← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 64

Sashe 4

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin tafarfasa zuciyar ta ta fara a ƙirjin ta, inda sun mata magana cikin mutuntaka ita me basu haƙuri ce dan bata da wannan girman kan, sedai yanzu da suka biyo mata ta wannan hanyar zata gwada musu ainahin wacece Kisnah.

Sam be lura da intention ɗin ta ba se ƙarar marin da ya karaɗe gurin se ko raɗaɗin da ya ratsa kwanyar sa, kafin a ankara ta saukewa ɗayan ma nasa a kuncin sa, zaro idanu Hameedah tayi yayinda Meenah tayi hanzarin riƙe ta ganin tana aniyar ƙara marin wanda aka kira da Haroon, fincikewa tayi ta ƙarasa gaban ɗayan tana nuna shi da yatsa tace "inga uban da ya tsaya maka yau a garin nan in Kai ɗan halak ne".

Juyawa tayi da nufin wucewa ragowar biyun suka sha gabanta fuska a haÉ—e duk da cikin ransu fargaba ce cike dan basu san wane É—iban albarkar zata yi musu ba su kuma.

Kamar wanda ya fita daga shock haka yayi firgigit yana kallon ta cikin tsantsar takaici da baƙin ciki
"Lallai yau se na yi maganin ki, se n ga uban da ya tsaya miki a garin nan".
Ya faÉ—a yana zaro dalleliyar wayar sa yayi danne danne na Æ´an sakanni kana ya sa a kunnen sa.

"Ina buƙatar motar ƴan sanda biyu yanzun nan ciki har da mata, ina parking lot ɗin clear screen cinema".

Gyara tsayuwa Kisnah tayi tana sakin murmushi yayinda ragowar matasan biyu suke kwarzanta wanda yayi kiran
"Gaskiya Abeed ka nuna wa yarinyar nan ko waye kai in ba Haka ba ai ƙimar mu ta zube, ace har mace ta samu guts ɗin ɗaga hannu ta mareka, gaskiya this is so disgusting".

Hura hanci kawai Abeed yake Yana aiyana abinda ze sa ayi mata a police station ɗin dan se ya sa an wulaƙan ta ta, jinginewa tayi jikin wata mota dake bayan tata ta maƙala airpeace a kunnen ta tana maming waƙar guzarish tana gyaɗa kai, su Surayya da suka san ba abinda aka isa ai mata su ma hankali kwance suka jijjingina da motocin su suna pressing phones ɗin su.

Jiniyar motar ƴan sanda ce ta cika wajen yayinda suka ƙaraso har inda Abeed ya faɗa musu, kashe motar suka yi sannan ragowar suka fiffito.

Da hannu Abeed ya nuna inda take tsaya yana haÉ—e fuska irin ba wasa É—in nan
"Arrest her know". Ya faÉ—a cikin sigar bada umarni.

Da hanzari ƴan sanda biyu mata suka ƙara sa inda take har lokacin idanun ta a lumshe, buɗe idon ta tayi jin an riƙe mata hannu ana ƙoƙarin ɗaura mata abu, cikin zafin rai ta janye hannun tareda wanke ta da zazzafan marin da seda tayi baya kamar zata faɗi, gani take tunda tazo duniya ba'a taɓa yi mata tozarci irin na yau ba.

Da sauri É—ayar ta tare Æ´ar uwar ta tana wurgawa Kisnah wani mugun kallo, bata ko kalle ta ba ta janyo wayar ta daga purse a fusace ta Fara dannawa, cikin tsiwa da rashin kunya ta ke magana tana wawwatsa hannaye

"Har ni jami'an ku zasu zo suce zasu kama, waye su, eye nace waye su, waya tsaya musu, to wallahi se sun san sun taɓa ni, kuma ina buƙatar ganin ka yazun nan in ba Haka ba kasan sauran".

Kashe wayar tayi tana huci yayinda jami'an suka sha jinin jikin su, kallon kallo suka tsaya yi a tsakanin su da alama communicating suke ta hakan, tsayuwa suka gyara dan babban su yace su tsaya su gani, maybe ma duk kurari ne kawai.

"Shigowar motar ASP ne ya sa gaba É—aya Æ´an sandan zaro ido, basu kaÉ—ai ba har su Abeed sun sha jinin jikin su da ita dan su kansu sun zata irin pretending É—in nan ne se ga ASP a gaban su.

Tura hular kanta tayi baya shedar zata yi rashin mutunci, kallon uku saura kwata tayiwa ASP kana ta nuna matan nan biyu
"A basu suspension ɗin wata ɗaya, su kuma waɗannan a tafi da su har se na neme su, mind you wallahi aka sake a ka bada belin su without my consent se rai ya ɓaci". Ta ƙarashe tana nuna su Abeed, ba tare da ɓata lokaci ba ASP yasa ragowar ƴan sandan suka riƙo su Abeed aka danna su a mota su ma matan ƴan sandan suka shiga da kansu.

Dogon tsaki taja ta buɗe motar ta ta shiga ta tayar, batare da ta kula ko ɗaya daga cikin ƙawayen nata ba tayi wa motar key ta fice a 360, girgiza kai kawai Meenah tayi tana fatan Allah ya kai ta gida lafiya dan a yadda ranta ya ɓacin nan ta san yau gudun da zata sheƙa ba na hankali bane, sallama sukayi kowacce ta shiga motar ta ta ɗau hanyar gidan su, dama tafiyar ta suke jira dan ba wadda ta isa ta tafi ta barta sedai ita ta tafi ta barsu.

Zagi ne tashi shi har ba adadi dan da yana fitowa a jiki to fa yau da ba zata sake ganuwa ba, wani shegen parking ɗin ganganci tayi ta fice daga motar ko samun arziƙin rufewa batayi ba, daidai ƙofar da zata shiga parlor taji an bangaje ta, ɗagowar da zata yi sukai ido huɗu da Maigado, bata jira komai ba ta sauke mata nata marin a kuncin ta kafin ta ja tsaki ta wuce tana tsartar da yawu, sakarere Maigado tayi da hannu a kunci kafin ta bi ta ciki a fusace, fizgota tayi tana daidai zata fara hawa matattakala, riƙe hannun Maigado tayi wanda ta ɗaga da  sunan marin ta ta murɗe shi har se da ta fara ihu kuma taƙi saki, ihun Maigado ɗin ne ya fito da Mommy dake nata parlon da baƙi, kallon kallo suka yi kafin Mommyn ta ƙaraso ta ƙwace hannun Maigado wanda ta saki ne kawai ba dan Mommyn ta ƙwata ta ƙarfi ba.

Nuna Mommy take da yatsa cikin nuna gargÉ—i tana faÉ—in
"Ki jawa ƴar ki kunne kiyi mata gargaɗi, hawainiyar ta ta kiyayi rama ta wallahi, in ba haka ba wataran se na karya ta a gidan nan, in ta ƙaryata kuma kar ta fasa in har ta haifu cikin uwar ta wato ke".

Tana gama faɗa abin da ke ranta ta hayewar ta sama cikin tafiyar gudu gudu sauri sauri, key ta sa ta buɗe ƙofar ta shiga parlon tare da maida ƙofa ta rufe.

Haɗaɗden falo ne da yaji kayan ado na zamani masu matuƙar tsada da kyau wanda samun irin su se gidan wane da wane, tun a nan ta fara cire kayan jikin ta tana watsar wa, kafin ta shiga bedroom saura pant da bra kawa a jikin ta, toilet ta wuce ta shige cikin jacuzzi tana kunna tap ɗin ruwan sanyi.

Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ruwan ya fara sauka a jikin ta, haka ta kasance cikin cold water for at least 30 minutes kafin taji ga dawo daidai ta buÉ—e rariya ya fita, fita tayi daga jacuzzin kana tai diluting hot water with cold one daidai yadda take so ta shiga ta fara wankan ta.

Towel ta ɗaura ɗan guntu da beko gama sauka ƙasan kwankwason ta ba ta fita daga toilet ɗin, wardrobe ɗin ta ta buɗe dan duba kayan da zata saka, cike damƙan wardrobe ɗin take da kaya kamar za'a buɗe shago, sutturu ne gasu nan kamar zasuyi magana kama da ga kan atamfa, lace, shadda, abayas se ƙananan kaya wanda sune sukai dominating.

Tsaki taja dan ta rasa wane ma kayan zata saka, kan gado ta faɗa ta ja bargo rabin jikin ta ta rufe ido, bacci take ji kamar me, sauƙin ta ma yau bata da lectures shiyasa zata yi abin ta ta more.

Kamar wadda akayi wa magana ta tashi da sauri zuwa jikin wasu drowers dake jikin bango, ɗaya dag ciki ta jawo slowly, hannu ta ɗora kan photo album ɗin dake ciki kafin ta jawo shi a hankali cike da takatsantsan dan bata buƙatar abinda ze taɓa mata shi balle har ya yage.

Zama tayi bakin gadon ta buɗe shi a hankali tana yi tana shafawa, photo ne ya bayyana a shafin Farko na album ɗin, hoton wasu kyawawan couple da kallo ɗaya za'a yi musu a tabbatar da tsananin ƙauna da soyayyar dake tsakanin su, ƙurawa hoton ido tayi tana kallo cikin wani irin maɗaukakin shauƙi da ya kasa ɓoyuwa kan fuskar ta, hannu ta ɗora daidai saitin fuskar macen ta shafa haɗi da lumshe kyawawan idanun ta, tsawon mintuna kafin ta buɗe idanun ta janye hannun ta ta maida fuskar namijin yayinda idanun ta suka cika da hawaye, shafa fuskar take cikin kewa da son kusan ci sedai hakan ba me samuwa bane.

Next page ta buɗe wanda ke ɗauke da hoton same couple sedai wannan karon hannun su riƙe yake da jaririya nannaɗe cikin showel me tsananin kyau da ɗaukar hankali dan an masa ado ne irin na yara a jiki, ko daga idanu kasan ze yi tsananin taushi, fuskokin ma'auratan ɗauke da kyakkyawan murmushi da ya ƙara musu kyau duk da duk cikin su ba baya wajen kyan.

Hawayen da ya zubo daga idon ta yasa ta maza ta rufe album ɗin tareda janye shi dan bata so ya ɗiga akai balle ya ɓata shi, maida shi tayi wajen ajiyar sa kana ta dawo kan gadon ta kwanta, ɗaga pillown ta tayi ta janyo wani photo guda ɗaya wanda shima dai photon wannan couple ɗin ne ta rungume a ƙirjin ta kana ta kashe wutar ɗakin haɗi da lumshe idanun ta..........................✍️

©️ Ouummey 📚✍️

☑️ote,Comment andShare fisabilillah.

Ouummey 04 (7/30/2022 6:00 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                      Page 4️⃣
Chapter 4 · 0% Book details