← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 64

Sashe 43

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can ɓangaren Saraki kuwa be dawo gida ba seda akayi sallar Isha, wanka yayi ya canja kaya zuwa jallabiya mara nauyi ya zauna kan sofar ɗakin ya buɗe pack ɗin abincin sa na tun office dan shikam kasa ci yayi a can, gani yake kallon sa zata dinga yi.

Seda ya cika cikin sa ya kwashe ragowar ya saka a fridge sannan ya zauna zuwa lokacin da abincin ze faÉ—a masa, tunanin ta ne ya faÉ—o masa a lokacin

"Allah yasa tayi Sallar". Ya faɗa a fili dan yasan kaɗan daga ayyukan ta taƙi yi ɗin, wanda tayi ma takura mata yayi to wanna da baya nan kuwa ai se abinda Allah yayi kawai.

Murmushi yayi tuno dramar su a office ɗin yau, ya sani she's so simple compared to girls of her age Kuma masu kyau da dukiya irin nata, ya sani da wata ce baya jin de iya tanƙwara ta cikin sauƙi haka bayan shi ɗin ba komai ne gare ta ba se mere driver Wanda yake mata aiki take biyan shi haka kuma yasan Allah ne yaso ta da shiriya shiyasa ya sa ta zama mara girman kai balle wulaƙanci though yakan ga tayi wa wasu sedai yawanci ba talakawa bane masu kuɗi ne wanda ya fahimci kodai sun shiga gonar ta ko kuwa sun wulaƙanta kan su.

Kwanciya yayi tare da karanto addu'ar bacci ya shafe jikin sa kana ya lulluɓa yana rufe idanun sa a hankali hopping bacci ya ɗauke shi kar ya kuma shiga wata duniyar tunanin da yake ta hana kan shi faɗawa a kullum.

*******

"Wai Awwaf me kake nufi da zaman da kayi a wajen Æ´an iskan abokan ka bayan kasan ina jiran ka mu fara namu takun kan waccan Æ´ar iskar, in Kuma ka fasa ba zaka iya bane ka faÉ—a min in yi introducing wanda ze iya cikin tafiya ta".

Da sauri ya miƙe zaune yana hankaɗe matashiyar dake kwance kan sa, Muryar sa har tana rawa ya fara magana

"Haba Mommy wane irin bazan iya ba, kin kuwa san yadda nake burin mallakar yarinyar nan da har kike batun kawo wani, to wallahi bari kiji in kika yi hakan se na tona asirin kowa ya sani, gwara ma ki jira ni dan nan da kwana uku zamu dawo, ina dawowa kuwa ba ɗaga ƙafa zan yi ba dan nasan tun yanzu kun riga kun shirya yadda komai ze kasance".

"Are You threaten me?, Lallai har yanzu baka san wace uwar ka ba, ka wuce kwana ukun da kace ka gani in komai be faru ba, sedai kaji ana yi shashasha kawai".

Mommy ta katse wayar tana huci dan kalaman Awwaf ɗin na wai ze Tona asirin ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, zaman tayi a kan kujera tana jefar da wayar, da sauri ƙawar ta Jamila dake zaune ta cafe tana matsowa kusa da Mommyn

"Haba sadiya, meye abin fushi haka a maganar yaron nan, kin fa san su samarin nan in suka ga sun girma se haƙuri, kawai lallaɓa shi za muyi ya dawo dan plan ɗin se ya fi tafiya dashi dan nikam yanzu bana yadda da saka bare cikin aiki na kin san mutanen yanzu ba amana, kalli fa yadda yaron can Nuhu ya ci amanar Hajiya Talatu, yanzu gashi ta sanadin sa tayi biyu babu, shiyasa duk abin naka gwara shi ɗin dai, so ki kwantar da hankalin ki dan Ni nasa zamu yi Nasara, tabbas zamu lalata rayuwar Kisnah ni na faɗa miki".

Ajiyar zuciya Mommy ta sauke tare da wani zazzafan huci

"Duk yadda zan kwatanta miki yadda na tsani yarinyar nan Jamila ba lallai ki game ba, kin san dai yadda muka sha fama da rayuwa cikin talauci har Allah ya kashe iyayen ta muka dawo zama tare da ita cikin daula, ina faɗa miki yarinyar nan bata taɓa bari na na samu kwanciyar hankali ba tun ma tana yarinya har se da baban Maigado ya kai ta England karatu sannan na sami sauƙi muka sami damar rayuwa cikin jin daɗi da walwala muka huce duk wani haushin abubuwan da talauci ya sa mana a da, zan iya ce miki ban taɓa shiga cikin damuwar da na shiga ba shekaru huɗu baya zuwa yau wato dawowar yarinyar kenan, ban san wane irin banzan tunani ne ke damun baban Maigado ba amma saboda tsabar baƙin ciki yaƙi kai Maigado ƙasar waje karatu, ki ga dai yadda ita wannan ta yi kyau ta ƙaro aji ga wayewa shiyasa samari kamar ana mata wahayi dan ma ita bata saurarar su ita kuwa Maigado fa, duk da ta samu waye wa da aji amma ai ba kamar waccan ba haka kafin kiga saurayi ɗaya ya biyo Maigado da sunan aure wallahi se a fi watanni zuwa shekara, sedai an ayi rayuwa a ji daɗi sauƙi na ɗaya ita sam ba hakan a gaban ta amma da ya kike zaton tashin hankalin da zan shiga, yanzu fa ki kalla wai ta koma zuwa Companies ɗin ta zata dinga kula dasu manufar ta a hankali a hankali ta ƙwace komai nata dake hannun baban Maigado, ta yaya hankali na ze kwanta in har ban ga na Kai ta ƙasa ba fisabilillahi".

Sauke numfashi Jamila tayi tana gyara zama sosai tare da fuskantar Mommy

"Shiyasa nace miki da ki yarda Awwaf ya aure ta, a ganina ta haka ne kawai zamu sami nasara a kanta, kinga maganar Companies ko d ta ƙwace wa take dashi da zai kula mata dasu dole dai mijin t zata ɗora a kan komai  so kinga sun dawo hannun mu dai haka kuma ta nan ne kaɗai zaki sami damar musguna mata ki fanshe duk tarin tashin hankali da damuwar da ta jefa ki a ciki ko ba haka ba?".

Shiru Mommy tayi dan ita kam Allah ya sani bata jin zata taɓa yarda ta bar ɗan ta auren yarinyar da ta san karuwa ce, ita da take fatan samun tsarkakkun jikoki da sirika me mutunci se ta yadda a kwaso mata kaska, to amma kuma duk batun Jamila na akan hanya, bari dai zata yi tunani taga wanne ne fi mata in ya kama auren se ta haƙura amma fa se ta tabbatar ta hana ga haihuwa dan bata buƙatar zuri'a daga gare ta.

Juyowa tayi ta kalli ƙawar ta kuma ƴar uwar ta da ta zuba mata ido dan jin me ta yanke

"Kin kawo shawara me kyau dan haka zan yi tunani Jamila, kafin dawowar Awwaf zamu tsayar da batu É—aya".

Jinjina mata kai jamilar tayi ta reda sauke murya tayi mata raɗar da ta sa suka saki dariya tare da tafawa....................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

Ouummey 29 (8/21/2022 10:30 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                          Page 2️⃣9️⃣

_______________________📖 Yau ma Ka&S drinks suka nufa maimakon K&S Furnitures kamar yadda su kawu suka yi hasashe dan bata jin zata iya tafiya ta bar gurin nan a yadda yake sedai a maimakon su zauna duka su biyu se ya ajiye ta shi ya tafi construction company ɗin dan cikin zuwan da suka yiyyi tare ya fahimci yadda wajen yake tafiya se a bin da ba'a rasa ba.

Cikin farin ciki kawu ya ƙaraso cike da jin daɗin ze gabatar da aikin sa hankali kwance sedai lokaci ɗaya fara'ar nan ta ɓace ɓat lokacin da yayi ido biyu da Saraki zaune kan kujerar sa cikin office ɗin Kisnah.

Be sami zarafin cewa komai ba yaga Sarakin ya miƙe dan lokacin suke da meeting da wani Company da zasu basu kwangila, cikin ɓacin rai kawu ya juya gida dan ji yayi ma sam baze iya zama cikin Company ɗin ba.

Cikin kwanciyar hankali aka gama meeting ɗin komai ya tafi daidai, sedai a maimakon Saraki ya bari a saka rabin kuɗin aikin da aka yi da su zasu biya cikin account ɗin banki se ya bayar dana Kisnah dan haka kawai yake jin something is fishy a nan ɗin ma dan haka ya ɗau wannan matakin wajen daƙile koma meke shirin afkuwa.

Tana zaune tana aikin ta can a office ta ji ƙarar shigowar alert phone ɗin ta, ajiye aikin tayi tare da jawo wayar, mamaki ne ya cika ta ganin uwar kuɗin da ya shigo cikin account ɗin ta ko da ta duba sunan se ta ga sunan Company ɗin da suke batun karɓar kwangila wajen su ne, kenan hakan na nufin an daidaita shine suka yi half payment ko me, Yes haka ne ma, to amma me ze sa a saka kuɗin cikin account ɗin ta bayan akwai na Company?.

Shiru tayi tana jujjuya lamarin cikin ranta se dai ganin ta kasa ganewa se ta ajiye shi a gefe dan ta san dole Saraki ze mata bayani.

Tuno da sunan sa ya sa ta kalli wajen zaman sa cike da kewar sa tana tuno yadda suke wuni tare tayi ta masa surutu yaƙi kula ta in ma ta dame shi ya haɗe rai shikenan ya kashe bakin maganar se ta shiga taitayin ta.

Tuni yadda ta rungume shi da yadda yayi reacting se kawai ta tuntsire da dariya tai tayin abin ta ita kaÉ—ai kamar wadda ciwon hauka ya kama kafin tayi shiru ta cigaba da aikin ta tana sakin smiles kamar zararriya.

Hankali kwance ta cigaba da ayyukan ta tana me jin farin ciki cikin ranta.

A can ɓangaren Saraki shima aikin can ya cigaba da dubawa yana tabbatar da kasancewar komai a muhallin sa.

Kawu kuwa da baƙin ciki ya cika wa rai yana komawa gida number Alh Haladu ya kira telling him all that happened, shima sosai ran sa ya ɓaci ganin yadda yarinya ƙarama take neman wahalar dasu tun bare ma shigowar wannan ɗan iskan yaron cikin rayuwar ta kamar an ƙara mata ƙwarin gwiwa ne.
Chapter 43 · 0% Book details