← Book details Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 64

Sashe 17

Wani Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari bayan sun kammala shirinsu an fito musu da kayayyakinsu an saka acikin mota mal jabir da ummu suka shiga wurin goodness tana kitchen tana shirya breakfast dinta taji motsinsu, da sauri ta fito ta gaishesu,

"Za muyi tafiya da ummu al'amin amma ni sati uku zanyi nadawo, al'amin ma yana nan sai daga baya zan kaishi idan ta sama masa school din da zai yi acan, ga wannan ki ajiye saboda ko zaki bukaci wani abu, sannan daga karshe banda fita rampantly, ranar Sunday kawai na yarda ki fita kije Church amma baya ga wannan ko menene indai ba halin rashin lafiya ba ban yarda ki fita ba"

Kudi ya mika mata rafa biyu yan dari bibbiyu, hannu tasa ta karba duk jikinta yayi mata wani irin sanyi,

"Idan akwai abunda nayi miki kiyi hakuri ki yafe min, nima na yafe miki" ummu al'amin ta fada tana kallonta,

"No maman al'amin honest to God you didn't done anything wrong to me, i pardoned you if there is something wrong"

Tafada ranta duk babu dadi domin zaman gidan tasan bazai yi mata dadi ba ita kadai gashi ko al'amin dinma ba abarshi awurinta ba,

"Sai na dawo" yafada tareda juyawa ya fita ummu na biye dashi, ajiye kudin tayi tabi bayansu tana sanye da kayan bacci _cotton_ riga da wando da hula akanta baka,

Bakin motar da zasu shiga ta tsaya anan kuma ta fara hawaye, kuka tafara sosai marar sauti, yana hangota lokacin da yake kokarin shiga cikin motar, har ya shiga sai kuma ya fito yazo inda take tsaye tana faman kuka ya kama hannunta da tattausan hannunshi mai laushi,

Part dinta ya nufa da ita yayinda ita kuma hawaye ke cigaba da zarya akan kumatunta, har cikin falonta ya shigar da ita, manyan dara daran idanuwansa ya daga ya kalleta,idonta arufe suke tana hawaye shar sharrrrrr,

Hannuwansa biyu yasa ya dafe kumatunta for the first time da yaji tausayinta acikin ranshi har yaji wani abu wanda bai san ko menene ba yana yawo acikin jijiyoyin jinin jikinshi,

Bakinsa yasa akan goshinta yayi mata wani zazzafan kiss, cikin sauri ta bude idonta ta dagasu ta kalleshi har lokacin bakinsa nakan goshinta bai dauke ba ga hannunshi duka biyu akan fuskarta,

Lumshe idonta ta sake yi take wasu hawayen suka sake kwaranyowa akan kumatunta, amma kuma tana cikeda tsananin farin ciki saboda yau ya nuna kulawarsa agareta,

Bakinsa ya cire daga kan goshinta,ahankali cikin cool voice dinsa yace "ki daina kuka kinji, daga ni har ummu zamu dawo kamar yaune, sannan idan nadawo zan dauko miki al'amin kuci gaba da wasanku tunda naga abokin wasanki ne"

Dariya maganarshi taso bata wai al'amin ne abokin wasanta lallai ma ashe kallon yarinya karama yake yi mata, har alokacin hannayensa na kan kuncinta ya dago kanta,

Saura k'iris maganarshi ta sata dariya, dago da kanta ya sake yi ya manna mata wani kiss din a habarta ya saketa ya juya ya fita,

Gaban window ta karasa ta tsaya tana hangoshi har ya shiga mota inda ummu ke zaman jiransa amma bata damuba dan tasan sallama yake yi da goodness din,

Akan idonta motarsu ta fita daga harabar gidan, wani farin cikine ya lullubeta marar misaltuwa duk da ta kasa gano dalilinsa na rashin yiwa bakinta kiss sai habarta da goshinta da yayiwa, hakanma ba karamin dadi ya sata ba domin ko babu komai for the first time in history dan karamin bakinsa da take kwadayi ya taba jikinta, lumshe ido tayi ta soma tuno yanayin da yasata aciki dazu.

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/3, 9:51 PM] Ummi A'isha👌🏻: *WANI HASKE*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_48-50_

~~~Tana cike da damuwar tafiyarshi har yamma tayi lokacin tasan may be sun sauka agarin _madinah_ ko kuma sun kusa isa,

Raba dare tayi da daddare tana kallo gashi tana son jin muryar nan tashi mai sanyi amma ta kirashi wayar tashi bata shiga dole ta hakura taci gaba da kallon wani Nigerian film atashar African magic mai suna _life partner_ ,har wurin 1 takai na dare tana kallon kafin taje ta kwanta.

Da safe ma haka ta tashi sukuku gidan shuru kamar babu kowa, duk sai taji ranta ya b'aci sa'arta daya da misalin karfe 11 nasafe sai ga yayarta anty bilkisu tazo nan suka bata da adaki suna shan hira.

"Yanzu matar tashi zata dade bata dawo ba kenan?" Anty Bilkisu ta tambayeta,

"Eh tace min zata kai 2 years ko 3 years bata zo ba"

Jijjiga kai anty Bilkisu tayi "am advising you ki rike mijinki ki kyautata masa babu maganar kunya, kinga su matan hausawa kunyace dasu basa iya zagewa su bawa mijinsu kulawa yadda ta kamata shiyasa wasu mazan hausawan sunfi son auren yare domin sunfi basu kulawa ta musamman"

Huduba sosai anty Bilkisu tayi mata wadda ita dai goodness har kunya taji domin batun babu sauki acikinsa anty Bilkisu bata komai take abude babu rufi, har dare suna tare sai wurin karfe 9 sannan mijinta yazo suka tafi.

Cigaba da al'amuranta tayi har su mal jabir suka kwana 8 da tafiya yanzu abinda yafi damunta shine rashin jin muryarsa da kuma rashin ganinsa, mai gadi ta aika gidan malam wurin Baban mal jabir ya amso mata phone number dinshi ta can.

***

Kwanansu biyu da sauka agarin madina mal jabir yayiwa ummu duk wani shige da fice na karatunta, ya gama mata registration yayi komai yanzu lectures kawai zata fara zuwa gashi ya samar mata gidan da zata zauna ita da al'amin Wanda kusa yake da jami'ar da zata rinka zuwa gashi dama gidan na females students ne zalla,

Kwance yake adakin yayinda ummu ke kwance ajikinshi ta gefensa yana yi mata tausa ajikinta, lumshe idonta tayi domin jabir akwai iya soyayya sai dai bashida yawan bukata amma kula da mace kam ko sharukhan nan ya ganshi ya barshi,

Tunani yake yi aransa yau kwananshi 9 a madina amma bai san halin da goodness take cikiba al'amin kuwa kullum sai sunyi waya dashi awayar Malam,

"Yakamata na nemi number yarinyar nan dan jin halin da take ciki saboda ko kazarka ka daure ka tafi wani wuri ka barta ya kamata ace kana bibiyar yanayin da take ciki bare mace mai bukatar a kula da ita" yafada acikin zuciyarsa, karar shigowar text massage yaji awayarshi dan haka ya mika hannu ya dauko ya duba, number Nigeria ce kuma daga gani goodness ce tayi masa text din dan ga abunda tace:

_"Some people have a nice smile, some have a nice face and some have a nice eyes, you, you have all of them and nice heart, you are such a special one to me, i can't explain how i fell so lonely during your absent, I MISS YOU....!"._

Sake maimaita karanta text din yayi sannan ya tashi zaune ya fita falo domin ummu tayi bacci tun tuni, dialling number din goodness din yayi,

Tana kwance tana kallo kiransa ya shigo cikin wayarta,

Da sauri ta tashi zaune ta kara wayar a kunnenta,

"Hello sir"

"Goodness how you? Ya gida?"

"Everything moving fine sir, ina maman al'amin?"

"She's sleeping, nima nakusa dawowa nanda 12 days"

"Ok sir adawo lafiya idan ta tashi send my regard to her pls"

"I shall, babu wani problem ko?"

"Sir babu komai"

"Alright sai anjima"

Katse wayar tayi tabita da kallo tana murmushi har na tsawon wani lokaci.

Shi kam daki ya shiga yaje toilet yayi wanka ya fito ya shirya ya fita cikin gari, kasuwa ya shiga ya fara yiwa al'amin siyayyar tsarabar da zai kawo masa,

Itama goodness doguwar bakar riga mai zubin after dress ya siyo mata guda biyu sannan ganin mayyar english wears ce ita yasashi siyo mata su wurin set shida, riga da wando da skirt, sannan ya siyo mata takalma guda hudu.

Zamansa a madina yasashi bawa ummu kulawa sosai har ana sauran kwana daya ya tafi, kasuwa ummu taje ta yiwa mutanen gida tsaraba ciki harda goodness domin kayan bacci ta siya mata kala biyar masu shegen kyau amma araha banza da yake a madina ne,sannan ta kwaso mata turarruka masu dadin kamshi da sure wurin kala goma goma,

A washe gari jirginsu mal jabir ya d'aga daga madina zuwa Nigeria bayan sunyi sallama da matarsa wacce suke jin kamar karsu rabu da juna.

Tun yana cikin jirgi ya turawa da goodness text massage cewar yau zai dawo kafin sallar isha ko kuma bayanta,

Lokacin da taga text din nasa sashensa ta nufa ta shiga ta shareshi ta gyaggyara ta goge ko ina ta fesa room freshener ta jawo ta rufe ta koma sashenta domin dora masa girki duk da cewar tasan ba lallai bane yaci,

Fried rice tayi ta yi masa yan soye soyen tareda chicken pepe, wanka ta shiga tayi bayan ta gama harhada komai,

Bayan ta fito daga wanka ne ta shirya cikin wata body hug ash colour mai zanen eyes ajiki, daga tsakiyar rigar an rubuta _Dream again_,bakin wando jeans tasaka tareda daura bakin dan kwali bayan ta daure kitson attach dinta da red colour din ribbon.

Misalin karfe 8:30 na dare jirginsu ya sauka, malam idi driver ne yaje ya dauko shi daga airport, goodness na zaune a falonta tana sauraren zuwansu,

Tana zaune tana sauraren music wakar p square acikin wakarsa ta _lifes is so sweet_,alamar bude get din da tajine ya tabbatar mata da cewar sun karaso, bakin window ta tashi taje ta tsaya, ahankali ya bude motar ya fito yana sanye da farar doguwar jallabiya da yar karamar hula fara tas, wani kyau na musamman taga fuskarsa tayi ko kuma dan ta dade bata ganshi bane oho,

Kamar ya shiga part dinta sai kuma ya wuce nashi saboda ko salla bai yi ba, lokacin da ya shiga part din nashi ba karamin dadi yaji ba domin komai a gyare yake tsaf, dakinsa ne dai kawai bata gyara ba shima dan ba a bude yake ba shiyasa,

Alwala ya shiga yayi ya dawo falo ya fara ramuwar sallolin dake kansa yana kan yin sallar ne goodness ta shigo hannayenta dauke da food flaks wadanda ta zuzzuba girkin da tayi mishi aciki,
Chapter 17 · 0% Book details