxer indai tana son taji sawaba gashi gashin mai cika ne cukus,

Turarruka masu kamshi ta dan feffesa amma sai taji kamshinsu baiyi mata dadi irin na jabir ba, sashensa taje ta shiga _bedroom_ dinshi taje gaban mirror ta dauki nasa ta feffesa nan dakin ya gauraye da kamshinsa,

Fitowa tayi yanzu jinta take kamar suna tare dashi saboda ga irin kamshinsa nan tana shaka,

Part dinta ta koma ta kunna kallo yanzu bata yin kallon ma da yawa sama sama take yinsa, ganin har 9 tayi yasata fara tunanin to ina jabir ya tafi kodai wurin ta ukun ya tafi ne, itafa ta ukun nan ta shiga ranta tun lokacin da jabir ya fada taji ta kasa mantawa da maganar.

Tana nan zaune ita kadai tana kallo har 9:30 tayi,

Idonta kyar akan tv ko kiftawa bata yi ya turo kofar ya shigo tun kafin yayi sallama kamshin turarenshi ya ziyarci hancinta,

Dagowa tayi ta kalleshi lokacin da yake rufe kofar bakinshi dauke da sallama,

Sallamar ta amsa tana mai cigaba da kallonsa yau dinnan ba karamin kyau yayi ba cikin blue din boyel din da yasa,

"Wowww....!" Tafada ahankali tana kallonsa,

Zama yayi akan kujera "wato bakya jin magana ko? Har yanzu kina nan da wannan mayen kallon Daren da kikeyi ko? Dama baki daina ba?"

Kallonsa ta sake yi kamar yaune tafara ganinsa "abbu wlh ba nayi, anadade inkai 11"

Tafada cikin shagwaba,

"Ahaf" kawai yace ya mike zai fita,

Mikewa tayi da sauri, "abbu tsayani mu tafi tare"

Kayan kallon ta kashe ta bishi suka fita tare, a falonshi ta zauna ta fara duba kayan ciye ciyen da ya shigo dasu, kaza ce gasasshiya da fruits su kankana, apple, banana, oranges da sauransu, sai kuma chocolate wanda tasan ko ba afada mata ba ita ya siyowa,

Filet da fork ta dauko da wuka ta zauna ta yanyanka masa fruits din tabar sauran da zummar gobe zata yi musu lemon kankana dasu,

Tana tsaka da shan chocolate dinta ya fito sanye da kayan bacci, _maroon_ colour masu santsi riga da wando, tana kasa akan carpet azaune shi kuma yana kan kujera zaune, akan stool din gabanshi ta ajiye masa fruits din takoma ta zauna taci gaba da shan chocolate dinta sai da tasha da yawa sannan ta fara cin gasasshiyar kazar, yana zaune yana kallonta ta gefen ido yanda bama zata san yana kallonta dinba,

Sai da taci rabin kazar sannan ta tashi ta dauki tsinken sakace hakori tafara sakatar hakorinta tana son cire naman da ya makale mata ahakori, kasa cirewa tayi dan haka ta matsa kusa da jabir,

Kneel down tayi agabansa ta mika masa tsinken,

"Abbu pls ka cire min, nakasa cirewa"

Kallonta yayi ya karbi tsinken "oya bude bakin" budewa tayi ta daga kanta ya fara cire mata, ido ta runtse ta dafe hannunsa wanda ya dafe kanta dashi,
Chapter 35 · 0% Book details