← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 64

Sashe 6

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannu sir" tafada cikin farin ciki

"Yawwa" yafada yana balle clips din hannun rigarshi,

"Sir yau naje unguwane shiyasa ban zo da wuri ba"

"Babu damuwa amma ki kiyaye next time"

"Yes sir" bai sake magana ba ya nufi toilet.

***

Bayan ya tashi daga office around _5_ ya nufi gidan mahaifinshi, a babban falon shi ya tarar dashi zaune ya bude katon alqur'aninshi yana karantawa, jin sallamar malam jabir yasashi rufe alqur'anin ya juyo ya dubeshi da fara'a a fuskarshi,

Zama yayi kusa dashi ya russuna ya gaisheshi,bayan ya amsa ne yace

"Jabir dalilin kiran da nayi maka ayau shine kaga dai nafarko kana daya daga cikin mutanen da ake girmama su acikin garin nan ake koyi dasu, kuma kallum aikin samun lada kake yi, wannan dalilin ne yasa yau na sake kawo maka kokon barar wani aikin samun ladan, nasan Allah ya hore maka arziki, da kuma zuciyar da zaka iya rike mata biyu, wannan dalilin ne yasa na umarceka da kayi hakuri ka daure ka auri wata yarinya ma'abociyar littafi wanda nake kyautata zaton cewa idan Allah ya yarda _*wani haske*_ ce agareka kamar yadda kaima zaka kasance _*wani haske*_ agareta, ba musulma bace amma ta kamu da tsananin sonka saboda nagartarka da kyawawan dabi'unka gamida kyawawan halayenka da ta duba,ni kuma nasha mata alwashin insha Allahu zaka aure ta zaka zame mata _*wani haske*_acikin rayuwarta"

Tun farko tun asali ko acikin mafarki bai taba tsammanin zai iya aurar wacce ba musulma ba saboda basa burgeshi amma yanzu bazai iya yiwa mahaifinshi gardama ko musu ba dan haka ya aminta "shikenan malam insha Allahu zan aureta kuma zan zauna da ita"

"Allah yayi maka albarka jabir, amma kayi min alqawari zaka riketa bisa amana"

"Malam insha Allahu zaka sameni mai rikon amana akanta tareda yin adalci"

Albarka mahaifin nasa ya shiga saka masa tareda yi masa fatan alkairi acikin rayuwarsa, sallama yayi masa ya tashi ya tafi yana jimamin wannan al'amari acikin ranshi, wai a matsayinsa na mai wa'azi shine zai auri wacce ba musulma ba.

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[10/28, 9:26 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/23, 10:08 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_26-30_

~~~Tun yana hanya ya fara laluben number uwar gidansa wato ummu al'amin kamar yadda yake kiranta, ringing biyu ta daga cikin sallama,

"Abu al'amin yau baka dawo da wuri ba, duk aikin office dinne ya rike ka haka?"

"Gani nan nataho yanzu, na dan biya ta gidane naga malam"

"To Allah ya kawoka lafiya, ga al'amin"

Karbar wayar al'amin yayi cikin murna yace "hello abbu na kaga ummu ta dakeni"

"Ohhhhh al'amin rikici, laifi kayi mata ko?"

"Abbu ni banyi mata laifi ba"

"Haka kawai ta doke ka? To idan na dawo zan rama maka"

"Yawwa abbuna sakallahu kairan wa ilal liqa"

Kashe wayar yayi yana murmushi a rayuwarshi yana son yaron nan nashi shiyasa yake son yaga ya tsaya tsayin daka don ganin rayuwarshi ta inganta to amma yanzu gashi wani al'amari mai girma ya na kokarin kunno kai cikin rayuwarshi data iyalinshi, sam bashida ra'ayin auren ma'abota littafi wato (ahlul kitab) to amma yanzu hakan ya zame masa tilas ko dan samun ladan yin jahadi amma yana jinjina ta yanda zai iya rayuwa da macen da bata tsarki.

Lokaci kankani suka isa gidansa dake unguwar farin gidaje, gidane na alfarma tamkar gidan wani sarkin nidai ummi A'isha nace ashe malamai suma yan jin dadine, farfajiyar gidan driver yaje yayi packing yafito ya budewa GM kofa shima ya fito ya nufi cikin gidan, part ukune part din farko shine na ummu al'amin, nakusa da nata nashi na karshen kuma empty yake babu kowa aciki, yana shiga falonta ya jiyo surutun al'amin wanda yaketa wasansa yana kallon tashar spaceton Arabiya, da sallama ya shiga, da gudu al'amin ya taso ya rungumeshi, hannunshi ya rike yabi ta kofar falon yafita wani dan korido ya shiga sashensa yana shiga daki al'amin yafito ya tafi falo yana kokarin kunna tv, wanka ya shiga yayi ya fito ya shirya cikin jallabiya fara da yar hularta itama fara ya fito falonshi nan ya tarar da al'amin yana kallon tv, zama yayi kusa dashi daidai lokacin wata kyakkyawar mace yar madaidaiciya ta shigo tana sanye da doguwar riga da dan karamin hijabi shekatunta ba zasu fi 28 ba fara doguwa,

Hannunta dauke da food flasks guda biyu, "barka da isowa Malam" tafada tana dan murmushi,

"Yawwa yagida" yafada yana duban al'amin wanda yaketa faman dariya saboda cartoon din da yake kallo na larabci,

"Tashi kaje kayi alwala mu tafi salla ko walad"
"Abbu ni yanzu ba walad bane na girma"

"Yaushe ka girman?"

"Abbu nagirma nazama rajulin" yana gama fadin haka ya tashi da gudu ya fita,

Murmushi ya rakashi dashi yayinda ita kuma matar ta matso kusa dashi "yau baka dawo da wuri ba ashe wurin malam kaje"

Kai ya daga mata "malam ne ya kirani sai nadawo zanyi miki bayanin abunda muka tattauna dashi"

"To adawo lafiya abu al'amin"

Tare suka fito ya shiga falonta yana kiran al'amin domin yazo su tafi masallaci.

Bayan idar da salla zama yayi yafara dorawa mutane karatu kan littafin da suke karantawa ako wacce rana mai suna adabul mufrad, har lokacin sallar isha yayi bayan sun idar da salla ne ya dauko al'amin a kafadar shi ya shiga cikin gida mai gadi ya mayar da kofa ya rufe.

Dakin ummu ya nufa acan ya sameta zaune kan abin salla tana karatun alqur'ani mai girma, gefen gadonta yaje ya kwantar da al'amin ya juya ya fita ya shiga sashensa, abincin ya zauna ya fara ci har ummu ta shigo cikin kyakkyawar shiga ta sanya hijabi babba mai hannu,

"Yau baka samu kaci abinci da wuri ba" tafada tana murmushi,

"Eh wlh dan ban dawo da wuri bane" ya fada cikin muryarshi mai dankaren sanyi,

"Naji kace zaka yi min bayani Allah dai yasa lafiya"

Abincin gabanshi ya ture ya juya ya fuskanceta,

"Lafiya lau, maganar aure ne wanda zanyi"

Kallonsa tayi da sauri amma tasan tunda ya fada dagaske yake saboda baya yi mata irin wannan maganar,

"Aure Abu al'amin? Yaushe? Meya faru?"

Girgiza mata kai yayi 'ban san dai nan da yaushe bane sai abinda malam yace"

Wani bacin rai taji ya fara mamayar zuciyarta, take fuskarta ta sauya ranta ya baci ta mike tsaye,

"Asshhha! Da ace mutane sun san halayenka to da basu zauna sun bata lokacinsu sun saurari wa'azinka ba, kullum kana yiwa mutane wa'azi amma kai kuma Baka yiwa kanka, me nayi maka da kake son sai kayi min kishiya?"

Tsaye shima ya mike "haba Salma akan kawai nace miki zanyi aure shine zaki jefeni da wadannan kalmomin, ubangiji ne fa ya bani damar auren mace fiyeda guda daya acikin suratul nisa'i aya ta uku, yace mun halarta muku ku auri abinda yayi muku dadi daga mataye.......!"

Katseshi tayi da sauri, "ya isa, sarkin wa'azi ni ba aya nace ka jawo min ba, Allah yabaka ikon yin adalci kawai"

Tana kaiwa nan ta juya ta fita tanufi dakinta tana sharar kwalla,shi kam tatafi ta barshi da mamaki karara akan fuskarshi lallai mata akan kishiya basu da dama, ko sun san abu sai su take yanzu duk ilimi irin na Salma akan kishiya tana neman birkicewa.

***

A bangaren goodness kuwa tun ranar da sukaje wurin mahaifin GM ita da nura bata sake komawa office ba saboda yanzu bata son taje ko GM yasan itace itace wacce take son ya aureta,

Dawowarsu kenan daga church itada ma ta tarar da labari mai dadi cewar GM sun zo shida mahaifinsa wurin babanta zuruf ma ta mike

"Papa goodness ban gane abinda kakeso kayi ba, kana son goodness ta auri musulmi hausa man saboda addininku daya?"

"Ma ba laifin baba bane, nice nake sonshi wlh ma yanada kirki"

"Shut up, poor girl, idan ya sakeki ko yayi miki kishiya kar ki kuskura kizo min nan gidan" ma tafada tana zazzaro ido,

Shidai mahaifinta bai ce komai ba domin yana cikeda tsantsar farin ciki domin yasan insha Allahu goodness ta kusa samun rahamar ubangiji,

"Ko kin auri hausa man to ba zaki yi addininsu ba,and papa goodness kasan dai wannan bikin a church za muyishi ko?"

Ba goodness ba hatta mahaifinta sai da maganar ta girgizashi.

Cikin kidima goodness take kallon mamanta kafin mahaifinta ya bada amsa "kiyi bikinki a church nikuma nayi nawa a nan shikenan?"

"Yawwa haka yayi dai dai saboda zan kaita church pastor yayi mata addu'a" tana dasa aya ta tashi ta karasa dakinta, nan baban goodness ya shiga yi mata nasiha da yanda zata zauna da mijinta lafiya sannan ya gargadeta da kiyaye daukar hudubar mamanta domin bikinta nan da sati shida za ayi tunda GM babban mutum ne ba shirme za a tsaya yi ba, wani sanyi ne ya mamaye ruhinta amma bata nuna ba a lokacin har sai da ta tashi ta shiga dakinta ta fada kan katifarta tana murna ta kira nura tana fada masa anan yake sanar da ita ai shine ya jagoranci su GM din har zuwa gidansu kuma yanzu GM yasan itace wacce zai aura saboda har yayi masa maganar cewa ya sake nemo masa wanda zai ci gaba da aikinta a office, tashi zaune tayi tace

"Heyyy nura don't bring female i beg you, ka samo masa namiji"

Dariya nura yayi tareda kashe wayar, wani irin son GM taji yana azazzalarta tana son taji sanyayyiyar muryar nan tashi nan ta tuna da cewar tana da tsohon layi a ajiye na zain, da sauri ta bincikoshi tasa a wayarta ta fara kiran layinshi, sai daf da zata tsinke sannan ya dauka yayi sallama, shiru tayi tana sauraren muryarsa, wata sallamar ya sake yi nanma tayi shiru har sai da yayi sallama sau uku babu amsa hakan yasashi katse wayar, wata ajiyar zuciya ta saki tana mai muradin ganin ranar aurenta da GM.
Chapter 6 · 0% Book details