← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 64

Sashe 2

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru sukayi yana kwance akan ƙafarta ita kuma tana shafa kansa har zuwa wani lokaci kafin ya buɗi baki

"Mami ki samin Albarka zan tafi, zan yi biyayya ga umarni da hukuncin me martaba duk da ban kasance mai laifi ba".

"Albarka ta na tare da kai a ko yaushe a kowane hali, ina mai maka nasiha da ka kasance mai gaskiya a duk inda ka kasance, ka gujewa haram duk daɗinta duk babunka, ka nemi halal ɗin ka ko da a wuta ake nema, ka gujewa zaluntar wani dan daka zalunta gwara a zalunceka, ina mai maka nasiha da kaji tsoron Allah ka kiyaye al'aurar ka daga datti da dauɗar zina, kar ka fara ko da hangar gonar da bata kasance mallakinka ba, ka kasance mai tausayin na ƙasa da kai kuma mai taimako da duk ƙanƙantar abinda kake dashi, ka guji zargi domin Annabinmu ya hane mu dashi a ƙarshe ina kuma tunasar da kai ka zama me gaskiya da riƙon Amana, ka kuma kasance mai yafiya, kuma ina so ka lura a duk inda zaka zauna dole zaka samu masoya da maƙiya, to kaso masoyanka ka kuma yi taka tsantsan da maƙiyanka domin ko anan su suka fitar da kai daga gadon ka kuma abin tunƙahon ka, ka girmama kanka kar ka yadda a wulaƙanta domin kai ɗin mai daraja ne, kasa a ranka ina matuƙar so da ƙaunar ka sosai saraki nah".

Goge mata hawayen da ke fuskarta yayi kana ya sake rungumarta kafin a hankali ya zare jikinsa ya sumbaci goshinta sannan ya miƙe ya fice.

Fashewa tayi da kuka dan tasan shikenan sallamar tasu sai kuma watarana in Allah ya ƙaddara saduwarsu in gaskiya tayi halinta......✍️

©️ Khairert

☑️ote
Comments
Share fisabilillah

Ouummey 02 (7/28/2022 3:05 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

                     Page 2️⃣

_________________📖 Tafiya yake a nutse cikin kwanciyar hankali kai baka ce yana cikin damuwa ba alhalin a lokacin inda za'a bincika zuciyar sa to fa sai an tadda ta tafi gawayi baƙi saboda baƙin cikin sharrin da akai masa.

Duk yadda ya tsani kallo yau dole ya haƙura ya kau da kai domin kuwa ya san sai an kalle shin dan yau yasan sharrin da akayi masa ke trending a garin nasu. Tuno da facemarks ɗin da ke cikin aljihun wandan sa yasa ya saki ajiyar zuciya kafin ya laluba ya ciro shi kana ya maƙala a fuskar sa.

Ta ƙofar baya ya fice daga gidan sarautar dan yasan ƴan jarida nacan cike a main ƙofar shikuma a halin da ake ciki bazai so yin magana dasu ba, bawai dan ba shida abun faɗar ba, a'a sai dan yin biyayya ga umarnin mahaifin sa.

Cikin takunsa na nutsuwa ya ƙarasa Save more Bank dake kusa da unguwar sarki wato unguwar su, ATM ɗin sa ya zaro wanda yake ɗan ajiye kuɗi aciki sa'i da lokaci dan lalura in ta taso, bai san nawa ne ainahin yawan kuɗin ciki ba shi dai kawai yana zubawa ne ashe zai masa amfani a rana irin ta yau.

Dubu Ashirin yai withdrawing kana ya tare ɗan acaɓa ya kai shi tasha sai dai in da matsalar take ba wasu garuruwa ya sani ba a ƙasar ta Hawarya dan kaso mafi yawa na rayuwar sa ba anan yayi ta ba.

Jin wani karen mota na ta maimaita sunan Garin Manya yasa kawai ya nufi motar dan haka kawai yaji sunan yayi masa kuma ya na san zuwa garin.

Kuɗin mota ya biya 10k dan Garin Manya yana arewacin ƙasar Hawarya ne yayin da Garin Giwa ke kudanci dan haka akwai tazara sosai tsakani.
Tafiyar kwana da wasu awanni ce ta kai su garin na Manya, garin da akewa kirari da "BABBA DA YARO KOWA DATTIJO NE, MANYA MASU HALIN MANYAN MUTANE DA MUTUNTAKA, HAWARYA IN BA MANYA KANGO CE!

Sosai Yarima Saraki ke yawatawa da idanunsa kusufi kusufi ganin yadda Garin yake a cike, kowa se sana'ar sa yake ba ruwan kowa da kowa in ba neman arziƙi ne ya haɗa ba, masu dako, masu abinci , masu ruwa har ma da masu shayi duk acikin tashar.

Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin ina zai nufa dan ba inda ya sani a wannan garin, hasalima bai taɓa jin ko sunan ba sai ko yau balle ayi batun zuwa.

Driver ɗin motar da ya sauke su ne ya ganshi har lokacin ya na tsaye yayin da duk ragowar fasinjoji sunyi nasu wuri, bai masa magana ba sai da ya gama ƙare masa kallo tare da nazartar sa kana ya matsa kusa dashi.
Sallama yai masa suka gaisa bayan ya amsa, nan yake tambayar sa ina zashi yayinda take Saraki ya amsa masa da baisan inda zashi ba bashi da kowa a garin arziƙi ya zo nema.

Ƙare masa kallo driver ɗin yayi tun daga sama har ƙasa sai dai shi sam baiga alamar talauci ko wahala a jikin sa ba dan duk wahalar zaman motar da yasha bai hana sheƙi da ƙyallin da fatar sa keyi bayyana ba, sai dai banda haka ba wani kayane mai tsada a jikin sa ba, simple shirt and trousers ne wanda suka ɗan cukurkuɗe saboda zaman mota.

Gyaɗa kansa yayi bayan ya tabbatar wa da kansa insha Allah mutumin kirki ne dan sosai nutsuwa da hankali ke bayyana kansu a tattare dashi, wayar sa ya fito da ita daga aljihu tare da dialing number ƙanin sa ya Kira shi kan yazo yana neman sa.

Kallon Saraki yayi yana masa bayanin ga ƙanin sa nan zai zo ya rakashi inda zai sami wajen zama na haya in Yana so tare da ɗan aikin da baze gagara ba dan dillali ne shi amma na kasuwa.
Cikin yabawa da karamcin mutumin Yarima Saraki yai masa godiya.

Cikin mintuna ƙalilan ƙanin driver ɗin ya ƙaraso, yaro ne matashi dan bai wuce sa'an Sarakin ba, gaisawa sukai kana ya'yansa yai masa bayani, cikin fara'a ya jagoranci Saraki zuwa jerin wasu shaguna dake bakin kasuwar durumi wadda itace babbar kasuwar garin, ya kawo shi nan ne dan yaji sauƙin fita neman kuɗin sa tun da yace arziƙi yazo nema.

Dubu Ashirin da biyar ya biya kuɗin hayar shekara na ɗakin kana idriss ƙanin driver ya rakashi cikin kasuwa dan ya siyo kayayyakin da ze buƙata na rayuwar yau da kullum.
Kayan shayi ya siyo masu ɗan auki, se kayan sawa jeans da t shirt set huɗu, jallabiya guda biyu, silifas guda biyu sai takalmin kwalliya mai ɗan kyau suma biyu, bucket madaidaita biyu sabulun wanka da klin kowanne biyar biyar, sabulu wanka ne ya ɗan so ya basu matsala dan shi da mai tsada ya saba amfani sai dai a wannan gaɓar dole ya karɓi sauyin rayuwar da ya zo masa kwatsahan batare da ya shirya ba, dudu osun idriss yai masa recommending dan haka ya siya kusan guda goma sha biyar, dan shi ɗin kamar kifi yake wajen son wanka, se kuma katifa da suka siya irin wadda ake ɗin kawa rigar nan bayan mutum ya siya, suka siyo net da ɗan ƙaramin carpet da zai wa ɗakin daidai, labulaye suka ɗin ko guda biyu na ƙofa da window se kuma akwati mai sauƙin kuɗi da turarurruka masu ɗan sauƙi suma, kayan abinci ya siya kaɗan kaɗan,macroni rabin carton, sphagetti ma haka, se mudun shinkafa uku se ko wake mudu ɗaya, Maggi Leda biyu, gishiri da kuma kayan spices, Mai kuwa nacikin jarka ya siya dan yace bai yarda da ingancin wannan ɗan ɗurin ba.

Kafin kace me kuɗin hannun sa sun ƙare wadda a banki ya tsaya ya ciri 100k sedai yanzu yan canjin da suka rage a ciki ƙalilan ne, dole ya ciro wasu idriss ya na nuna masa hanya suka siyo 4 plates da bowls guda biyu se spoon uku dan shi ɗin yana da tsantseni baze iya cin abinci da abubuwan siyar wa ba, mayukan gashi ya siya suma set hakan yasa kuɗin hannun sa suka sake yin ƙasa, padlock kawai ya siya suka koma shagon.

A jimillance da Idriss yai lissafi sun kashe kusan 200k da hawa, Idriss akwai kirki, shi ya taya Saraki gyara É—akin yana masa fira duk da shi Sarakin ba wani amsa masa yake ba se eh, a'a ko yai amfani da body language i.e jijjiga Kai ko gigizawa.

In a blinking of an eye har sun gama, sosai kuma ɗakin yayi kyau kamar bashi bane kangon ɗakin da baya ɗauke da komai sai tiles dake ƙasan ɗakin.
DaÉ—in É—akin É—aya Saraki yaji ganin cewa akwai toilet a ciki, dashi yayi amfani yai wanka bayan Idriss ya É—ebo masa ruwa cikin bucket a wani gidan wanka dake bayan su.

Se kusan ƙarfe 11pm Idriss yai masa sallama ya wuce bayan ɗumbin godiyar da ya sha wajen Saraki, basshi dai da miskilancin sa amma yasan Alkhairi, yana matuƙar daraja dukkan wanda yai masa Alkhairi komi ƙanƙantar sa haka kuma bai da girman kai wajen yin godiya in an kyautata masa.

Kwanciya yayi bayan ya canja kayan sa zuwa na bacci cikin kayan da ya siya, suratul mulk yake biyawa ƙasa ƙasa wadda bakin sa ke motsawa cikin alamun nuna karatun yake, cikin wannan yanayin bacci yai gaba dashi dan ba ƙaramin gajiya ke nuƙurƙusar sa ba duk kuwa da wankan da yayi.

******"
      
       *MILLIONAIRE'S QUARTERS, MANYA STATE, HAWARYA*

Unguwa ce ta riƙaƙƙun masu kuɗin da suka tara ya taru, cikakkun ƴan boko da kuma manya manyan jiga jigan siyasa.

Da wani irin ihu budurwar ke magana cikin tsakiyar parlon da ya haɗa ƙofofi uku se ko stairs ɗin da zata kai mutum zuwa wani ginin dake sama.

"Na rantse da Ubangiji wannan karon Bazan yarda ba, nakai maƙura da haƙuri da wulaƙaci da rashin mutunci wannan shegiyar yarinyar, Mommy...Mommy ki fito kizo kiji dan kar ma kice ban faɗa miki ba".
Chapter 2 · 0% Book details