Sashe 3
Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ok, to aikinki ne kula da duk wani shige da fice na files din da akayi amfani dashi anan office din, sannan zaki rinka rubuta duk wata wasika wadda zata fita daga nan office din"
Tunda ya fara bayanin take binsa da kallo musammam ma dan karamin bakinsa mai dauke da jajayen lips,
"Kin gane" yafada a hankali,
"Yes sir"
"Kina iya tafiya"
"Ok sir" tafada tareda juyawa tafita daga cikin office din.
Kujerarta ta koma ta zauna tana jinjina isa da takama irin na wannan mutumin kodai dan yaga yana da kudine, ko dan yana da kyau? Tana nan zaune yafito daga office dinshi yana gyaggyara hannuwan rigarshi da alama alwala yayi zai tafi salla,
"Adawo lafiya sir" tafada bayan ta mike tsaye
"Yawwa" yafada a takaice, yafice,komawa tayi ta zauna jagwaf tana cewa "ohh wannan mutum da rashin kulawa da mutane yake".
Mintuna kadan wadanda ba zasu wuce 20 ba ya dawo ya wuce cikin office din shi. Kallo ta bishi dashi har ya shige office din shi ta jiyo tana jijjiga kai.
Lokacin tashi yana yi ta tattara kayanta ta nufi gida lokacin karfe _5:00_ dai dai, tana zuwa ta tarar da ma bata nan har ta tafi church sai iya babanta ne agidan, wanka kawai tayi taci teba miyar kuka wadda ta tarar an dafa agidan ta dauki Bible dinta ta nufi church.
Washe gari ya kama friday kamar yadda ta saba haka ta shirya ta tafi office, lokacin da taje GM din bai zo ba dan haka ta zauna tafara karanta jaridar sa da aka kawo masa, tana cikin karantawar ne ta jiyo kamshin turare mai mutukar dadi hakan ya sata tsaida idanuwanta akan hanyar shigowa, minti kadan ya bullo yana sanye da farar shadda sai kyalli take dinkin tazarce, kansa dauke da hula ja yana amsa call, cikin sauri ta mike tsaye tana yi masa sannu da zuwa, hannu kawai ya daga mata ya wuce cikin office dinsa.
Mintuna biyu da shigarsa ta dauki jaridunsa guda biyu ta shiga office din,
Good morning sir"
"Morning" yafada ba tare da ya dago ya kalleta ba, jaridun ta ajiye ta juya ta fita, zama tayi tana tunanin to shi wannan wanne irin mutum ne ? Sai dai kuma fa yanayinsa da wannan dabi'un nasa sun burgeta saboda ita mutum marar hayaniya yana mutukar burgeta maganar Massinger ne ya katseta,
"Oga yana kiranki"
Cikin sauri ta mike ta shiga ciki, ta tsaya "gani sir"
Rubutun da yake yi yaci gaba dayi, "yau ba aturo min wani mail daga office din governor ba?"
"Eh ba aturo ba sir"
"To zasu turo,idan an kawo ko bana nan ki turawa director personnel, meeting za muyi da governor zasu bayar da kwangilar gina gidajen ma'aikata guda dari biyar"
Idonta kyam akan bakinsa yanda yake mul mul da baki yana yi mata bayani ita dai wannan bakin nasa yana burgeta, jin shiru bata amsa ba yasa shi dagowa ya kalleta kur yaga ta kura masa idanuwa ko kiftawa ba tayi,
"Kina jina?", yafada tareda dan buga teburin gabansa, firgigit tayi ta fara yan kame kame,
"Yes sir, zasu kawo, eh zan kawo maka"
Girgiza kai yayi yace "you can go" acikin ransa kuma yana cewa "anya kuwa wannan yarinyar kanta daya? Sai ayita yimata magana amma ba zata amsaba sai dai ta zubawa mutum ido"
Tana fita taga wasu baki sunzo su biyu mata nan tafara binsu da kallo daya bayan daya,
"Ya akayi?" Tafada lokacin da take zama akan kujerarta,
"Sannu sakatariya munzo ganin malam jabir ne" daya daga cikin bakin tafada,
"Yasan da zuwanku? Shi ya baku appointment?" Tafada tana yatsina fuska
"Eh shine yace muzo office mu sameshi"
"To yanzu dai bazai samu damar ganinku ba saboda aiki yake yi" tafada tana janyo drawer zata dauko wani file,
"Haba ranki ya dade ki shiga ki sanar masa mana idan yaga zai ganmu sai mu shiga idan kuma bazai ganmu ba ahikenan"
"Bazai ganku ba"
Mikewa sukayi suka fita zukatansu babu dadi, kallo ta bisu dashi "an fada muku ina haukane da zan barku ku shiga wurin wannan zankadeden? Ai wannan nawane" tafada tana murmushi.
Tun daga wannan rana goodness ta bullo da sabon salo domin duk bakuwar da tazo ganin GM bata barinta ta shiga mazan ma sai tayi niyya, yauma tana zaune akan kujerar ta ta hada tea saboda lokacin da ta fito daga gida bata yi breakfast ba, wata mata ta shigo yar madaidaiciya da ita tasha les mai tsada tana ta kamshi tace tazo ganin GM nan goodness tace baya nan, matar tace "munyi waya fa dashi shine yace nazo yau"
Karkacewa goodness tayi tace "to sai ki kirashi ki fada masa ai"
Juyawa matar tayi tafita tana zaro wayarta daga cikin jakarta, ko minti biyar ba ayiba sai gashi ya fito da kansa, kanshi ko hula babu hakan ya kara masa kyau,
"Meyasa idan nayi baki bakya zuwa ki fada min sai dai kice musu bana nan? Wannan aikin nasaki?
"Sorry sir" tafada tana kallon fuskarsa,
"Yanzu kinga meeting zamu yi da S. A ta commerce and industry amma tazo kince mata bana nan alhalin kuma abinda zamu tattauna da ita abune mai muhimmanci"
"Sorry Sir" tafada tana zare ido,
"Bani mail din da aka kawo min daga code of conduct bureau"
Hannu ta mika ta zaro takakardar cikin rashin sa'a kofin shayin data hada ya tuntsire akan takardar tare da sauran files din dake kan tebur din.
_*Ummi Shatu*_👌🏻
[10/28, 9:26 PM] +234 810 100 9022: [8/21, 2:52 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_16-20_
~~~Kallonta yayi da manyan dara daran fararen idanuwansa ya juya ya koma office ba tare da yace da ita komai ba, hakan ya sake rudata,
_"ohh God help me pls, pls God"_ tafada arude lokacin da tafara diri diri acikin office din,
"Allah yasa kar oga ya bani query yau"
Hankalinta atashe ta dauki mail din ta bashi cikin office dinshi, lokacin da ta shiga baya kan kujerarsa, yana can kan wata doguwar kujera ta zaman baki, ya dora kafafuwansa akan dan glass table din dake gaban kujerar, yana kallon wata tasha a satellite wacce aka saka karatun alwur'ani mai girma, indai bata manta ba tun lokacin data fara shigowa office dinshi wannan channel din taga yana kunnuwa koda yaushe,
"Am sorry sir" tafada tana rikeda takardar,
"Je ki dorata akan table dina" yafada ba tare da ya kalleta ba domin idonshi yana kan TV,
"Thank you sir" tafada tareda juyawa ta nufi kan table dinshi ta dora mail din ta juya ta fita daga cikin office din zuciyarta cikeda murna.
Karfe biyar ta tashi ta tafi gida tana zuwa ta tarar da sister dinta tazo anty bilkisu sai dai ita musulma ce, suna zaune itada mahaifinsu suna hira goodness ta shiga kunnenta sakale da earphone tana sauraren d banj cikin wakarsa ta _a new day has come_ tana bin wakar ta shiga falon, ganin anty bilkisu yasata dariya, "hey when did you come?"
"Tun safe nazo ashe kin fara zuwa office?"
"Inata so ai nazo gidanki na fada miki ban samu time ba"
"Ayya babu komai Allah ya sanya alkairi" yayar tata tafada tana kare mata kallo yadda ta dame cikin wasu riga da wando,
"Amin, ma taje church ko?"
"Tun dazu ta tafi" inji mahaifinta,
"Oh make i quick because we have weekly prayer today" tana gama fadin haka tayi wurgi da jakarta ta shige daki ta dauko bible dinta ta ajiye akan kujera, ta shiga kitchen ta zubo abinci, sakwara miyar agushi, kusa da anty bilki tazo ta zauna tafara cin abincinta tana cewa "anty ya mijinki? Ranan mun dawo daga church nida promise da ma mun ganshi amma shi bai ganmu ba"
Murmushi anty bilki tayi "ya fada min shima ya ganku" amma acan kasan ranta wani bacin rai takeji marar kwatantuwa, ace mahaifiyarta da yar uwarta basu bawa annabi Muhammad (S.A.W) gaskiya ba,
Mintuna kadan ta cinye abincin ta dauki Bible dinta tafita tana cewa "anty idan nadawo na sameki to, idan kuma kin tafi kigaida mijinki"
Tana fita anty bilki ta dubi mahaifinsu, "yanzu baba haka zamu ci gaba da ganin mama da goodness suna zuwa church? Addininsu daban namu daban yanzu hakan yayi daidai?"
Girgiza kai yayi "Bilkisu halin mahaifiyarku sai ita, da ace tanada rabon musulunta da tuni ta musulunta to bata da rabo, tun kuna yara kanana ni na musulunta amma ita taki saboda macece mai taurin kai da kafiya, ke kuwa lokacin da ta fahimci kina sha'awar musulunci tun daga nan ta tsaneki tamkar ba itace ta haifeki ba, da salla babu abinda take miki haka zata barki kaca kaca dake amma idan Christmas tazo kar kiso kiga irin kwalliyar da take yiwa goodness, nidai ina nan ina yi musu addu'a akan Allah ya shiryar dasu, kema kici gaba da addu'a kinji?"
Kwallar idonta ta share saboda tabbas tasan tasha wahala a hannun mama dalilin bin mahaifinta da tayi ta taso a musulma dama yar gata sai goodness itace shalele saboda halinsu daya da mama wurin kyamar addinin musulunci, su a kafiran ma yan akida ne,
"Babu komai baba, zanje nakoma" tashi tayi tareda ajiye masa wasu yan kudi wanda ba zasu haura dariya shida ba domin yanzu baya aiki ya jima da yin retire.
Lokacin da goodness ta taso daga church tare suka taho da saurayinta promise, wata yar karamar robar giya ya dauko daga cikin aljihunsa ya fara kurba,
Bata rai tayi ta dauke kanta, "promise am tired with your habit, baka da aiki sai shan giya? Gaskiya yana da kyau ka daina shan giya, kazama dan gayu kadaina wadannan halayen"
Kallonta promise yayi da kyau "goodness har lokaci yayi da zaki fara cewa kin gaji halayena? Goodness kece kuwa, nine fa promise dinki masoyinki, ko har kin fara mantawa dani ne?"
"Ni ba wannan maganar nake maka ba kawai dai ina son kadaina wannan shan giyar ne"
Jijjiga kai yayi yace "good kije gida zanzo nasameki agida"
Batare da tace masa komai ba ta wuce tabarshi awurin tana tunanin ita yanzu koda zata auri promise to sai ya koma irin oganta na office wato GM, kai bama ta tunanin zata iya auran promise din.