← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 64

Sashe 38

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abbu ba kai bane kace wurin budurwarka zakaje ba" ta fada tana kallon fuskarshi,

"Wurin baba nazo saboda rabona dashi tun cikin azumi lokacin da nazo yi masa sannu da shan ruwa ana saura biyu natafi umarah"

Kanta ta daga gabanta yana faduwa domin tunowa da tayi har yau fa mamanta bata san ta musulunta ba, tabbas tasan akwai drama agaba.

Suna komawa gida ta shiga sashenta tayi wanka ta tsuke cikin kayan baccinta farare tas riga yar karama da wando iya gwiwa,

Turaren shifax ta shafa tatafi dakin jabir wanda ke gaban mirror yana gyara sajensa, ta cikin mirror din ya ganota tana shigowa kanta babu dankwali tana ta barbaza gashin kanta,

"Abbu gashin nan nawa gobe sai naje ansake wanke min akusa da gidan anty Bilkisu"

Juyowa yayi yana kallonta ba karamin kyau tayi ba cikin kayan baccin dake jikinta,

"Meyasa zaki saka fararen kaya bayan kina d'iga?"

"Abbu gobe zanje awanke min kaina wlh bai fitaba"

Ta kawar da maganar da yayi mata ta farko,domin kunya yake bata,

"Allah ya kaimu"

Kan gadon ta hau ta kwanta yayinda shima ya kwanta agefen gadon,"abbu duk wannan wurin Zaka barmin? Gaskiya yayi min yawa,yayi min girma"

Matsawa tayi ta kunnaceshi ta kwanta agefenshi,hannunshi ta dora akan gaban gashin goshinta,

"Abbu kajifa inda duk nabi na kone"

Wurin yafara shafawa da hannunshi, daga karshe ya dago kan nata ya dora akan kirjinshi yaci gaba da yimata lalube acikin gashin kanta,

"Abbu Idan nayi bacci kayi min addu'a pls"

"Kema ya kamata ki koya saboda ki rinka yi da kanki"

Idonta alumshe ta lalubo hannunshi daya ta rike cikin nata, "abbu har yanzu surori hudu kawai na iya daga fatiha, sai kul a'uzu bi rabbil falaq, nass,sai kulhuwallahu ahad"

"Ina sane da hakan binti amma zan fara yi miki dori daga yanzun nan sannan indai baki maida hankali kin iya ba zaneki zanyi"

Murmushi tayi ta sake gyara kanta akan kirjinshi, "abbu duka?"

"Ehh duka" yabata amsa yana cigaba da shafar kanta

"Abbu kofa al'amin ban taba gani ka daka ba amma shine ni zaka dakeni"

"Ai al'amin baya wasa da karatu shiyasa bana dukanshi amma ke indai kika yi wasa zaneki zan rinka yi"

Kanta ta daga tana kallon fuskarshi acikin hasken dakin,

"Abbu dama ance Ku mazan hausawa dukan matanku kuke yi, gaku kunyi suna wurin yiwa mata kishiya sannan kuma babu wuya kunyi saki"

Maganarta dariya ta bawa jabir domin tunda take dashi bata taba ganinshi yana dariya harda kyakyatawa ba sai yau,

Sai da yayi dariyarsa da yawa sannan ya matsa hannunta dake cikin nashi,

"Binti da wasa nake yi miki fa, taya zan dakeki? Sannan waye yace miki mazan hausawa suna dukan matansu? Jahili ne zai daki matarsa amma ba mai koyi da annabi ba, mutukar mutum da annabi yake koyi ai bazai rinka dukan iyalinshi ba domin zaluncin yayi yawa, sannan mata amana ne awurin mazajensu"

Fuskarta ya shafo yana murmushi,

"Binti duk laifin da kika yimin komai girmansa bazan taba dukanki ba, ai babu tsari ace miji yana dukan matarsa domin ba baiwa bace, ko dabbace aka ajiye maka ai bai kamata kana dukanta ba bare yar adam wacce ta zamanto wani bangare na rayuwarka, amma wasu mazan saboda tsananin zalunci koda yaushe acikin dukan matansu suke wani abin haushinma wani har agaban yaransu yake dukan matar wani kuma agaban makota, agaskiya wannan baya daga cikin koyarwar annabi,domin annabi kullum cikin nishadi da kyautatawa iyalan gidanshi yake"

"Abbu to kuma sakin fa? Mazanku suna da yawan saki"

"Binti saki halal ne amma Allah baya sonshi domin duk lokacin da akayi shi sai al'arshi ya girgiza, kuma wani sakinma rashin hakuri ne yake kawoshi, ki kwantar da hankalinki indai nine insha Allahu bazan taba sakinki ba zan zauna dake har karshen rayuwata"

Wani farin cikine ya lullubeta wanda har sai da tayi mishi kiss akan kirjinsa ba tare da ta saniba,

"Abbu to kuma kishiyar fa?"

Ta tambayeshi tana murza yan yatsunshi,

"Aure ai Allah ne ya bamu dama yace mu auri mata har guda hudu"

"To yan gata"

Haka kawai ta fada ta tashi daga cikin jikinshi ta koma can karshen gadon ta kwanta,

"Binti" ya kira sunanta yana murmushi shidai ya kasa gane wanne irin kishine da ita, shiru bata amsa ba hakan yasa shi kashe hasken dakin,

Minti biyar atsakani taji wani abu ya garya mata cizo akan fatar idonta daya, zumbur ta tashi tana sosa wurin,

"Abbu..!"

Shiru shima yayi mata wato shima ya rama yanda tayi masa dazu,

"Abbu..!" Tasake kiransa tana sosa wurin, wani cizon taji kwaron ya sake yi mata awuyanta,

"Abbu, wayyo idona, abbu kunama ta cijeni" tafada gamida fashewa da kuka, cikin Sauri jabir ya tashi ya kunna fitilar dakin ya matsa wurinta,

"Kunama?" Tashi mugani, tana tashi sai ga cinnaka ya fado wani kato dashi bakikkirin,

Kasheshi yayi yana dan murmushi "wannan yarinya da rangwanta kike wai cinnakane kunama"

Yafadi acikin mind dinshi,

Komawa yayi zai kwanta, rarrafawa tayi tabishi tana kuka, "abbu idona, kaga har akan idona ya cijeni"

Hannu ya mika ya kwantota jikinshi,

"Sorry binti" yafada yana dan bubbuga bayanta,

"Abbu ka sosa min pls"

Dan yatsanshi ya dora asaman idonta yafara sosa mata wurin,

"Abbu har yanzu da zafi, ka sosa min"

Sosa wuyanta take tayi shikuma yana mulmula mata saman idonta da yatsanshi,

Ta dade tana yi masa rikici har bacci ya dauketa sai alokacin hannun jabir ya huta, murmushi kawai yake yi na darun binti,

Addu'a yayi musu ya kashe wutar dakin yaja bargo ya rufesu.

Washe gari tun wurin 10 tagama shirinta tsaf driver ya kaita gidan yayarta bilkisu saboda tana son wanke gashinta,agida ta tafi tabar jabir domin har yanzu bai koma office ba,

Ba karamin murna anty Bilkisu tayi data ganta ba,

Nan ta shiga hidima da ita duk da cewar mijinta ba mai kudi bane amma akwai rufin asiri da wadatar zuci,

Nan suka shiga tattaunawa musamman ma maganar mahaifiyarsu wacce har wannan lokacin bata san goodness tabar addinin kiristanci ba,

Sun dade suna tattaunawa sannan suka gangaro kan zamantakewar auren jabir da goodness, kamar kullum yauma lecture anty bilkisu ta zage tayi mata mai taken "ki zama karuwar mijinki tun kafin wata ta zama karuwarsa awaje?"

Lecture din ta shigi goodness sosai amma bata yarda anty Bilkisu ta gane cewar har yanzu babu abinda ya shiga tsakaninta da jabir ba domin tasan wannan wani babban sirrine atsakaninsu wanda ko uwar data haifeta bazata taba iya sanar da itaba shiyasa take ganin kokarin matan auren da suke zama agidan biki ko gidan suna,suna bayar da labarin abinda ya gudana tsakaninsu da mazajensu, wata ko menene mijinta yayi mata to sai ta fadawa kawarta musamman ma amare dan wasu amaren adaren da aka kaisu gidan miji da safe sai sun kira kawayensu awaya sun zayyane musu tsaf abinda ya faru komai sai sun fadawa kawaye tamkar agabansu aka aikata, yakamata arinka kiyaye wannan sirrin,

Sai da anty bilkisu ta gama dorata akan network sannan ta tashi ta shiga gidan gyaran gashin, wanke mata aka sake yi ta shiga drayer aka gyara mata gashinta tsaf, tuni gashin yayi baki wuluk yayi kyau ya dau kyalli,

Gidan anty Bilkisu ta koma sai da ta jima agidan sannan ta kira wayar jabir lokacin yana kwance afalonshi yana waya da ummu,

Waiting call tagani har wayar ta tsinke, bari tayi aka yi kamar minti biyu nanma data sake kira har lokacin waiting call, wayar ta zubawa ido aranta tana tunanin to dawa abbu yake waya kodai da budurwar tasa yake hira?

Wani kishine ya mamaye zuciyarta, yafi minti 20 suna waya da Ummu da al'amin sai da yagama sannan yaga missed called din yar darun tasa,

"Binti rikici, yau zansha daru kenan" yafadi hakan azuciyarshi lokacin da yake kara wayar akunnenshi domin kiranta,

Ai kuwa tana dauka ta buntsure baki kamar yana kallonta,

"Abbu sai yanzu ka gama wayar?"

"Binti da matata nayi waya" yafada da niyyar zolayarta,

"Nasani ai, nagama tun dazu driver kawai nake jira"

"Zai zo ya daukoki yanzun nan binti, tana gaisheki"

"Bana amsawa" abinda ta fada kenan ta tsinke wayar.

Lokacin data koma gida afalo ta iske jabir yana yan karance karancenshi kamar yadda ya saba,

Daf dashi taje ta zauna tareda zame hijabin kanta,

"Abbu ka gani"

Gashin nata yabi da kallo, ba karamin kyau yayi masa ba gashi sai wani irin kamshi yake mai dadi,

"Nagani binti, yayi kyau"

Kan cinyarsa ta dora kanta, "abbu dora min karatun"

Tana kwance acinyarsa ya fara dora mata suratul nasri, aya biyu yayita maimaita mata har lokacin fitarshi yayi, part dinta takoma ta mike akan gadonta.

Misalin karfe _9:30_ nadare ta shiga kitchen ta dafawa jabir shayin na'a na'a, shiryawa tayi cikin kayan bacci orange colour marassa duhu, riga da wando masu laushi,

_Bedroom_ dinshi ta shiga ta sameshi yanata faman aiki a laptop dinshi, kan gadon ta hau ta kwanta akusa dashi bayan ta ajiye masa tea flask din agefenshi shi,

"Binti kafin kiyi bacci ki karanto min abinda na koya miki dazu"

"To abbu" cinyarshi ta dafa da hannunta ta soma karanta masa har ta gama,

Kur tayi masa da ido tana kallonsa shikuma yanata aikinsa na amsawa mutane tambayoyinsu akan abinda ya shafi addini,

Cikin sanyayyiyar muryarshi wacce tafi ta *Pherty Xarah* sanyi yace da ita,

"Binti taso kiga wani abu"

Tashi tayi takai dubanta ga laptop din tashi, anan ta hango sako daga wata mata tana tambayarsa kamar haka: _Assalam malam shekarata 5 da aure yanzu haka inada yara guda biyu, malam tambayata itace shin dagaske ne duk lokacin da miji ya ziyarci shimfidar matarsa sai tayi wanka? Dagaske ne idan shi yayi wankan ita basai tayi ba? Malam idan dagaske ne ana yin wankan to ya ake yinshi? Menene siffar wankan? Sako daga wata baiwar Allah_

Kallon fuskarshi goodness tayi duk da cewa ita bata dade acikin musulunci ba to amma ta dan fuskanci wani abu kadan akan sakon nan,

Rufe laptop din yayi ranshi abace ya ajiyeta akan drewar ya kwanta, kan kirjinshi taje ta kwantar da kanta tana kallon fuskarsa,

"Abbu menene? Meye ya bata maka rai?"

Cikin raunananniyar muryarsa wacce ta haduda bacin rai yafara magana cikin sanyinshi,
Chapter 38 · 0% Book details