← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 64

Sashe 5

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

__________________📖 ƙarfe huɗu da rabi sannan ta tashi daga baccin, miƙa tayi ta ɗan zauna for some minutes har ta ji tayi daidai sannan ta miƙe ta shiga toilet. Wanka tayi sannan ta ɗauro alwala ta fito, zama tayi kan madubi ta lailaye jikin ta da mayukan shafawan ta masu matuƙar tsada da suke tashin ƙamshi kamar wani turare, busar da gashinta tayi tayi oiling ɗin sa ta parking ɗin shi in a crazy style.

Kwalliya ta zauna ta tsara a fuskar ta kamar me shirin zuwa zaɓen sarauniyar kyau na duniya, though nude make up ne amma ba ƙaramin haɗuwa tayi ba, gajeran wando ta saka wanda ya tsaya iya cinyar ta se ƴar shimi me siraran hannuwa biyu a each kafaɗa, band kalar wandon ta saka a kanta tareda sake yiwa jikin ta ɓarin turarurruka masu ƙamshi sosai.

Jikin wardrobe É—in ta koma ta buÉ—e wani side ta Ciro dogon hijab Wanda take sallah da shi ta zura kana ta koma inda praymat É—in ta yake ta tada sallah.
Shaf shaf tayi sallar ta idar da Azahar, without any azkar ta Kuma miƙewa ta tada sallan la'asar shima nan da nan ta idar, gaba ɗaya raka'a takwas ɗin a mintunan da basu fi huɗu ba tayi ta idar.

Cire hijab ɗin tayi ta saka wani flat shoe me matuƙar taushi ta buɗe ɗakin ta fita, ta ƙofar bayan dake jikin stairs ɗin nata ta fice zuwa garden, Zama tayi cikin ɗaya daga cikin kujerun da suka ƙawata kyakkyawan gurin da yake da matuƙar kyau da ɗaukar hankali duba da yadda korayen flowers da ciyayi suka lulluɓe shi, gefe ɗaya kuma swimming pool ne me ɗan girma ruwan cikin sa tsaftatacce dan ana iya hango ƙasan pool ɗin.
Gefen hagu kuma bishiyu ne da sukai girma na ban sha'awa, bishiyar guava, bishiyar ayaba, bishiyar mango and some other kinds of fruits.
Airpeace ta saka a kunnen ta ta lumshe idanunta tayi tana sauraren waƙar ta cike da jin daɗi da nishaɗi, a duk lokacin da take buƙatar kaɗaici nan ne wajen zaman ta, ta ji waƙar ta in ta Kai Mata ta taka rawar ta.
Se kusan ƙarfe bakwai ta bar wajen dan har an ɗan jima da idar da sallar magrib, wannan karon ta cikin main parlor ta ratso ta wuce su Mommy zaune suna hira ita da ƴaƴan ta, wani banzan kallo Maigado tabi ta dashi haka ma Mommy banda Awwaf da ya bita da kallon ƙurilla kamar ya cinye ta ɗaya.

Bata dubi ko ɗaya daga cikin su ba ta haye stairs ɗin ta tana yi tana moving jikinta towards each sound na waƙar.
Sauke ajiyar zuciya Awwaf yayi ya dubi mahaifiyarsa, haɗa ido suka yi tana jefa masa kallon gargaɗi, shafa kansa yayi ya ɗan zame zuwa kishingiɗa, hannun Mommyn ya riƙo yana marairaice murya

"Mommy I can't take my eyes off this beautiful creature, pls ki bar ni na aure ta mana".

Wani irin fisge hannun ta Mommy tayi tana watsa masa wulaƙantaccen kallo sedai kafin ma ta buɗe baki tuni Maigado ta riga ta
"Over my dead body, yanzu kai yaya da bakin ka kake faɗar zaka auri wannan karuwar? Are You in your right sense or yau ɗin ma kaje kasha kayi tatul ne, duk wulaƙanci da rashin mutuncin da take mana baka gani ba kake batun aurar ta? what came over you ne? Ko da yake ba abin mamaki bane zaka iya fiye da haka ma zakayi tunda ba uban mu ɗaya ba ai dole se ka nuna mana wannan bambancin".

Zaburowa yayi ze dake ta Mommy ta riƙe shi tana hararar shi kamar idanun ta zasu faɗo
"You stupid boy, har ni zaka kalli fuskata kace zaka auri maƙiyar da bani da sama da ita? Eye, ko da yake gaba ɗaya zantukan Maigado akan daidai suke , zaka iya fiye da haka tunda ka zama son of that worthless bitch, lemme tell you something, wallahi ko da wasa na kuma Jin that bitter sentence from your mouth se na saɓa maka ta yadda baka taɓa tunanin zan iya ba, stupid being kawai".

Komawa yayi ya zauna yana me dafe kansa kafin kuma ya buÉ—e su yana kallon ta
"Naji na bar maganar auren ta, but sincerely speaking I can't take my eyes off her, dan haka I'll follow ko ma wace irin hanya ce in same ta dan I have passion in her".

Washe baki Mommy da Maigado sukayi, Mommy ta dafa shoulder É—in sa
"That's my son, se yanzu naji daɗi, nima ban ce ka ƙyale ta ba, ka bi kowace hanya ka biya buƙatar ka akan ta zan tsaya maka, in fact ma Sena fi kowa farin ciki da murna saboda rayuwar ta ta lalace".

Murmushi ya sake jin yadda Mommy ke goyon bayansa tareda ƙara masa ƙarin gwiwa, sosai yaji yana zumuɗin samun damar aiwatar da ƙudurin sa dan yasan ko ta wace hanya Mommy bazata taɓa bari a gano shine ba, haka suka cigaba da tsare tsaren su na abubuwan da zasu yi wa Kisnah su huce takaici da baƙin cikin da take ƙunsa musu.

Baiwar Allah ita tana can ɗakin ta kwance a gado bayan ta idar da sallar magrib, chatting suke yi da su Hameedah suna bata haƙuri kan abinda ya faru ɗazu ta bada umarnin a sake su Abeed ita kuwa ta kafe tace bata san zance ba, dole a wulaƙanta mata su dan bazata yarda su tafi Scot free ba.

Kashe datan tayi ganin tara yayi, a ƙa'ida tara take bacci in har bata da party ko club ɗin zuwa, wanda tuni ta ware ranakun juma'a, asabar da Lahadi as clubbing days ɗin ta.
Miƙewa tayi cikin shigar kayan baccin da tai wadda ƴar guntuwar riga ce da ta tsaya can saman cinyoyinta, ƙaramin hannu gare rigar masu kama da na brazier, flat bedroom slippers ɗin ta masu taushi ta zura ta fita daga falon gaba ɗaya zuwa ɗakin kawun ta mijin Mommy a Haka batareda ta nemi abin suturce jikin ta ba.

Gaba gaɗi ta murɗa ƙofar ɗakin fa shiga parlon nasa without any permission or sallama, Mommy kaɗai ta tarar zaune kan one of the cushions na ɗakij tana danne danne a waya, zagaye falon tayi da idanun ta amma bata ganshi ba which means Yana bedroom, hanyar bedroom ɗin ta nufa ta buɗe ta shige bata kula kiran da Mommyn take mata ba kan ta jira ya fito.

Sanye da jallabiya yana tsane ruwan kansa ta same shi, zama tayi gefen gadon sa shikuma yana gaban mirror sedai tun shigowar ta ya ajiye towel É—in ya dawo gefen ta shima ya zauna.
Wani irin kallo yake ƙare mata ta gefen ido yayinda ita sam bata san yanayi ba dan abinda ya kawo ta ta shiga faɗa batareda ta gaishe shi ba dan tuni ta yaye gaisar da mutanen gidan.

"Nace matar can ta faɗa maka ina buƙatar 2 million urgently Amma sedai har yanzu ban ji alert ba, me hakan yake nufi?
Washe baki Kawu yayi duk kuwa da cewa zancen ta ba ƙaramin ɗaci yayi masa ba a zuciya

"Kuɗin Company ne yayi ƙasa ƴar Kawu shiyasa kika ga ban turo ba akan ta faɗa min, dama ina jiran gobe tayi ne se in turo Miki ko 1 million ne tunda ba 2 million a ƙasa".

Wani banzan kallo take bin Kawu dashi tun lokacin da ya fara magana har ya gama kafin cikin tsiwa da rainin hankali ta fara nata faÉ—an

"Bangane kuɗin Company yayi ƙasa ba, wai Kawu me kake da kuɗin nan ne da duk sanda zan yi maganar kuɗi seka kawo min wani banzan uzuri, wait, wane Company ɗin ne kuɗin sa yayi ƙasa, specify Ina jinka tunda dai kasan ai companies ɗin da yawa".

HaÉ—iye wani yawu Kawu yayi yana É—an inda inda
"Ehm dama, dama , ehm dama Company ɗin flour ne amma ba ma wani ƙasa yayi sosai ba kawai dai na faɗa ne dan naga karɓar kuɗin da kike yayi yawa".

Wata muguwar harara ta watsa masa kana ta miƙe tana riƙe ƙugu
"Excuse me dattijo, the last I checked dai kuɗin bana wani ƙaton banza bane nawa ne ko? Ko kuwa kun haɗa ƙarfi da Abbu lokacin neman su da tara su ne ban sani ba?, bana son wani banzan excuse, dukiya dai ta wace , wakilci na baka to meye zaka ringa wani son nuna min gadara da iko, okay nagane duk laifi nane amma xan gyara, a tattara min bayanan shiga da ficen kuɗin kowane Company da nake dasu, ɗaiɗai har biyar , dole in canja wakilai dan nagaji da wannan baƙin halin naka, and mind you, kafin in ahiga ɗaki kayi min transferring ɗin 2 million ɗin da nace".

Ficewa tayi tana banging Masa ƙofar, dafe kai Kawu yayi cikin tsantsar takaici da ɓacin rai ganin yadda ƴar cikinsa take kallon idanun sa tana faɗa masa maganganu, har shi take kira da ƙaton banza batareda tayi la'akari da alaƙa da matsayin da yake dashi a wajen mahaifin ta ba, ƙwafa yayi yana miƙewa tsaye dan ƙarasa shirin bacci daidai shigowar Mommy, wata banzan kallo Kawu yayi wa Mommy Yana nuna mata ƙofa da hannun sa alamar ta fice masa daga ɗaki, turus Mommy tayi kafin ta buɗe baki zatai magana sedai rikitacciyar tsawar da Kawu ya daka mata yasa ta juya ta fice da sauri a ranta tana tsinewa Kisnah dan duk ta ji abinda take faɗa kafin ta fice.

Dogon tsaki Kawu yaja yana hararar ƙofar kamar Mommyn na gurin har lokacin.

Ita kuwa Kisnah tana shiga ɗakin ta wayar ta ta fara jawowa ta kunna, pop up ɗin message dake yawo kan screen ɗin ta ta danna, kyakkyawan murmushi ta saki akan fuskar ta da ya kuma ƙara mata kyau ganin 2 million ɗin da tace har ya shigo, ƙwafa tayi tana jijjiga kai dan fa dole ta canja Kawu a kan dukiyar ta tunda har yan da guts ɗin cewa karɓar kuɗin ta yayi yawa kamar wani gadon sa.
Chapter 5 · 0% Book details