← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 64

Sashe 54

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama tasa kafadar ta dafa tana kallon dan mitsitsin bakinshi mai kyau "abbu shiyasa nake son zama dakai, aduk lokacin da muke tare kana yawaita sammin ilimin da ubangiji ya hore maka, bazan iya kwatanta irin son da nake yi maka acikin raina ba" kwalla ya gani tana kokarin kwaranyowa daga idonta,

Hannunshi yasa yafara kokarin share mata kwallar,

"To kuma menene abin yin kuka? Haba binti meye abin kuka, duk wanda kake so to zaka tashi tare dashi aranar karshe, mutum yana tashine tareda wanda yake so inji annabi Muhammad (S.A.W) shiyasa ake son duk wanda zaka so zaka kaunata to ya kasance nagari domin tare za atasheku, yanzu dai kije kiyi sallar kar nasake tsayar dake"

Ganin tana tsaye taki yin gaba taki baya ya sanyashi nannade hannun rigarshi ya dauketa ya shiga toilet da ita, alwalar ya dauro mata ya fito da ita akafadarsa sai da suka zo tsakiyar dakin sannan ya ajiyeta tanata faman dariya,

"Ashe abbuna yanada karfi"

"Ai binti bama ke kadai ba har ku biyu zan iya dauka keda cikinki wata tara"

"Abbu dagaske?"

"Dagaske mana yarinya"

Doguwar riga ta zira tana murmushi, salla ta tayar shikuma ya fita falo domin yana son yin waya da uwar gidanshi.

Tunda ta idar da sallar ta mike akan abun sallar domin ta gaji iya gajiya, tana nan akwance jabir ya shigo "a'a binti kin gama gyaran naki part dinne?"

"Abbu ba yau ba,yanzu nadawo dakinka kafin nagyara nawa"

Akusa da ita yaje ya zauna,

"Sannu binti na ai kinyi aiki, bari nayi miki tausa"

Kanta ta mayar kan cinyarsa yafara matsa mata dukkanin gabobin jikinta.

***

Kwanansu 3 da dawowa jabir ya koma office amma sai da yasha rigimar bahijja kafin ta barshi ya tafi hakan ya sanyashi niyyar sakata awata makarantar islamiyya wacce ake zuwa kullum daga karfe 10 nasafe zuwa 12,ai kuwa ba karamin murna tayi ba duk da cewar shima yana koyar da ita agida haka ko wani aiki aka basu a makarantar idan ta dawo gida shine yake koyar da ita, basu dade da dawowa ba tayi fari fau da ita ga kiba da tafara hadawa kasancewar yanzu bata da damuwa sai ta mamanta wacce har yau taki sakar mata fuska domin ko tsarabar data kai mata ma lokacin data dawo daga umarah kin karba tayi wannan abu yana damunta mutuka sai dai kullum jabir yana yi mata nasiha kuma yana nuna mata muhimmamcin yin hakuri adukkan lamura.

Yau ta kama ranar juma'a, tunda taga jabir yana kokarin fita ta marairece masa,

"Abbu pop corn nake son ci"

"Dame kuma?" Ya tambayeta yana kallonta,

"Abbu da umbrella (fruit)"

"Kalli bakinki na kwadayi, hmm binti kiga yanda kike kiba amma ni sai rama kike sakani, ni kike tsotsewa ke kina kiba ko?"

"Abbu bakace to ba"

"Binti nace to, shikenan?"

"uhm" tafada tana turo baki,

"Rigimammiya kawai" yafada tareda lakuce mata hanci yana murmushi,

Rakashi tayi ya shiga mota ya tafi office ta dawo falonta ta kwanta tana jiran akawo mata sakon da tayi domin wadannan abubuwan guda biyu yanzu su take kaunar samu.

Tunda aka kawo mata guggurun shi ta wuni tanaci sam ta kasa cin abinci, har jabir ya dawo ya tarar da ita da guggurunta ahannu tana kwance tana kallo tana diba tana ci, washe gari kuwa tunda ta idar da sallar asuba tafada kitchen, hijab dinta kawai ta cire ta shiga kitchen tafara aikin kosan da ta tashi da sha'awar ci,

Kasancewar dan kadan zata yi yasanyata markada waken a blender, kayan hadi ta saka masa sosai ta dora mai tafara soyawa ga kuma yajinta a ajiye agefe dan haka tana tsamewa take cinyewa, jabir ne yadawo daga masallaci dan lokacin har 6 tayi da yan mintuna, ta window din dakinsa ya hangota a kitchen dan haka ya fita ya bita cikin kitchen din yana shiga ya ganta tana cin kosan sai dandanar yaji take yi gashi kosan sai uban tiriri ne yake tashi daga cikinsa kasantuwar lokacin ta tsameshi,

Yana daga bakin kofa yana kallonta wanda ita bata ma san ya dawoba,

"Duk yanda akayi al'amin ya samu kani ko kanwa kenan" yafada acikin zuciyarshi yana murmushi,

Cikin kitchen din ya karasa ya tsaya ata bayanta, "binti ya kike cin abu tun yana kan wuta?"

"Abbu yafi dadine da zafin" tafada tana yarfe hannunta saboda zafin kosan gashi kuma so take takaishi bakinta,

"To kawo in tayaki"

Gefe ta matsa ta tsaya yaci gaba da soya mata yana tsame mata tana ci har yakare, ko d'aya jabir baici ba duk ita ta cinye kayanta,

Hannunta Yakama bayan ya kashe risho din,

"To zomuje ki bani ladan aikin da nayi miki"

"Kai abbu ashe dama ba dan Allah kayi min ba"

Murmushi yayi yana gyara mata igiyar da take daure gaban rigar baccinta wacce ta kasance riga da wando pink colour,

"Dan Allah nayi bintu amma kuma akwai niyya"

Bin bayanshi tayi tana bubbuga kafarta "shi abbun nan wayone dashi Allah"

Yana jinta sarai kawai kyaleta yayi har suka shiga dakin baccinshi.

Wunin ranar bata huta ba saboda dambun shinkafa taji tana ra'ayin yi ta inda ta samu sauki tana da zogale agidan ashuke, haka tatashi aikin dambun, jabir tabawa gyaran zogalen ya karba ya zuge mata shi taje ta dora nan da nan gidan ya hade da kamshin dambun wanda nasan yanzu har yawun masu kwadayi irina ya tsinke,

Yana falonsa yana karanta wani littafin fiqhu wanda wani shehun malami ya rubuta ta shigo hannunta dauke da farantin abinci,

"Abbu ga dambun na kawo mana"

Agabanshi ta ajiye ta bude flask din ta zuba musu "har kin gama binti?"

Bata iya bashi amsaba ta gambada yaji ta tsulala mai acikin dambun tafara ci, kallonta ya tsaya yi yana murmushi,

"Bintina wannan cikin naki akwai kwadayi"

"Ciki kuma abbu?"

"Ehh mana binti, yaushe rabonki da bakonki?"

Dambun ta diba takai bakinta ta kalleshi tace "tun a madina"

"To kin gani, kema kin kusa samun babynki,shikenan nima na huta da bayar da pad"

Bata kara magana ba taci gaba da cin dambunta kafin daga bisani shima ya saka hannunshi acikin kwanon.

Yanzu kullum ita kenan a kayan kwalama bata iya yin normal girki na yau da kullum sai dai na kwadayi yau ma da niyyar yin meat fie ta tashi, zama tayi ta dage tana buga fulawarta wacce ta kwaba tafara murzawa da kwalbar lemu, tana gamawa taje tafara suya dama ita indai abin soyawa ne to tana daga tsaye take cinye kayanta,

Tana suya tana ci har taji ta koshi, sauran ta diba ta ajiyewa jabir wanda yana can a office yana aiki amma lokaci zuwa lokaci yana kiranta awaya yaji halin da take ciki,

Koda ya dawo gida kuwa rigima ta saka masa ita tuwo take so kuma tuwon ma na dawa miyar kuka,

Ido ya zuba mata yana kallonta, "binti tuwo?"

"Ehh abbu, wallahi yunwa nakeji"

Daukarta yayi suka tafi gidan malam amma acan dinma babu tuwon dawar sai na masara dakyar aka samo mata ma makwafta suka dawo gida.

Da safe kuwa bata barshi yayi baccin safeba tashinsa taje tafara yi,

Kansa ta hau ta zauna tafara jijjigashi,

"Abbu katashi muje ka fafe min gwangwani yau alala zanci"

Bude idonshi yayi ya riketa, "alale zakuci yau binti?"

Kai ta daga "ehh abbu yau alale zanci"

"Za kuci dai keda babynki"

Tashi yayi suka fita tare zuwa corridor dinta inda ta tara masa gwangwaneyen peak kanana,

"Binti meyasa ba zakiyi na leda ba yafi sauki wannan wahalar da kanki zakiyi"

"Abbu nidai bana son na leda, wallahi na gwangwani nake so" ashagwabe tayi maganar gashi ta rakwarkwabe fuska tana shirin yimasa kuka,

"To ya isa kar kiyi kuka zan fafe miki"

Zama yayi yafara fafe mata yana jin tausayinta har acikin ransa domin yanzu ita abar tausayice saboda lalurar da take dauke da ita na juna biyun dake jikinta, shiyasa kullum yake bata abinda take so kuma ako wanne lokaci cikin bata kulawa yake dai dai da rana daya bai taba jin ya gaji da yarintarta ko kuma shirmenta ba domin yasan har yanzu ita yarinyace saboda shekarunta har yau ba zasu wuce 25 ba kuma a ka'ida mata basa yin hankali na hakika har sai sunkai 35 alokacinne suke tantance baki da fari shiyasa ma acikin alqur'ani Allah ya ambaci matan aljanna wato hurul aini da cewar matasane masu hankali malamai sunce anan ana nufin yan shekara 35 ne, koma dai menene dama dole miji sai yana yin hakuri da matarsa saboda hankalinsu da nutsuwarsu ba daya bace,

Yanata yan tunane tunanenshi yana fafe mata gwangwanin ita kuma tana gyara wakenta domin akai mata markade,

"Abbu yanzu fa nan da shekaru 20 kazama tsoho ko" tafada tana dariya,

"Ai maza basa tsufa binti kece dai kika tsufa lokacin, nikuma lokacin zan auro yarinya Yar 18"

Waken ta bari ta koma kusa dashi "abbu dagaske kake yi?"

Kallonta yayi yanda duk ta rirrikeshi ta cukwikuyeshi tana kallonsa tareda hayewa jikinshi,

"Dagaske mana" yabata amsa yana tara mata gwangwanayen wuri guda, babu zato yaji tasaka masa kuka,

"Kai binti ai lokacin kema fa kin girma kilama kinyi auren babbar yarki"

Kukan ta daina ta rufe fuskarta, "kuma dan nayi auren yata shine zaka auro min sa'arta?"

"Ehh mana ai hakan yafi lada" yafada yana janye hannuwanta,

"Tam shikenan Allah ya kaimu lokacin idan ka aurota yayana zan saka suyi mata duka" tana gama fadin haka tatashi daga kusa dashi ta dauki bokitin wakenta takoma cikin kitchen, dariya sosai jabir yayi saboda jin abinda ta fada,

Lafiyayyen alalenta tayi yasha manja da alayyahu _(nasan pherty Xarah uwar kwadayi har yawunki ya tsinke, to kwalelenki, ga Batool Mamman canma na hangota tana lasar lebe to kema kwalelenki)_, yaji ta dauka roba guda ta koma falonta inda jabir yake yana hira da al'amin a waya,

"Ga antyn naka sarkin kwadayi"

Bata wayar yayi ya dauke robar yajin data dauko,

Duk hankalinta ya kasu kashi kashi dan haka agurguje ta yiwa al'amin sallama ta riko hannun jabir "abbu bani yajin, wallahi idan babu yaji bana jin dadin abincin"

"Kullum ke kenan acin yaji, yajifa bashida wani amfani ajikin dan adam"
Chapter 54 · 0% Book details