← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 64

Sashe 16

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihu al'amin yasa "yes oh anty you didn't catch me"

Dagudu ya tafi wurin abbunshi yana dariya, kunyace duk ta kamata saboda rungumar da ta yiwa jabir bata wasa bace ta gaske ce sosai,

"Al'amin i will catch you next time"

"Abbu mutafi tunda na yiwa anty wayo ta kasa kamani"

Murmushi jabir yayi ya kama hannunsa suka juya suka fita, zama tayi sharafff akan kujera "oh oh this clever boy make me to fell shy".

Tunda suka fita jabir yaji goodness ta dan burgeshi saboda yadda ta saki jiki da yaronshi kwallo daya tal a duniya,gashi tana biye masa suyita wasa kamar wani sa'anta hakanne ya sashi niyyar bata wani dan karamin muhalli acikin zuciyarsa dalilin soyayyar da take yiwa gudan jininsa al'amin.

_*Ummi Aisha*_👌🏻
[10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/3, 3:29 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_45-47_

~~~Koda suka je shagon askin ma tunani ne fal acikin zuciyarsa gameda goodness duk da yasan ba wani sonta yake ba amma yasan baya jin tsanarta yanzu acikin zuciyarsa saboda soyayyar da take yiwa al'amin.

Ana kiraye kirayen sallar magrib suka dawo gida, a masallaci suka tsaya ba tareda sun shiga cikin gidan ba har sai da aka idar da sallar isha sannan yaja al'amin suka shiga cikin gidan domin yau babu karatu,

Lokacin da suka shiga misalin karfi _8:30_ ,kansa tsaye part din ummu ya shiga shida al'amin kamar kullum tana zaune akan abun salla da alama salla ta idar ga tashar sunnah tv tana kallo,

Zama yayi akan kujera yayinda al'amin yaje ya dale bayanta wai ta goyashi,

"Ummu al'amin ina tunanin fa nan da three weeks zaki bar kasar nan zuwa madina saboda admission dinnan naki ya fito fa gashi komai sunyi shi acikin kurarren lokaci"

Kallonsa tayi lokacin da take mikewa da al'amin a bayanta tana ninke abin sallarta,

"Abu al'amin dagaske? Shine baka sanar dani ba? To ya zamu shirya tafiyar?"

"Eh zan fara kaiki idan munje nayi miki registration nagama zan taho nabarki saboda lectures zaku fara nanda sati ukun wannan session din basu fitar da admission din da wuri ba, idan kika fara karatun sai ki bincikawa al'amin makaranta anan kusa dake sai na kawo miki shi, amma yanzu tafiyar ba zata yiyu dashi ba domin gaskiya visa tana wahala, ni dinma ba lallai ne nasamu ba kinga idan ban samu ba sai dai ki tafi ke daya"

Murmushi tayi tana jijjiga al'amin dake bayanta wanda yake shirin yin bacci,

"Ai kuwa nima bazan je ba indai babu kai"

"Da wasa kike ummu, ai tafiya ta kamaki ko ke kadai ce tunda karatu zaki je"

"Haka dai kace" daki ta shiga domin kwantar da al'amin shi kuma ya tashi ya fita ya nufi sashensa.

Bai sake fitowa ba sai da gari ya waye, bayan ya shirya yayi breakfast ya fito domin tafiya office, falon goodness ya shiga, hangota yayi tana yin mopping din tiles din dining area dinta gashi kuma kamar kullum yau ma ta music dinta tana sauraren wakar p square cikin wakarsa ta _"teaching me how to love you"_

Daga ita sai wani gajeren wando baki iya cinya da _vest_ baka tana faman bin wakar da take sauraro,

_Remote_ ya dauka ya fara rage volume din tv din gamida juyowa ya kalleta, ita dinma juyowar tayi nan suka hada ido,

"Ke wannan k'arar bata damunki ne wai?"

"Morning sir" tafada tana sunkuyar da kanta k'asa,

"Morning how you?" Ya fada yana gyara zaman hularshi akanshi,

_"wow! This dress suit you my cool"_ tafada ahankali domin yau ba fararen kaya ya saka ba, wata hadaddiyar shadda ya sa kalarta ruwan toka dinkin samfarin boda sannan yasa hula ash colour mai digon baki ajiki, takalmin kafarshi _half cover_ shima kalar ruwan toka ga wani agogon fata da ya daura shima kalar kayansa ga wani irin kamshi mai dadi da yake fita daga jikinsa, gemunsa da sajensa ya gyarasu ya tajesu sai sheki suke, nikaina ummi nace lallai malamai yan gayune ga iya kwalliya,

Kallonta yayi yana balle clips din hannun rigarsa "me kike cewa?"

"No sir bance komai ba"

"Ok naje office" juyawa yayi ya fita nan tabishi tana lek'enshi ta window har sai da taga shigarshi mota taga fitarsa daga gidan sannan ta koma taci gaba da aikinta tana yi tana murmushi "he's good looking" tafada tana murmushi.

Tun ranar da promise yakai goodness club tun lokacin bata kara zuwa church ba hakan ba k'aramin tayarwa da mamanta hankali yayi ba nan ta shiga nemanta a waya dakyar ta samu layin goodness din, lokacin ita goodness ma kwance take a falonta tana karanta Bible dinta,

"Hello ma, good afternoon"

"Goodness hold your greetings i didn't want it, yaushe rabonki da church? Goodness yaushe kika zama strong headed? Goodness ki dawo cikin hankalinki fa tun kafin mijinki yayi deceiving naki"

"Am sorry ma, ba wai nadaina zuwa church bane, kinga yanzu tafiyar daga gidana zuwa church is too long, how many kobo will i spent for the transport from my house to that church? Shiyasa nayi deciding zan rinka zuwa duk ranar Sunday kuma tunda there is one church near my house zan rinka zuwa can daily service"

"Ok yanzu nagane, so kiyi kokari kina zuwa ranar Sunday din"

"Don't worry ma, i shall come by God willing"

"Thank you my daughter, bye bye take care"

Tana katse wayar ta saki nannauyar ajiyar zuciya dan ba karamin sa'a tayi ba da ma ta amince da abinda ta fada.

Tun daga lokacin goodness take zuwa church sau 1 a sati saboda dokar da jabir ya kafa mata, yayinda ita kuma ummu al'amin keta shirye shiryen tafiya madina garin manzo domin gudanar da karatu, a bangaren jabir shima hakan take domin har ya karbo musu visa dinsu,yanzu baifi kwana 6 ya rage su tafi ba.

Goodness zaune a falonta bayan ta kammala taje gashin kanta, agogo ta kalla karfe 9:30 nadare agogon bangon nata ya nuna yanzu tasan jabir ya dawo gida daga wurin karatu dan haka ta mike ta dauki dan siririn mayafinta domin so take taje ayi mata kitso a shagon _blessing_ shiyasa take son yanzu taje ta dauki _permission_ awurin oga,

Riga da wando ne ajikinta, rigar milk colour marar nauyi shikuma wandon samfurin _pencil_ kalarshi ja,

Ahankali ta bude falon ta shiga, a babban falo ta dan tsaya tana lekewa ahankali, al'amin ta gani zaune kusa da jabir, hannun al'amin rike da wani littafi mai yatsu guda uku ajiki,

"Abbu banyi fassara ba, ka tambayeni fassarar" ta jiyo muryar al'amin yana fada,

"To al'amin yi min inji, waye ubangijikinka?"

"Allah ne ubangijina wanda ya halicceni,ya reneni, da ni'imominsa"

"Da wanne abune kake sanin ubangijinka?"

"Ina sanin ubangijina da alamomi masu yawa, daga cikinsu akwai dare da yini, da rana da wata"

"Waye ya halicci sammai da kassai,da rana da wata?"

"Abbu Allah shine ya halicci kasa wacce muke tafiya akanta, ya halacci sama wadda rana take cikinta, ya halicci wata da taurari wanda suke acikin sama, ya halicci mutane,da duwarwatsu, da bishiyoyi,da dukkan komai,Allah shine yake saukar da ruwan sama, yake fitar da tsirrai,yake azurta bayinsa, yake basu lafiya, Allah shi kadai ya cancanta a bauta masa ba tareda kowa ba"

"Jayyid, jamilun jiddan al'amin, to yanzu ina zan dora maka?"

Sak'are goodness tayi tana kallonsu amma kuma wadannan abubuwan fa da suka fada abin dubawa ne, tabbas wannan addinin nasu akwai *wani haske* acikinsa tunda gashi har al'amin ma yaro karami yana iya fadarsa,

Kanta ta kutsa cikin falon tana kallonsu,

"Weldon sir" tafada tareda dan rissinawa,

"Yawwa" yafada yana kallonta, domin bata saba shigowa sashensa ba,

"Sir ina son zanje kitso ne gobe"

"Which place?" Ya tambayeta yana kallonta,

"Sir near unity bank, unguwar sarki"

"Ok Allah ya kaimu goben, zan baki kudin kitson before i left"

"Ok thank you sir"

"Anty zan rakaki" al'amin ya fada yana murna,

"To al'amin zanje dakai"

Juyawa tayi ta koma sashenta taje ta cigaba da kallon tv. Washe gari kafin ya fita kamar yadda yace ya shigo ya bata kudin kitson ya tafi, dan haka tana gama abubuwan da zatayi tayi wanka ta tafi kitson wanda tun safe sai daf da magrib aka gamashi, kitson attach aka yi mata yifi yifi mai yawan gaske, lokacin da ta dawo gida su al'amin na shirin fita masallaci shida abbunshi.

Bayan sun fito daga sallar ne misalin karfe 8:30 suka shiga sashenta anan suka sameta tana shan ruwan lipton daga ita sai towel a daure ajikinta, kitson nan nata yayi asalin yin kyau kamar bada hannu aka yi ba,

"Sai yanzu kika dawo?" Jabir ya tambayeta yana kallonta,

"Eh wlh sir kitsonne dayawa shiyasa" ta bashi amsa tana kallon al'amin wanda ya kura mata ido yana kallonta.

"Anty babu kyau k'arin gashi, kidaina domin annabi ya la'anci matar da take kara gashi da wadda ake karawa, da mai yin wushirya,ko abbuna? Ai kaine ka koya min hadisin ko?" Ya fada yana girgiza hannun jabir,

"Zan daina al'amin kaji? Zan daina" tafada tana murmushi, juyawa jabir yayi yaja hannun al'amin suka fita daga daki zuciyarsa cikeda mamakin yaronshi al'amin hakika yaron nan wayonsa yayi yawa gashi da iya rike abu sam bashida mantuwa girgiza kai yayi koda yake ai annabi yace "karatun yaro kamar rubutune akan dutse, karatun babba kuma tamkar rubutu ne akan ruwa"

Tabbas wannan magana haka take domin al'amin duk abinda aka koya masa to ya daukeshi kenan acikin kwakwalwarsa shiyasa har yanzu bai daina bashi zamzam da Zuma yana sha ba.

***

Acikin "yan kwanakin ummu har ta kammala shirinta na tafiya haka shima jabir duk ta harhada masa nasa kayan wanda zai bukata acan duk da shi ba wani jimawa zaiyi ba sati uku kacal zaiyi ya dawo,

Ana i gobe zasu tafi ya dauki al'amin ya kaishi gidan malam mahaifinshi daga can yayi sallama dasu ya dawo gida, aranar da daddare ummu ta shiga wurin goodness take sanar mata da batun tafiyarta gobe wanda idan ta tafi zata dade bata zo ba may be ma sai ta shekara 2 ko 3 kafin ta zo gida,

Duk da ba wani zama suka yi mai yawa ba sai da goodness taji babu dadi, tareda yi mata fatan alkairi anan ummu ta tashi ta koma sashenta wurin jabir.
Chapter 16 · 0% Book details