← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 64

Sashe 5

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zuwa gida wanka tayi ta shirya cikin riga da wando matsattsu ko tea bata sha ba ta nufi office, karfe _9:00_ ta isa lokacin har GM ya dade a office dan haka jakarta kawai ta ajiye ta nufi cikin office dinshi domin ta kagu taga kyakkyawar fuskarshi gashi zuciyarta sai harbawa take yi fat fat,

Kwankwasawa ta danyi kafin ta bude kofar ta shiga, can ta hangoshi zaune kan kujerarsa hannunsa rikeda wani littafi wanda ba zata iya tantancewa ba yana dubawa sannan ya kunna karatun alqur'ani kasa kasa yana saurare, yana sanye cikin farar shadda mai kyau sai kyalli take, kusan duk kayansa farare ne a yanda ta fuskanta domin bata taba ganinshi da wasu kalar ba daga fari sai milk colour,

"Good morning sir" tafada tare da dan durkusawa,

"Morning" yafada a hankali, sanin bazai kara magana ba ya sata juyawa zata fita,

"Am kinga" yafada ahankali, hakan yasa ta dawo tace "na'am sir"

"Kidaina irin wannan shigar idan zaki fito office, ki rinka sako normal kaya saboda nan kinga cikin mazane kuma mu a addininmu hakan bai dace ba, kamar yadda kuma a addininku hakan laifi ne, dan Allah akiyaye"

Kur tayiwa dan karamin bakinsa da idonta lokacin da yake mata magana, dagowa yayi ya kalleta yaga itama shi ta kurawa ido,

"Kinji abinda na fada"

Sai alokacin ta dawo hayyacinta "yes sir, nagode sir"

"Ok kina iya tafiya" yafada tareda mayar da idonsa kan littafin da yake karantawa,

Office dinta ta koma ta zauna tana murmushi amma kuma zuciyarta har yanzu bata daina bugawa ba, tunani tafara yi itafa duk kayanta totally babu atamfa domin bata dinkasu kuma ko ta dinka ba dinkine na cin mutunci domin sai anyiwa atamfar kaca kaca kafin a dinkata, sai anyi mata gutsi gutsi, dan haka kayanta daga riga da skirt sai riga da wando amma duk da haka zata daure ta zabo masu dan dama dan ganin tabi maganar da ya fada mata kuma hakan da yayi ba karamin sake burgeta yayi ba.

Da yamma ta tashi daga aiki ta koma gida, a kofar gida ta hadu da nura cikin murna ta jashi cikin gidan domin dama tana son ganinshi,

"Yanzu kin zama worker kinyi wuyar gani ko?" Nura ya fada ya dariya,

"Sorry nura dama inata son nayi maka waya, nura dan Allah ka taimakeni ka sanar dani wani abu dangane da GM dinmu domin zuciyata ta kasa kyaleni in huta"

Kallonta nura yayi "ban fahimceki ba, wai malam jabir kike nufi? Me ya faru?"

"Nura nothing, i beg ka fada min pls nura, am in bad condition, ina bukatar jin wani abu game dashi domin ina son na aure shi"

Zaro ido nura yayi "aure? Aure fa kikace goodness, taya kike tunanin wannan auren naku zai yiyu kina Christian kina ikirararin Allah ukune, kina mai yarda da cewa Annabi Isah Allah ne, kina cewa Maryam Allah ce, kina cewa Isah dan Allah ne, shikuma mal jabir yaki yake da wannan kalmar, kiran mutane yake akan su daina furta wadannan kalmomin, kira yake abi Allah shi kadai,tayaya wannan hadin naku zai yiyu? Da ace shi ba malami bane mai wa'azi tabbas may be zai iya aurenki, to amma shi mai wa'azi ne malamine wanda yayi suna ba a iya kasar nan ba har da sauran wasu kasashe na musulmai ai kinga abun kunyane agareshi aji yana auren wacce ba musulma ba"

Ajiyar zuciya goodness ta sauke mai nauyi "gaskiya ka fada nura amma kuma ni rashin aurenshi agareni wlhi tamkar rasa rayuwata ne dan Allah nura ka taimakeni" ta fadi hakan lokacin da kwalla tafara bin kumatunta,

"Shikenan goodness babu komai zan taimaka miki domin nasan haduwarki da malam jabir _*Wani Haske*_ ne acikin rayuwarki, zan taimaka miki har kikai ga samun wannan hasken, yanzu kin san ya za ayi? Zanje gidansa anjima da daddare zan halarci majalissinsa inda yake karantarwa bayan sallar magrib anan zan nemi fatawa cewar wata wacce ba musulma ba ta ganni tana sona shin zan iya aurenta? Kinga anan zan gane ko zai yarda ya aureki ba tare da kin musulunta ba"

"Good nura nagode sosai, ina jiranka idan ka dawo"

Tashi nura yayi ya fita a lokacin ma ta shigo tana rikeda bible dinta "hey goodness, meya hanaki zuwa church? Am asking you meyasa ba kije church ba? Kin fara wasa da addinmu ko goodness? Idan kinci gaba da haka pastor will punishe you nikuma ba ruwana ehem"

"Sorry ma dawowana kenan daga office, gashi nagaji shine nabari sai da daddare zanje church din night service"

Fara,a ma tayi cikeda murna tace "i like you my daughter, God bless you, ina babanki fa?"

"Ma babu kowa agidan lokacin da na dawo ina jin ya fita"

Kada kai ma tayi ta wuce cikin daki tabar goodness zaune anan zuciyarta tanata harbawa domin rashin sanin abinda nura zaizo mata dashi.

Kamar yadda nura yace haka yayi bayan an tashi daga karatu ya dubi malam jabir yace "malam ina da tambaya, wata yarinya ce ta yaba da nagarta ta kuma ta yaba da rikon addinina da halayyata tace tana son na aureta to amma fa ita ba musulma bace, mahaifiyarta ma ba musulma bace mahaifinta kuma musulmi ne, to malam ya halarta na aure ta?"

Kallonsa malam jabir yayi yana murmushi "ya halarta ka aureta,addini ya baka dama amma sai ta kasance wacce ba mazinaciya ba, sai ta kasance ya ba baiwa ba wannan shine sharadin, addinin Allah mai saukine, babu haramci a auren ma'abota littafi kwata kwata sai dai idan mutum bashida ra'ayi ne domin ba kowanne mutum ne zai auri wacce ba musulma ba, kaga kamar ni idan ka bani wacce ba musulma ba bazan aureta ba saboda wasu dalilai amma nasan aurenta ba haram bane".

Daga kai nura yayi dama tun farko abinda ya zarga kenan, "to malam amma misali idan kaga yarinyar zata fada cikin wani hali marar kyau ai zaka aureta ko?"

Murmushi malam yayi har sai da hakoransa suka fito "kune yara ku ya kamata kuyi irin wadannan taimakon"

Yana kaiwa nan ya tashi ya shiga gida, tahowa nura yayi jikinsa a sanyaye, a farkon layinsu ya hango goodness tsaye tana jiran dawowarshi.

Tana hangoshi zuciyarta taci gaba da dukan uku uku har ya karaso suka samu wuri suka zauna,

"Goodness gandoki kin kasa zama agida kin biyoni nan"

Murmushin karfin hali tayi "ya akayi"

"Komai mai yiyuwane da yardar Allah amma shi dai a ra'ayinshi bashida sha'awar auren wacce ba musulma ba sai dai wannan ba shine yake nuna cewar bazai aureki ba, kinga na farko shi mutumne wanda ya karanci addini tsantsa saboda asalima baifi shekara 5 da dawowa _Nigeria_ ba daga _madina_ acan yayi karatunsa na addini wanda ya shafe fiyeda shekaru _20_ acan, bayan dawowarshi ne yayi aure yanzu yana da yaro guda daya, amma goodness mezai hana ki yarda ki karbi musulunci idan kikayi sa'a ta sanadiyyar karbar musuluncin ya aureki"

Da sauri ta girgiza kanta hawaye na bin kumatunta "no, nura ba zan iya musulunta ba nidai ya aureni a haka nayi addini na yayi nashi, idan nace zan musulunta ma bazata yarda ba"

"To shikenan yanzu kin san ya za ayi? Mahaifinsa za muje mu samu kiyi masa bayani, shi mal jabir mutum ne mai tsananin biyayya wa mahaifinsa, baya ketare umarninsa, nasan indai mahaifinsa ya yarda shima zai yarda"

Dan murmushi tayi "Allah yasa ya yarda, nura nagode, yaushe zamuje?"

"Gobe za muje da safe sai ayi masa bayani"

Cikeda murna sukayi sallama ta tafi church, acan ta kwana sai da asuba ta dawo, yanzu promise ya gama gane cewar ta daina sonshi dan haka shima ya fita a harkarta.

Karfe 10 nasafe suka hadu da nura suka tafi unguwar masanawa inda acan mahaifin mal jabir yake, gidane babba kato da masallaci a kofar gidan, acikin masallacin suka sameshi yana lazimi, tsoho ne dan kimanin shekaru 70 aduniya fuskarshi duk farin gashi amma jikinsa ras yake,

Ita goodness bata shiga ciki ba awaje ta tsaya tasa doguwar riga yar kanti ta daura bakin dan kwali, nurane ya shiga ciki suka gaisa da tsohon yayi masa bayanin komai wanda yasani babu abinda ya boye tun daga farko har karshe sannan ya kara da cewa "mahaifinta da mahaifiyarta dukkaninsu yan okene ne amma suna zaune anan jalingo, sannan mahaifinta ya dade da musulunta tun shekaru masu yawa da suka wuce ta sanadiyyar wani makocinsa da suka zauna tare agarin jos, amma ita mahaifiyar har yanzu tana nan akan addinin yahudu da nasara"

Dan murmushi tsohon yayi yace "yaro wannan mutumin da kace ya musulunta nine nabashi kalmar musulunci lokacin ina zaune agarin jos ina koyarwa a jami'ar addinin musulunci dake garin, shekarune masu yawa bana mantawa aka kawo min shi akace zai musulunta, nine nan nabashi kalmar shahada, babu komai insha Allahu jabir zai aureta kamar yadda take son ya auretan, amma ka sanar da ita idan tasan zata aureshi ne da niyyar ta cutar dashi to gara ta fasa idan kuma tsakani da Allah take sonsa to falillahil hamdu insha Allahu sai jabir ya zama _*WANI HASKE*_ acikin rayuwarta"

"Mun gode malam, Allah ya kara girma da nisan kwana" nura ya fada tareda tashi ya fito inda goodness ke tsaye tana sauraronsu, duk wadannan maganganun da akayi acikin kunnenta akayi su shiyasa farin ciki ya mamaye zuciyarta marar misaltuwa, machine din nura suka hau suka bar wurin ya tafi kaita office duk da cewa yau tasan ta makara sosai amma haka zata daure taje dan ta ganshi,

Murna fal acikin zuciyarta nura yana ta kara yi mata karin bayani har suka je office din ta sauka tana yiwa nura godiya ta shiga ciki, Massinger dinsu ta samu zaune shi kadai ganinta ya fara yi mata sannu da zuwa, anan yake sanar da ita oga yana conference room yana meeting da directors dinshi, wannan rana ta yau goodness na cikeda farin ciki.

Sai da lokacin salla yayi sannan masu meeting din suka firfito domin zuwa salla, office dinsa ya nufa domin yin alwala, yana shigowa sukayi ido hudu da goodness, dauke idonsa daga kanta yayi yashiga office dinsa bayan massinger ya bude masa kofa, binsa ciki tayi lokacin ya cire hular kansa yana saka silifas zai shiga toilet,
Chapter 5 · 0% Book details