← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 64

Sashe 53

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To saboda wannan tafarnuwar da naci ne, mala'ikun rahma basa zuwa kusa da mutumin da yaci danyar albasa ko kuma tafarnuwa shiyasa alokacin manzon Allah annabi yace duk wanda yaci tafarnuwa ko albasa to kar yazo mana masallaci domin annabi baya sonta ko kadan amma kuma yana kaunar zuma sosai"

"Mun gode abbu" al'amin yafada yana dariya, inda suke jabir yaje ya zauna yafara tayasu aikin shirmen da suke yi yayinda ita kuma ummu ta mike adoguwar kujera ta kwanta tana hangosu daga inda take har tasamu bacci ya dauketa.

Suna nan zaune sunata buga game din da al'amin da jabir ganin jabir zai yi wining din al'amin ya sanya bahijja shigar masa suka cigaba dayi tare itada jabir har ummu ta tashi daga baccin da takeyi ta shiga kitchen ta fara aiki, binta bahijja tayi ta tayata har suka kammala.

K'arfe 4 suka fita mike kafa, ita ummu tana rikeda hannun jabir kamar wanine zai kwace mata shi ita kuma bahijja tana makale da na al'amin, har dare yayi suna cikin gari domin bude ido sai da dare ya danyi sosai sannan su jabir suka raka su bahijja masaukinsu,

Yauma kamar jiya bahijja kasa bacci tayi amma ta dan sassautawa zuciyarta wannan ne ma ya sanyata niyyar yin watsi da tunanin jabir da ummu ta rungumi ibadar da tazo yi domin samun dacewa saboda taji jabir yace duk wanda yayi umarah kuma ya kyautata to kamar ya rayu tare da annabi ne, ta dukufa sosai wurin yiwa mahaifiyarta addu'a akan itama Allah ya ganar da ita gaskiya yasa ta samu *wani haske* acikin rayuwarta.

Yanzu kullum a masallaci suke wuni suna sallolin nafila da karatun alqur'ani da sauran nau'o'in ibada har kwanakin suka shude domin yanzu har sun fara shirye shiryen komawa Nigeria kasarmu ta gado,

Ana saura kwana uku su tafi jabir ya dauki ummu da bahijja sukaje wani makeken supermarket domin yin siyayya, cemusu yayi kowaccensu ta dauki abunda take so, hakan yasa bahijja nutsawa cikin supermarket din ta shiga boutique inda ake sayar da kayan sakawa na maza, gajerun wando da kayan shan iska ta fara diba,duk wani abu da tagani na maza wanda ya burgeta sai ta daukawa jabir dama haka ya kamata duk abinda mace taga ya burgeta to kamata yayi ta saiwa mijinta yayi mata kwalliya dashi,kayan data daukawa kanta kadanne sai yan gidansu data daddaukawa abubuwan da ba arasa ba, lokacin da sukaje wurin biyan kudin kayan kallonta Ummu ta tsaya tana yi tana ganin ikon Allah yarinya karama wacce batafi sa'ar kanwar kanwarta ba tazo tana neman mallake mata miji,

Jidar kayansu suka yi suka nufi gida, masaukinsu bahijja suka fara zuwa ganin kayan sunyi mata yawa yasa jabir daukar mata wani ya tayata suka shigar dashi dakinta,

Tsayawa tayi tana kallonsa duk zuciyarta babu dadi domin agaskiya tana bukatar mijinta kasancewar yau wurin kwanaki 22 kenan rabonta dashi,

"Binti sai da safe?" Yafada bayan ya riko hannayenta,

Shiru tayi masa bata bashi amsa ba amma acan kasan cikin zuciyarta wani irin kololon bakin ciki takeji,

"Bari naje binti kinga Ummu tana jirana"

Hakan da yafada ne yasake tunzurata, hannunta ta fusge ta juya masa baya,

"Binti....!"

Yakira sunanta yana kallonta cikeda mamaki, shiru bata amsaba,

"Binti ni ne nake kiranki amma kika kyaleni?"

Nanma shirun ta sake yi ganin haka yasashi juyawa yafita ya nufi wurin ummu inda itama ta cika tayi fam tana jiran dawowarsa, dauke kanta tayi bata ko kalleshi ba lokacin da ya shigo cikin taxi din har sukaje gida bata ce masa ko uffan ba har suka fita daga taxi din suka shiga cikin gidan,

Sai alokacin tayi magana "ai nazata acan yau zaka kwana" tafada cikin kufula,

Kallonta yayi zuciyarsa cikeda mamaki wato sudai mata sam ba a iya musu duk hakurinka watarana sai sun kaika bango indai akan kishine,

"Ban ganeba" yafada yana kokarin cire rigar jikinsa,

"Dama ai bazaka ganeba" tafada gamida figar jakar kayanta tanufi cikin dakinta, bin bayanta yayi yashiga toilet yayi wanka yafito, itama toilet din tashiga tayi wankan tafito ta shirya tana gamawa tazo inda jabir yake kwance ta kwanta ta juya masa baya.

Juyo da ita yayi yafara rarrashinta "haba ummu al'amin, bai kamata muyi irin wannan rabuwar ba dake, antyn al'amin fa batafi matsayin kanwarki ba dan Allah kar ki daga hankalinki akanta"

"To ai abu al'amin gani nayine kamar kafi sonta shiyasa"

Sakata yayi acikin jikinsa yana murmushi "haba ummu bai dace kiyi irin wannan tunanin ba, koda ace zanso wata mace to bayanki zata bi"

Sai da taji haka sannan ta iya jin sanyi aranta tabar wannan zancen takoma fagen soyayya kuma.

Ita kuwa bahijja jabir yana fita tazauna dabas agefen gado zuciyarta cikeda damuwa gashi taga kamar alamun fushi yayi mata,

Rasa inda zata tsoma ranta taji dadi tayi, kukan nan dai data saba yauma shi tayi ta share ta kwanta tafara tuna jabir acikin zuciyarta.

Tun daga ranar jabir bai zo mata ba sai ana igobe zasu tafi da yamma sai gashi yasha kyau cikin yadi kalar ruwan madara, lokacin data ganshi cewa tayi acikin zuciyarta,

"Kai gaskiya abbu kanada kyau kullum yaro kake dawowa"

"Al'amin me ya samu idon naka naga kanata sosawa" ta jiyoshi yana yiwa al'amin magana, daki ta shiga batafi minti 1 da shigaba taji shigowarshi yana dosar inda take tsaye yana zuwa ya rungumeta ta baya,

"Binti badai fushi kike yiwa abbu ba?"

Jin yanda ya kanannadeta yasata kasa yin kwakkwaran motsi,

"Binti" yakira sunanta cikin rada,

"Na'am, bayan kaine katafi kaki dawowa" tafada ashagwabance,

Hannunsa yakai ya rufe bakinta "to ai gani yanzu nazo, kiyi hakuri kinji bintina"

Kalar rarrashin da yasoma yimata ne ya sanyata hakura dan dolenta ba tareda ta shirya ba.

Washe gari misalin karfe 2 suka isa airport domin tafiya, ummu tana rikeda jabir taki sakinshi sai wani kankameshi take yi hakan yasa bahijja acikin ranta cewa "to ku zauna kar ya tafi mana"

Dakyar suka rabu itama bahijjan dakyar ta iya banbare al'amin ajikinta yana kuka tana kuka har suka shiga jirgi, jabir ne ya kwantar da ita agefen jikinsa ya soma rarrashinta daga karshe ya bige da tsokanarta,

"Shiyasa nace miki ki dage ki haifi naki saboda irin wannan amma kin kasa kullum ke kenan acikin yoyo kamar wata agwagwa"

Dariya yasata wacce batayi niyya ba "abbu kana bani dariya"

"Burina kenan binti ko kina son nabaki kuka?"

Kai ta girgiza, suna ta hira shida ita har jirginsu ya tashi suka tasamma kasar Nigeria.

Karfe 3:30 suka sauka mal idi driver yaje ya daukesu ya karasa dasu gida, sashen jabir suka fara shiga nan taga duk kura tako ina, kayan hannunta ta ajiye ta tatafi part dinta nan dinma ba acewa komai domin shima ya hada kura sosai, kayan jikinta ta rage tafito daga ita sai yar body hug green wacce ajiki aka rubuta _its all about me_ da manyan haruffa sai dan short din wandonta jeans baki iya gwiwarta,

Sashen jabir ta koma tana dauke da kayan aiki, lokacin da ta shiga yana tsaye afalo yakasa koda zama ma saboda kurar da take ciki,

"Abbu atsaye kake sai kace soja?" Tafada tareda yin dariya,

"Ehh yau dai kam nazama soja da alama"

"To ai kai ba zaka iya soja ba" tafada lokacin da tagama nade center carpet din da yake shinfide afalon domin fara shara,

"Saboda ni ba namiji bane?" Ya tambayeta yana nannade kafar wandonshi bayan ya cire rigar jikinshi,

"Haba abbu har ka fassarani? Ni ba haka zance ba"

"To me zakice?" Ya tambayeta yana jan rigarta ta baya,

"Abbu wlh kai kam da lawyer kafi dacewa"

"Saboda me?"

"Saboda iya tambayarka"

Murmushi yayi ya dauki mopper, tana shara shikuma yana yin mopping,

"Kinga kuwa yawan tambayoyi babu kyau domin abinda mutanen farko suka yi kenan Allah ya halakar dasu"

"Tambayar?" Ta tambayeshi bayan ta mike tsaye tana rike bayanta,

"Kwarai kuwa, ai mutanen farko akwai su da tambaya musamman ma mutanen annabi musa, a zamaninsa ansamu wani mutum ya mutu to kuma mutane suna zargin ko wanine ya kashe shi amma suna son su tabbatar sai suka tafi wajen annabi Musa sukace ya rokar musu ubangijinsa kan ya fada musu wanda ya kashe wannan mutumin, sai annabi musa yace Allah ya ce su samu saniya su yanka, daga nan sai suka shiga tambayoyi marassa dalili, wacce irin saniya? Wacce kala? A ina zamu samota? Awurin wa take? Daga karshe sai da suka sha wahala sosai kafin su samu saniyar nan saboda yawan kwakwarsu amma da ace tun farko da aka ce musu su samu saniya sun samo basu yi wadannan tambayoyin ba da shikenan bukatarsu ta biya acikin sauki, shiyasa annabi yace da sahabbai acikin wani hadisi, kashedinku da yawan tambayoyi domin abinda ya halakar da wadanda suka gabaceku shine yawan tambayoyinsu da sabawa annabawansu, idan na haneku da wani abu kubarshi, idan kuma na umarceku da wani aiki to ku zo dashi gwargwadon iko"

"To ai abbu kai ba irin tambayoyin mutanen farko kakeyi ba, irin na mutanen yanzu kake yi"

"Kar kiyi min cuwa cuwa dai yanmata"

Kiss tazo tayi masa akumatu ta wuce cikin bedroom dinsa domin sharowa,

Har akayi kiran sallar la'asar sunata aikin, alwala jabir yayi ya tafi salla ita kuma taci gaba da aikin har tagama gyaran dakin nasa tsaf ta kunna turaren wuta na tsinke samfarin touch me nan dakin ya kaure da daddadan kamshin, tana shigar masa da kayansa wanda yazo dashi cikin dakin ya dawo daga sallar,

"Abbu har kadawo?"

"Nadawo, ke kinyi sallar ne?"

Kai ta girgiza "wallahi banyi ba dama so nake nakarasa wannan aikin"

Kusa da ita ya matsa ya tsaya adaf da ita tana dagowa tajita ajikinsa, kafadunta ya dafa "binti duk abinda mutum yake yi to zarar an kira salla ko kuma lokacin salla yayi bari akeyi aje ayi sallar sai adawo aci gaba bawai atsaya har sai an karasa abinda ake yiba, antambayi manzon Allah wanne aikine yafi lada yafi soyuwa awurin Allah? Sai annabi yace _"'as salatu fi waqtiha, ma'ana yin salla akan lokacinta"'_, dan haka duk abinda kikeyi da zarar lokacin salla yayi to ki hakura har sai kinyi salla,mata dayawa acikinku kunada wannan sakacin"
Chapter 53 · 0% Book details