← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 64

Sashe 21

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rigar ba karamin kyau tayi mata ba gashi tayi rolling wanda indai ba saninta kayi ba babu abinda zai hana ka dauka bahaushiya ce ita,

Dagudu al'amin yaje ya kama hannunta "sannu anty kin warke? Ya daina yi miki ciwo? Yanzu babu jini ko?"

"Wannan antyn naka al'amin ai Raguwa ce tunda tana yiwa hydrogen kuka" ya fada da niyyar zolayarta,

Kallonsa tayi yanda yayi maganar yaso bata dariya amma sai ta dake bata yi ba,

"Muje ko, ko har yanzu baki daina jin tsoron hydrogen din bane?"

Murmushi tayi ita gaba daya yau abbun al'amin mamaki yake bata yanda ya sake yake janta da wasa, ashe dama haka yake? Ya iya jan magana ga iya soyayya kamar wanda ya zauna a class aka koya masa,sai dai ita tanada masaniyar baya sonta kawai yana karanta matane saboda danshi al'amin sannan yana zaune da ita ne a bisa k'addara wacce masu iya magana kance ta riga fata,

Hannun al'amin ta kama suka fita yana biye dasu a baya har tsakar gida, mal idi ya kira ya karbi key din mota yace zaije chemist din baya ya dawo,

Da kanshi yayi driving, goodness na zaune agaba al'amin na kan cinyarta, sautin kira'ar karatun al'qur'ani tana tashi sama sama cikin muryar sheikh Ahmad Sulaiman kano inda yake karanta suratul taubah,

Bayan layinsu ya zagaya sai gasu a wani chemist (Al haq medicine & cosmetics store),dan satar kallon fuskarshi tayi yayi bala'in yi mata kyau.

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/9, 9:17 PM] Ummi A'isha👌🏻:

*WANI HASKE*

_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

_Sak'on gaisuwa da godiya ga"yan k'ungiyar fik'ira writers group 1and 2,bisa jinjinar da kuka yimin akan wannan littafi da nake rubutawa na wani haske, hak'ika nayi mutuk'ar farin ciki ganin akwai littattafai bila adadin amma acikinsu kuka zab'i nawa k'waya daya kuka yabeshi tare da yimin jinjina, ummu abdul naga sak'onki kuma nayi murna da ganinsa Allah yabar zumunci, ummi A'isha tana sonku._

_57-58_

~~~Zuba masa ido tayi bata ko k'iftawa tana kallonsa yana kokarin zare key din motar, "muje ko" ya fada ahankali, dan mitsil din bakinsa ta kalla yanda yake motsawa da k'yar idan yana yin magana,

Al'amin ta sauke ta fito tabi bayanshi har zuwa cikin chemist din,

Suna shiga suka samu wani nurse yana dan rubuce rubuce nan jabir yayi masa bayanin ciwon da goodness taji, tashi nurse din yayi yazo inda take zaune ya kalli d'an yatsan nata wanda har ya kumbure yayi suntum,

Kayan dressing ya d'ebo yazo inda take zaune ai tana had'a ido da hydrogen ta mik'e tsaye,

"Any problem?", jabir ya tambayeta,

"Sir hydrogen, pls kar asa min shi" ta fada kamar wacce zata yi kuka,

Nurse din ya fad'awa cewar ya saka mata hydrogen agida yanzu dressing kawai za ayi,

Take aka d'an goggoge mata d'an yatsan nata aka yi mata dressing suka fito, cikin motar suka koma ta dora al'amin akan cinyarta, shigowa ciki yayi yana kallonsu ita da al'amin din,

"Abbu kaima kana tsoron hydrogen ko kamar anty?"

D'an k'ayataccen murmushi yayi wanda ya k'awata fuskarshi sannan ya kalli goodness ta gefen ido,

"Ga mai yiwa hydrogen kuka nan antyn ka"

Ya bawa al'amin amsa, kallonshi tayi gaba d'aya ya mayar da hankalinsa akan driving din da yake yi, bata yi magana ba sai shida al'amin ne keta hirarsu har suka koma gida,suna shiga tafito hannunta rike da na al'amin suka shiga part dinta, doguwar rigar jikinta kawai ta cire ta dawo falo ta gyara inda jinin da ya zuba dazu ya babbata, tana gama gyaran wurin ta koma kitchen ta dora abincin rana,tuwon alabo miyar ganye ta yi tana kammalawa ta shiga wanka kamar kullum k'ofar bathroom din a bude ta barta, tana wankan jabir ya shiga dakin domin dawowarsu kenan daga masallaci sallar azahar shida al'amin,

"Wai ba zaki daina wanka toilet a bud'e ba" ya fada tare da juyawa zai fita daga cikin d'akin,

"Sorry sir i have finish, yanzu zan fito"

Ba tareda ya jiyo ba ya fice ya nufi sashensa, yana zuwa ya zaunar da al'amin a kusa dashi ya fara koya masa wani hadisi.

Tana fitowa daga wanka ta shirya cikin riga da skirt ta dauki abincin jabir ta nufi part dinsa, tana shiga tun daga babban falo ta jiyo muryar al'amin yana karatu,

"An abi hurairata, an karb'o daga abi huraira radiyallahu anhu, Allah ya k'ara masa yarda,k'ala yace, k'ala rasulullahi sallallahu alaihi wassalama, manzon Allah yabo da amincin Allah su tabbata agareshi yace, man la yashkurun nasa, duk wanda baya godewa mutane, la yashkurullaha, baya godewa Allah"

Saka kai tayi ta shiga cikin falon nasa tana murmushi domin tsarin irin yadda jabir ke bawa al'amin tarbiya abin yana burgeta she like his fathering,

Hannunta dauke da food flasks ta karasa kan dining table ta ajiye tareda dawowa wurinsu,

Zama tayi ta zubawa jabir ido yana zaune hannunsa rike da littafin _sahihul bukhari_ yana dubawa, ido ta ware taci gaba da kallonsa har tsawon wani lokaci,babu zato ya dago kansa caraf suka hada ido dashi,

"Akwai damuwa ne?" Ya fada yana kallonta,

"Me ya faru?" Ta tambayeshi, mayar da kansa yayi kan karatun da yake yi ba tareda ya kara yin magana ba hakan ya sake bata damar ci gaba da kallonsa,

"Abbu anty tanata kallonka tun d'azu" al'amin ya fada yana girgiza abbunshi,

D'agowa yayi ya sauke idonsa akan goodness wacce ta mayar da kallonta ga tv,

Murmushi yayi ya tashi ya shiga _bedroom_ dinshi domin yin wanka, yana tashi ta jawo al'amin,

"Al'amin me yasa baka jin magana? Uhum? Am asking you? Yaushe ka ganni ina kallon dad dinka?"

"Anty naganki mana sai kallonshi kike yi, ko ya zama tv ne?"

Murmushi tayi tajashi jikinta tana dariya, "ohh al'amin you are talkative"

"Anty ina jin yunwa"

"Oya tashi muje muci abinci to"

Mikewa suka yi suka koma sashenta anan ta kunna wak'ar _if do me i do you..._,zaunar da al'amin tayi ta kawo musu abincin ta ajiye suka fara ci,

"Anty me yasa kike yawan jin kid'a?" Al'amin ya tambayeta,

"Al'amin yana sakani cikin nishad'i ne that's why"

Ta bashi amsa tana jinjina basira irin ta al'amin domin komai mutum yake yi yana haddane dashi,

"Anty yawan sauraron kid'a yana sanya munafurci acikin zuciya, amma sauraron karatun alqur'ani yana sakawa zuciya nutsuwa da farin ciki"

Spoon din hannunta ta ajiye ta tsurawa al'amin ido tare da kama hannunshi, "al'amin a ina kake koyan wadannan abubuwan masu ban mamaki?"

Dariya yayi irin tasu ta yara, "anty abbuna da ummuna ne ke koya min, kema idan kina so abbuna zai koya miki"

Murmushi ta saki tana wani tunani acikin zuciyarta, "al'amin ina son abbunka sosai, abbunka ya zame min wani bangare na rayuwata, i can't do without him, he's parts and parcels of my life, i like him soo much"

Lokacin da take yin wadannan maganganun jabir yana tsaye a kofar falon yana saurarensu, kuma duk maganganun da tayi yajisu acikin kunnensa but shi matsalarsa guda daya ce bazai iya nuna mata soyayya acikin wannan yanayin da take ciki ba domin bata da tsarki shi kuma mutum ne shi mai tsananin kyankyamin kazanta komai kankantarta,

"Anty abbuna ma yana sonki soo much" al'amin ya fada yana dariya,

Bude kofar yayi ya shiga cikin falon suna zaune suna cin abinci ga _music_ nan yana tashi k'asa k'asa,

Gefenta ya wuce ya zauna yana kallonsu, "abbu yanzu anty take zancenka"

"To al'amin ka manta idan ana cin abinci ba a magana har sai an kammala?"

"Abbu na manta ne" ya fada yana rufe bakinshi da hannunshi,

Wani sanyayyen murmushi jabir yayi tareda kallon goodness wacce take ta sussunkuyar da kai k'asa domin bata son had'a ido dashi saboda akwai wani sirri a k'unshe cikin idanuwansa wanda ita bata iya jurewa,

"Goodness zan fita ina son zanje wata unguwa da aka gayyaceni domin bud'e wani sabon masallaci"

"Abbu zan bika nima"

"A'a al'amin ka zauna awurin antynka kaji, bazan jima ba zan dawo"

"Adawo lafiya sir" goodness ta fada tana kallonshi lokacin da yake mikewa domin fita,

"Abbu ka siyo min chocolate" al'amin yayi tsagal ya fada,

"Zan siyo maka,antynka fa me zan siyo mata?" Yana tsaye a bakin k'ofa ba tare da ya jiyo ba,

"Sir alewar tsinke" goodness ta bashi amsa, murmushi yayi acikin ranshi kuma yana mamakin k'uruciya irin tata shiyasa lokuta da dama yake danganta yarintarta da irin ta al'amin, bud'e kofa yayi ya fita ba tare da yayi magana ba,

Yana fita goodness ta kalli al'amin "al'amin meye ambition dinka a rayuwa?"

"Anty ina son idan na girma na zama kamar abbuna nima ina tara mutane ina koya musu karatun alqur'ani saboda annabi yace '''mafi alkairin cikinku sune wadanda suka san alqur'ani kuma suka koyar dashi"' kinga abbuna ma yana koyawa mutane"

"Good boy, ina sonka my boy" mikewa tayi ta shiga cikin bedroom dinta tabar al'amin yana k'arasa cin abincin.

Tunda jabir ya fita bai dawoba sai misalin k'arfe 8:30 bayan sallar isha ko al'amin ma ranar sai agida yayi salla baije masallaci ba saboda baya nan,yana idar da sallar taji ya fara karatunsa kamar kullum annabi yace "'sallu kama ra'aitumuni usalli, kuyi salla kamar yadda kuka ga ina salla"'.

Lokacin da ya shiga gidan basa part din goodness hakan ya sashi tunanin k'ila suna sashensa ai kuwa hakan take domin yana shiga ya hangosu suna wasa goodness tana yi musu after money amma da yake wayon al'amin yawane dashi sai runto yake yi mata,

Sallama yayi ahankali ya shiga, da sauri suka d'ago suka kalleshi yayinda al'amin ya tashi da gudu yaje ya rungume shi,

Ciki suka karasa yana rikeda hannun al'amin, "welcome sir" goodness ta fada tana kallonsu,

"Yawwa anty" ya fada ba tareda ya kalleta ba,murmushi tayi ta kalli dan mitsitin bakinsa wanda ya iya fadar magana sannan yayi fuska,in banda haka taya zai kirata da anty,

Ledar hannunshi ya bawa al'amin "maza kaiwa anty ta baka naka"

Ledar ta karba sautin sune ita da al'amin, alewar tsinke da chocolate manya manya, jan hannun al'amin tayi suka koma part dinta suka zauna suka fara shan kayan zakin da ya kawo musu, mintina kadan al'amin yayi bacci dan haka ta kwantar dashi kan cinyarta taci gaba da tsotsar alewar tsinkenta, tana kallon tv,
Chapter 21 · 0% Book details