← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 64

Sashe 6

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiye wayar tayi ta koma tayi locking ɗakin sannan ta dawo ta kwanta, a maimakon addu'ar bacci se airpeace ɗin ta tajawo ta maƙala a kunnen ta bayan ta saita wani indian remix me awa huɗu, hoton ta ta jawo daga ƙarƙashin pillow ta rungume a ƙirjin ta ta rufe idanun ta, within seconds bacci yayi gaba da ita.

*************

Tsaye yayi gaban madaidaicin mirror ɗin da ya siyo dan gyaran fuskar sa, dubu da ɗari biyar ya siye shi dan yana da ɗan girma, towel ne ɗaure a ƙugunsa yayinda yake taje sumar kansa cikin nutsuwa bakin sa na motsi alamar yana karanta wani abu ne.
Oiling gashin yayi bayan ya tsaneshi tas da towel, tunanin yadda ze siyi hand dryer yake yi sedai kuɗin hannun sa gaba ɗaya dubu ɗaya da ɗari biyu suka rage, ajiye comb ɗin  hannun sa yayi bayan ya taje shi to his satisfaction ya fara shafa mai a jikin sa, ɗaya daga cikin set ɗin ƙananan kayan da ya siyo ya ciro ya saka bayan ya saka undies, sosai kayan suka karɓe shi kamar dan shi aka yi su, perfumes ɗin sa ya ɗauka ya feffesa a jikin sa kana ya ajiye, gyara ɗakin yayi dan tun kafin yai wanka ya wanke toilet ɗin, seda ya gyara komai sannan ya share, plate, spoon and bowl ɗin da yaci abinci jiya da dare.

Tsane hannun sa yayi bayan ya gama ya ajiye su mazaunin da yai musu a É—akin ya fita tareda rufe É—akin.
Wajen me communication ɗin gaba da su kaɗan yaje ya karɓi waya ya kira Idriss kan gashi fa ya gama shiryawa har ya fito, amsa masa Idriss yayi da gashi nan ƙarasowa, kashe wayar yayi ya bawa me communication ɗin tareda kuɗin kiran da yayi Naira hamsin.
Nan wajen ya tsaya jiran Idriss ɗin har ya ƙara so, musabaha sukayi tareda tambayar lafiyar juna kana ya hau machine ɗin Idriss ɗin suka shiga cikin kasuwa inda za'a nema masa aikin da ze dinga yi maimakon zaman banza tunda yace arziƙi yazo nema.................✍️

©️ Ouummey 📚✍️

☑️ote, comment and share fisabilillah.

Ouummey 05 (7/31/2022 4:13 PM)

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                      Page 5️⃣

__________________📖 Sosai suka zagaya cikin kasuwar suka shisshiga shaguna da yawa inda Idris yake zantawa dasu har Azahar tayi, tsayawa Idris yayi wajen wata me abinci ya siya yayinda Saraki yace a ƙoshe yake.
Sallah suka yi bayan Idris ya gama, juyowa yayi ya dubi Saraki bayan sun idar da Sallah

"Me kake gani game da ayyukan da muka tuntuɓa? Munje shaguna da dama dakai, shagon kayan masarufi, kayan sawa, kanti nan sai da takalma da kuma aikin shara a Company, wanne kake ganin ka fi so yanzu muje in kaika dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe, kar mu zauna a cike gurbin da wasu".

Shiru Saraki yayi yana tunani yayinda zuciyar sa ta fi kwantawa da kasuwar takalma, buÉ—e bakin sa yayi cikin yanayin maganar sa a hankali kamar baya so

"I prefer shagon takalman".

Though Idris be fahimci abinda yace da turanci ba saboda be yi karatu ba amma ya jin takalmi a ƙarshe ya gane ya zaɓi shagon takalmin.

"To tashi muje in kaika su san da kai". Miƙewa suka yi suka fita daga masallacin tareda hawa machine ɗin suka shiga cikin sabon gari ƴan takalma, wani ƙaton shago suka tsaya, shiga suka yi yayinda Idris ya ƙarasa wajen ainahin me shagon suka tattauna na tsawon lokaci kafin suka yi musabaha ya dawo wajen Saraki, jan shi yayi suka fito waje

"Da a nan shagon nake, me shagon tsohon megida na ne, nasan shi mutumin kirki ne kuma adali, a iya sanin da nayi masa bashi da wata matsala, zaka ji daÉ—in zama dashi gwargwado, duk da ban daÉ—e tare da kai ba zan bada shaidar kai mutumin kirki ne, ina fatan tafiya tayi nisa tsakanin ku da me gida insha Allah zakuji daÉ—in juna, zaka fara aiki dasu yau, Allah ya bada Sa'a".

Motsa bakin sa yayi alamar Ameen, hannu yasa ya bubbuga kafaÉ—ar Idris tare da yi masa murmushi alamar godiya kafin ya juya ya koma cikin shagon, juya wa Idris yayi ya hau machine É—in sa yana girgiza kai, daga shekaranjiya zuwa yau ya gama fahimtar magana tana bawa Saraki wahala, sedai ya fahimci shi É—in mutum ne me kirki da sanin ya kamata in an fahimce shi, tashin machine É—in yayi ya wuce.

Zama Saraki yayi kan wani bench dake baki bakin shagon har zuwa la'asar da Alh Musa me shagon ya fito ya ganshi zaune, mamaki ne ya kamashi dan a tunanin sa ya shiga cikin ragowar yaran shagon suna hidimar su.
Sunkuyar da kai yayi ya gaishe da Alhajin ya amsa masa tareda cewa ya tashi su wuce masallaci.

Alwala yayi suka tafi masallacin, tambayoyi yake masa suna tafiya inda yake bashi amsa iya abinda ya tambaya har suka ƙarasa, sallah suka gabatar suka dawo shago, tara yaran shagon Alh Musa yayi ya gabatar musu da Saraki matsayin ɗaya daga cikin su tareda neman haɗin kansu.
Amsawa sukai yayinda suka dinga bawa Saraki hannu suna gaisawa ɗaya bayan ɗaya tareda sanar dashi sunan su, murmushi kawai yake musu har lokacin tashi yayi, Naira ɗari uku Alh Musa ya bashi as sallamar shi, karɓa yayi yana godiya cikin yanayin maganar sa can ƙasa.

Napep ya tare ya koma shagon sa, wanka yayi canja kaya ya ɗaura alwala sannan ya kulle shagon ya taka da ƙafa zuwa masallacin da ke gaba da su kaɗan.

Azkhar ya zauna ya cigaba da yi har lokacin sallah ya cika aka kira sallah ya bi jam'i, ko da aka idar be tafi ba nan ya zauna ya cigaba da karatun Alqur'ani har aka kira isha itama yayi cikin jam'i kafin ya fito.

Cikin tafiyar sa ta nutsuwa haɗi da ƙasaita ya koma ɗakin sa, indomie ya dafa saboda tafi sauri dan yunwa yake ji, wunin yau be ci komai ba tun tea ɗin da ya karya dashi.

Ko da ya gama ci tashi yayi ya fita ya rufe ɗakin ya fita strolling dan ya riga ya Saba duk dare se ya fita yayi exercise haka ma da safe, a hankali  yake bin gefe gefen titi yayinda ababen hawa ke ta tsuga gudun sa akan titi, be yi nisa sosai ba ya dawo dan ba sanin garin yayi sosai ba kar yaje ya shiga inda baze fito ba.

Addu'ar bacci yayi bayan ya rage kayan jikin sa dan baya bacci da kaya ko wane iri ne, boxers kawai ya bari ya ja blanket ya rufe rabin jikin sa bayan ya ƙure gudun fanka kasancewar sa me matuƙar san sanyi.

****************

Sanye da dogon jeans ya bi fatar jikin ta ya kwanta ta sauko, rigar jikin ta buɗaɗɗiya ce da ta sauko har kan cinyar ta sedai ta ɗaure ta daga ƙasan ƙirjin ta da zaren da aka tanada, ƙafarta sanye da hill shoe kamar kullum hannunta ɗauke da wayoyinta biyu se makullin motar ta.

Abinci Maigado ke ci a dining tareda Awwaf, tana tawowa Maigado ta ja wani dogon tsaki tana hararar bayan ta wanda tana jinta amma tai mata banza, har takai ƙofar fita falon ta dawo zuwa kan dining taja kujerar gefen me gado ta zauna.

Ruwan Lipton dake cikin flask ta tsiyaya a cup ɗin gaban ta, ɗauka tayi kamar zata sha ta kai kusa da bakin ta kawai ta sake shi daidai ƙafar Maigadon, wani irin ihu Maigado ta tsala na tsananin azaba yayinda itama Kisnah ta taya ta, ihu take tun ƙarfin ta tana tsalle kai kace ita ruwan ya zubar wa.

Da gudu Mommy ta baro kujerar ta ta jawo Maigado jikin ta, har lokacin Kisnah bata bar ihu da tsalle ba daidai lokacin Kawu ya fito, ƙara ɓare baki tayi tana kallon Kawu tana yarfe hannu

"Wayyoooo Abbu na Nana ta, wayyo ƙafa ta zata cire, wayyoooo Allah Sena Rama".  Haka take ta ihu tana faɗa kamar gaske.

Da sauri Kawu ya ƙaraso ya tsugunna gaban ta,

"Menene ya sameki daughter, faÉ—a min me ya faru?

"Ba Maigado bace, daga kawai na zo zan fita shine tace min wai karuwa nikuma nace mata ai a wajen uwar ta na koya shine fa kawai ta ɗauko hot tea ta watsa min a ƙafa, da suka ga zaka fito se kawai ta zubawa ƙafar ta kaɗan wai dan kar ka yarda dani"

Wani irin zabura Kawu yayi ya juyo wajen su Maigado da suka saki baki suna kallon Kisnah dake matsar ido tana girba ƙarya.

Wani irin zazzafan mari kawu ya sauke wa Maigado, ai tuni ta manta da ciwon ƙafarta ta shige bayan Mommy tana ihu, binta kawu yake zai dake ta tana ƙara laɓewa bayan Mommy, garin Haka Mommy ta samu rabon mari, anje Marin Maigado ta tare aikuwa ya sauka a fuskar ta.

Wata irin dariya ce ke cin Kisnah amma ta daure ta haɗiye, seda ta tabbatar ƙafar Maigado tayi tsami saboda takata da take yi haka ma shikansa kawun ya gaji sannan ta kwaɓe fuska tace

"Kawu ka ƙyale ta kaje wajen aikin ka na haƙura amma gaskiya in ta ƙara sedai ta bar min gidana ita da uwar ta dan ita take zugata, rannan naji tana cewa wai a zuba min maganin ɓera a abinci".

Zaro ido Kawu yayi cikin tashin hankali zuciyar sa na bugawa, amma wallahi Haleema ba ƙaramar mara mutuncin mata ba ce, yanzu so take a kashe yarinyar tun kafin burin sa ya cika aikuwa zata ga iskanci

"Ai dama nasan duk abinda ke faruwa ita take shirya shi, saboda tsabar baki da mutunci kike cewa a kashe Æ´ar É—an uwa na da bani da kamar sa ko, to kije gidanku se na neme ki".
Chapter 6 · 0% Book details