← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 64

Sashe 9

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                         Page 7️⃣

___________________📖 Sak saurayin da ta faɗa kan sa yayi dan it's unexpected kafin ya ɗan zare ta daga jikin sa ya ja baya kaɗan, zare Ido yayi ganin ta kafin unbelievably ya nuna ta Yana faɗin sunan ta

"Queen, Kisnah".

Da Æ´ar dariyar dake fuskar ta ta furta sunan sa Shima
"Deeq".

A sittin ya sake fisgota jikin sa ya ƙanƙame yana sakin dariyar farin ciki kamar yadda itama ta kasa rufe bakin ta, ƙara zare ta jikin sa yayi ya tsura mata Ido har se da ta hura Masa iska a bakin sa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya sake rungumar ta, wannan karon da kan ta tai breaking hug ɗin kana ta ja kujerar gefen sa ta zauna tana gyara zaman rigar ta da ta ɗan janye zuwa cikin ta.

Zama Shima yayi a kujerar sa ya sake kafe ta da Ido Yana kallo kamar irin Wanda ya Sami film É—in da ya daÉ—e Yana jira, É—an haÉ—e rai tayi tana dukan table É—in gaban su

"Zaka Fara ko Deeq bayan kafi kowa sanin bana San wannan ƙure kallon ko".

"Uhm..hmmm...am..am sorry Kissy, kawai na kasa daina mamaki da jin daÉ—in ganin ki ne, we missed you so badlyyyy".

Ya ƙarashe faɗa Yana Jan ƙarshen kalmar badly ɗin, murmushin ta me cike da aji tayi kafin a ɗan shagwaɓe itama ta mayar Masa da amsa

"I missed you people so much also, it's a kinda feeling I gat at that time, I thought of nothing but home, my country, my land, my pride and my happiness, and as you can see am enjoying it here".

Gyaɗa kansa yayi cikin yarda da abinda tace  "Sure I believe you're enjoying it, but what about we people, you don't have idea how we felt at the time, you leaving without even saying a goodbye is something we didn't expected".

"And am sorry for that, nasan in na faÉ—a muku ba zaku bar ni in tafi ba that's why I choose to just disappear without your consent".

"Allah ya shirya ki, so bani labari, how's life here in naija to you bayan nasan kin Saba da rayuwan Canada".

"The feeling of living in my home is as sweeter as honey, that's what I lack in Canada, but I missed all those partying, clubbing and dancing like hell though am trying to catch up here".

"I see, those girls?.

Ya faÉ—a pointing at su Meenah da suke cin abincin su hankali kwance dan sun Saba irin haka da Kisnah É—in,

"Friends". Ta Bashi amsa a taƙaice, nodding yai Shima without saying anything dan daga yadda ta amsashi ya tuna Kisnah fa bata son yawan tambaya da bin ƙwaƙƙwafi akan personal life ɗin ta, miƙewa tayi tana duban designer and fashionable wristwatch ɗin dake tsintisyar hannun ta

"We see some other times Deeq, will be having some lectures now".

"No am not letting you off until you gave me ur digits, kaɗan daga aikin ki ki ɓace min a garin nan".

Ƴar dariya tayi a gayance da ya bayyana wushiryar ta dake ƙara Maya kyau kafin ta shiga karanta Masa number ta Yana shigarwa wayar sa, hannu ta ɗaga masa bayan ya gama sawa ta wuce wajen su Meenah da zuwa lokacin su ma sun gama ita suke jira, Surayya ce ta ɗauka mata nata abincin da akayi packaging cikin wrapping paper me kyau duk da a cikin wani ƙayataccen takeaway take dan bata Sami cin abincin ba tana ta magana da Deeq.

Makarantar suka koma dan suna da lectures biyu kafin su tashi, kamar yadda ya zame mata halayya da É—abi'a wajen mai da hankali kan karatu yanzu ma haka tayi dan bata sake ko kallon su Hameedah ba se da suka fito daga theatre dan babu interval a jere ne lectures É—in, wani na fita wani na shiga.

Ƙarfe shida biyar saura suka fito, kowa ka kalla fuskar sa gajiya zaka karanto kwance kanta wanda su Kisnah na ɗaya daga cikin su, na lokacin ba abinda take buƙata se wanka dan wani irin danƙo da ƙaiƙayi take jin jikin ta na mata, haka yasa hannu kawai ta ɗagawa su Hameedah da suka ƙarasa wajen motocin su kafin ta shige tata ta fige ta a ɗari ta fice a makarantar.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta ƙarasa gida dan ba ƙaramin gudu ta ɗiba ba a titin, base nace komai ba kun dai san yadda tuƙin ta yake, bata tsaya bin yadda taji parlon nasu yau shiru ba hayaniyar kowa ba ta haure saman ta, tun a nata ƙaramin parlon ta fara cire kayan ta tana watsarwa har ta ƙarasa bedroom lokacin ba abinda ya rage a jikin ta ta faɗa toilet.

Sassauƙar ajiyar zuciya ta sauke bayan ruwan sanyin ya ratsa fatar jikin ta ya shige ƙashi da jinin jikin ta, tun tana yarinya Allah ya jarabe ta da son ruwan sanyi wajen yin wanka, ba ƙaramin sanyi za'a yi ba da zaka ga Kisnah ta yi wanka da ruwan ɗumi sedai ko ta gasa jikin ta da na zafi amma fa in ta fito se ta watsawa jikin ta na sanyin nan, abin a jinin ta yake shiyasa da yawan ruwan sama da ake yi yake ƙarewa a kanta dan da taga hadari zata canja kayan ta zuwa rigar wanka ko shimi iya cinya ta fita backyard ta fara wasa a ruwan har se anyi an ɗauke a kanta kafin ta koma ta canja kaya.

Shimi ta saka me ɗan tsayi da ta tsaya iya rabin cinyar ta ragowar kuwa na waje se ƙyalli fatar ta take yi tana ɗaukar ido, tun a kallon farko zaka san ba ƙaramin laushi da santsi zata yi ba shiyasa in ta saka kayan da basu rufe mata jiki ba zakaga maza na ta ƙure mata kallo suna tanɗar baki tun bare ma ƴan bariki da suka san sittin mata.

Parlon ƙasa ta sauka ta wuce kitchen inda ta sami Rayya tana girki cikin nutsuwa, gaishe ta tayi ta amsa a sake kamar yadda ta saba dan bata kasance cikin masu wulaƙanta ƴan aiki ba.

"Ya naji gidan shiru, ina mutanen gidan?".

A ladabce Rayya ta bata amsa
"Duk basa nan, É—azu Hajiya babba ta fita da trolley a hannu ita kuma Aunty maigado taje makaranta, yaya Awwaf kuma ........".

"Wannan surutu baki Rayya Allah ya yaye miki, kawai se kice min basa nan shikenan amsar tambaya ta, in Kuma na nemi ƙarin bayani se ki faɗa min ina suka je".

Dariya Rayya tayi
"Da ke kaÉ—ai nake surutun nawa ai Aunty Kisnah, Allah Baki na har ciwo yake yi na rashin magana a gidan nan".

"Toh Allah ya yaye miki, nidai yau a gajiya nake bare in biye Miki , zuba min abinci in tafi dan a gajiya nake".

"Amma gaskiya Aunty Kisnah wannan yaya Awwaf É—in É—an Air ne".

Rayya ta faÉ—a tana zuba mata fried spaghetti da tayi wadda taji kayan lambu sosai, zare kyawawan oily brownish eyes É—in ta masu kama da na mage Kisnah tayi

"FaÉ—a min me yayi miki ni Kisnah?".
Hankali tashe tayi maganar dan ita kan ta shaida ce Awwaf ƙwararren ɗan iska ne da bata fatan ace yayi wa Rayyan wani abu dan bazata so a ce a gidan ta aka ci mutuncin wata ba.

"Laah ba fa abin da yayi min kawai dai naji shi yana waya ne yana batsa".

Ajiyar zuciya Kisnah ta sauke
"Kome yake yi ba ruwan ki, ki kama kanki kin ji ko, bana san ko da wasa in ji wani abu ya haÉ—a ki dashi bayan gaisuwa, na faÉ—a miki".

"Insha Allah Aunty".

Karɓar abincin Kisnah tayi ta juya ta fita daga kitchen ɗin batare da ta kuma cewa Rayya komai ba,da ido Rayya ta raka bayan ta cikin kallon ƙauna, ba ita kaɗai ba duk ma'aikatan gidan haka suke san Kisnah dan bata da raina na ƙasa da ita, bata da wulƙanci balle rashin mutunci, barta dai da yawace yawacen ta, itace bata club, cinema, park, hotel da guest in, kullum tana da gurin zuwa dan bata fiye zaman gida ba se dai in tana da school wacce itace abu mafi muhimmanci a rayuwar Kisnah ɗin.

A duk yadda ake mata kallon karuwa ko Æ´ar iska har yau zuciyar Rayya ta kasa yarda da cewa hakan take, ita tana hango kamewa da mutuntaka a idanun Kisnah É—in da jama'a suka kasa gani, tana ji a zuciyar ta sunan karuwa be dace da Kisnah ba duk kuwa da ayyukan ta na zahiri sun tabbatar mata da sunan a idanun jama'a sedai ita har yau zuciyar ta takawa aminta da hakan.

Plate ɗin abincin ta ajiye kan carpet ɗin da ke tsakiyar ɗakin tare da zama ta ɗau spoon ɗin, shiru tayi cikin don tunawa da wani abu da tayi kafin fara cin abinci sedai ta kasa tunawa hakan yasa ta fara cin abincin ta cike da nutsuwa, sedai tayi kusan spoon uku sannan ta tuna da takeaway ɗin da Meenah ta saka mata cikin mota, ɗan taɓe baki tayi ta cigaba da cin na gaban ta , ko rabi ba tayi ba ta ajiye spoon ɗin tana nishi jin yadda cikin ta ya cika, mamaki sosai ya kama ni dan ba wani abinci bane na zai a gani gaba ɗayan sa, kun dai san yadda ƴan gayu keyin zubin abincin su wai amma a haka rabi kawai taci.

Seda ta É—an huta sannan ta jawo robar natural ginger drink dake ajiye gefen ta wanda ita take haÉ—a kayan ta ta zuba cikin fridge É—in É—akin ta saboda irin haka in taci abincin ta, sha tayi to her satisfaction sannan ta ajiye, laptop É—in ta ta jawo ta shiga bincike kan harkokin karatun ta wanda tayi zurfi a cikin sa sosai ya kuma É—auke ta lokaci me tsawo.
Chapter 9 · 0% Book details