← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 64

Sashe 2

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunta goodness ta kama tana murmushi "ma indai akan wannan ne karki damu, bazan musulunta ba, i promised you this, kuma ai ma ko a secondary sch da musulmai na zauna harna gama sch nawa, amma babu ruwana da addininsu suma babu ruwansu da nawa, akoda yaushe suna fada min cewa addininsu ya basu dama suyi mu'amala da Christian babu haramci aciki, and when i was in the polytechnic duk course mate nawa Muslim ne suma basu da problem, kuma ma ga baba shima musulmi ne"

Tsaki ma ta danyi tace "am not asking u about this rubbish, kawai ina fada miki ban yarda kiyi tarayya ko wani mu'amula da musulmi ba, sannan kiyi min alqawari cewar ba zaki musulunta ba, duk lokacin da kika zama musulma to bani ba ke, kuma sai na yanka ki, you heard?"

"Am agreed ma,and i promised you i will not become a muslim, i wish my self to die under this religion (Christianity)"

Shafa kanta mom tayi tace "thank you my daughter, am very proud of u" sannan ta juya ga mahaifin goodness wanda ke zaune yana sauraronsu bai ce komai ba tace,

"Papa goodness kaji your daughter done get a job, so ka saka mata albarka, pls bless your daughter"

"Allah sanya alkairi kinji goodness, Allah yasa wannan aikin ya zamo _*WANI HASKE*_ acikin rayuwarki, Allah ya baki nasara...."

Da sauri ma ta katseshi "ah papa goodness i don't like this thing fa, nace kasawa yarinya albarka an you have started your muslim prayer, ah"

"Ah ma leave him to finish pls" goodness ta fada fuskarta cikeda damuwa

Tashi ma tayi ta dauki Bible dinta ta wuce dakinta ta kyalesu a falon.

*Ummi A'isha*👌🏻
[10/28, 9:25 PM] ‪+234 810 100 9022‬: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_*8-10*_

~~~Juyowa goodness tayi ta kalli mahaifinta wanda fuskarsa ke dauke da alamun damuwa a tattare da ita,

_"am sorry baba"_ tafada idonta taf da kwalla,

"Kar kiyi kuka babu komai, abinda nake so dake shine kiyi hakuri da rayuwa aduk yanayin da tazo miki, duk da cewa nasan yanzu banida kalmar da zan iya fada miki tayi tasiri acikin zuciyarki saboda mahaifiyarki tasa kin taso da tsanar addinin musulunci acikin zuciyarki alhalin kuma musuluncin shine addini na gaskiya, ina yi miki addu,a kamar yadda Yar uwarki ta gane kema Allah yasa ki gane gaskiyar, Allah ya hadaki da *wani haske* acikin rayuwarki"

Yana kaiwa nan ya tashi ya fita daga cikin falon yabarta zaune,

Sam maganar da mahaifinta yayi bata wani tsaya mata arai ba saboda bata fahimci maganganun nasa ba kwata kwata,

Channel ta canza ta kamo wata channel inda ake nuna wani Nigerian film mai suna _bad romance_ ,film din taci gaba da kallo har ma tafito ta sameta tace ta shiga kitchen tayi girki ita zata koma church yanzu,

Tashi tayi tashiga kitchen din ta dora tuwon amala da miyar ogu tana yi tana yan wake wakenta _"there is no one like you, ehhh there is no one like you, ohhh there is no one like you"_
Muryar promise saurayinta ta jiyo atsakar gidan yana kwalla mata kira domin shi bashida katanga da gidan duk lokacin da ya ga dama zuwa yake,

Lekowa tayi ta hango shi wuyansa dauke da wani siririyar chain mai tambarin cross ajiki, ga suma da ya tara tuli guda, faratan sa kuwa tamkar na mage saboda tsayinsu,

"Welcome dear, ka shiga ciki ina zuwa" ta fada tareda sake komawa cikin kitchen din, amalar da miya ta zubo masa tazo ta sameshi a falo yana kallon film din da ta tashi tabari,

Abincin ta ajiye masa ta zauna kusa dashi, "dear ranar monday zanje na karbo upper dina"

Kamo hannunta promise yayi fuskarsa dauke da fara,a "congratulations my dear, nayi murna saboda nasan bikinmu ya kusa"

Kafadarsa ta dan kaiwa duka "see you, kaci tuwo gashi"

Hannun yasa yafara cin amalar yana dariya "dama nadade da yin mafarkin wannan lokaci, nayi mafarki zaki samu wani abu ashe wannan aikin zaki samu"

"Nima fa sai da nayi mafarkin dear, kabari kawai ma taci burin wannan auren namu tayi shiri sosai don tunkararsa"

"Yes oh,i like this" yafada yana kai loma, dariya goodness tayi takai masa kiss a kumatu.

*

Ranar monday kamar yadda nura yace haka goodness ta tashi cikeda murna,doki, da kuma farin ciki ta shirya cikin riga da wando na jeans da t shirt tasamo hill shoe mai mutukar tsini tasa tayiwa ma da babanta sallama nufi Abu Al'amin company ltd, lokacin karfe _8:30_ na safe.

Lokacin da taje company din bata wani sha wahala ba aka nuna mata office din da zataje ta karbi offer dinta bayan anyi mata verification, zama tayi tana jiran mutumin da zai bata offer din domin har lokacin bai zo ba.

Tana nan zaune tana ta kallon ma'aikatan kamfanin yanda kowa yake zuwa yake bude office dinsa ya shiga gashi company din kato ne yanada tsananin girma, gefe ga kuma wani dan madaidaicin masallaci, bin offices din da ido tayi ta yi tana jinjina tsaruwarsu,hawa hawa kowanne department da side dinsu, tana ta wadannan kalle kalle har wanda take yazo, ya bude kofar office dinsa ya shiga, mikewa tsaye tayi tana cewa "welcome Sir" gamida binsa cikin office din,

"Are you goodness jacob?" Mutumin ya tambayeta,

"Yes sir, nice" tafada tana dan rissinawa, wurin zama ya bata sannan ya karbi original din credentials dinta ya dudduba, bayan yagama gani ya dauko wata zungureriyar wasika ya bata, a lokacin ta rubuta acceptance letter ta bashi ta tafi bayan ya sanar da ita cewar next week zata fara halartar office, cikeda farin ciki ta koma gida tana zuwa ta rungume ma wadda take cikin kitchen tana harhadawa papa goodness kayan shan ruwa, nan ma ta shiga yi mata hudubar babu ita babu musulmi, kar ta yarda tayi wata mu'amula ta arziki dasu.

Cikin wadannan kwanakin goodness duk tayi sune kan shirye shiryen yadda zata fara zuwa office, tayi wanki ta goge kayanta kaf, ko ranar lahadi da taje church cikeda murna take, suna tashi daga church tabi promise ta rakashi wani club inda ake wani party, sai wurin _9_ ta dawo gida ta bar promise acan yana cashewa yana kora giya.

Washe gari ranar monday _9_ dai dai a office tayi mata nan aka nuna mata office dinta ta shiga a matsayinta na secretary din Genera manager wanda za arinka bata albashi akan naira _25,000_ banda wasu allowances da zata rinka samu, office din GM din ya hadu iya haduwa sanyin AC sai tashi yake tako ina, a falo office din nata yake wanda aka zuba mata kujeru da tebur ga kuma drawers na ajiye files,shi kuma ogan office dinshi na ciki.

Wani dan ihu ta saka "yeeehhh" lokacin da ta zauna akan luntsumemiyar kujerarta ta aiki amma da alamar yau GM din bai zo ba saboda taji office din nashi arufe, wayarta ta zaro daga jaka tafara kiran promise, yana dauka ta sanar dashi yau gata a office kuma ga yanayin office din, kashe wayar tayi tana kallon wasu baki wanda suka shigo da alama wurin ogan suka zo nan tayi musu bayanin ance baya nan yayi tafiya zuwa abuja amma acikin satin nan zai dawo.

Kwana uku da fara zuwanta office din har ta dan fara sabawa da mutanen wurin, ranar Thursday lokacin da taje Massinger yake sanar da ita oga yazo, ahankali ta bude kofar office din ogan ta shiga tana sanye da skirt baka na jeans da t shirt light blue tasa takalmi cover shoe baki, kanta daure da bakin dan kwali,

"Excuse me sir" tafada lokacin ta takai tsakiyar office din,

"Yes" yafada ba tareda ya dago kanshi daga file din da yake dubawa ba, hakan ya bata damar kare masa kallo, black beauty ne sosai dogo marar jiki mai dogon hanci, akwai saje agefen fuskarsa ga dan karamin gemu da ya tara, bakinshi kamar na mace domin wani dan tsut ne sai dai lips dinsa jajaye ne jur, yana sanye cikin milk colour din shadda da hula kalar kayan amma duk da yasa hular hakan bai hanata ganin tabon sallar dake manne agaban goshinsa ba saboda ya dan tura hular tasa zuwa keya, ayanda ta kwatanta shekarunsa ba zasu wuce _35_ ba a duniya, gaba daya office din ya cika da kamshin turarensa na _explorer_.

Tsayawa tayi kyam agaban teburinsa tana kallonsa ko kiftawa ba tayi,shi kuwa bai dago ya kalleta ba har sai da ya kammala abinda yake yi, ahankali ya dago manyan fararen idanuwansa ya zubasu akanta,

_"good morning sir"_ tafada cikin rawar murya saboda ganin baiwar surar da Allah ya hore masa,

_"morning"_ yafada atakaice cikin sanyayyiyar muryarsa, juyawa tayi zata tafi har taje bakin kofa taji yace,

"Aturo min director admin and finance" cikin maganarsa d'ai d'ai, domin kalma kalma yake maganar ahankali, gashi muryar sa ta cika sanyi sai kace cool water.

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[10/28, 9:25 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/20, 9:27 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_11-15_

~~~ "Ok sir" tafada cikin in ina tareda bude kofar office din tafita tanata ayyana maganar wannan bawan Allah acikin ranta gashi wani dan gayu dashi, massinger ta aika ya kirawo masa daf din kamar yadda yace.

Tana nan zaune akan kujerarta tana yan dube duben files din da aka fito dasu daga office dinshi,

Karshen wata wasika ta duba wadda ya rubuta hatta wasikar kamshin turarensa take yi, sai alokacin idonta yakai kan sunansa JABIR.M. AHMAD, jabir ta maimaita sunan tana mai shafa sunan nasa da hannunta, director ne yafito yace da ita ki shiga GM yana kiranki,

Tsam ta mike ta shiga office din yanzu kuma jarida yake dubawa ta daily trust ya dorata akan table din gabansa, duk da yaji maganarta amma bai dago ba har sai da yakai aya lokacin tafi minti 2 a tsaye,

Dagowa yayi ya kalleta ahankali ya fara magana, "staff officer ya sanar dake dukkan ayyukanki?"

Tabbas staff officer ya sanar da ita amma saboda tana bukatar taci gaba da sauraron maganarsa wacce yake yi dalla dalla yasa tace,

"No sir"

Dan lasar lebensa nakasa yayi ya mayar da idanuwansa kan jaridar da yake karantawa,
Chapter 2 · 0% Book details