← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 64

Sashe 15

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai hankalin Auntyn ya tashi dan wasan every blame ze koma kan ta ne in yayan Surayya yaji abinda ya faru, hakan yasa tuni ta manta da batun wulaƙanci ta roƙi Kisnah kar ta sanar da yaya gata nan zuwa, kashe wayar kawai Kisnah tayi ta ajiye ta maida idanun ta ta lumshe kamar dai yadda take a ɗazu.

Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sefa Auntyn ta ƙaraso, ba wanda ya kula ta a cikin su ta ƙarasa gaban gadon da Surayyan ke kwance, zare idanu tayi ganin har da ɗinki, cikin tashin hankali take tambayar su garin yaya hakan ya faru da ita, Leekha ce ta bata labarin komai kamar yadda Kisnah ta sanar dasu dan ko buɗe idanun ta ita Kisnah bata yi ba bare ta bawa Auntyn amsa, zage zage ta fara a ɗakin tana blaming Kisnah kan ita ke koyawa Surayya lalacewa Gashi nan ta sanadin ta daraja mata mutuwa, banza tayi wa Auntyn kamar bata jin ta har se da taji ta fara taɓo iyayen ta kafin ta buɗe idanun ta da suka canja kala daga attractive golden brown oily and sexy eyes zuwa brownish color so scary ga me kallon su, tsit Aunty tayi da bakin ta ganin mugun kallon da Kisnahn take binta dashi, duk iskancin ta tana shakkar yarinyar dan tasan ta fita iya shege da sanin malamar rashin mutunci shiyasa tana iya taka su Meedah amma bata taɓa kwatanta yi wa Kisnah ba se yau, yatsar ta manuniya ta ɗaga tana nunawa Aunty hanyar fita wato ta fice ta basu waje, jim tayi kamar bazata fita ba kafin taka uban tsaki tayi waje fuuuuu kamar zata tashi sama.

Haka suka ƙarasa wuni wajen Surayya har su Hameedah suka dawo, anan suke shaidawa Kisnah wanda yayi musu wannan aika aikan

"Kin tuna wani gaye da i think two months ago yazo wai yana son ki??

Yamutsa fuska Kisnah tayi cikin son tuno Wanda suke magana akai amma ta kasa, ko banza masu cewa suna son nata ai ba iya ƙirga su zata yi ba dan haka ta girgiza wa Meenah kai

"Wanda fa kika mara a club da ya rungume ki kina rawa".

Cikin sauri ta gyaɗa kai dan shi kaɗai ya taɓa mata haka kaf shekaru uku da tayi tana zuwa hideaway club

"To shine ashe ya sa miki drug acikin kunun ayar da kika ake da zaki rawa, he take advantage of us da bama hayyacin mu ya saka ita kuma Surayya dama kina tashi itama ta bi saurayin ta".

Shiru Kisnah tayi cikin tuƙuƙin ɓacin ran abinda yaso aikata mata jiya, wato dan ta mareshi shine bari ya yaga mata mutunci ko, aikuwa zata yi maganin sa.

"Yanzu me kuka ce ayi masa a station?". Leekha ta tambaya

Meedah ta bata amsa da
"Mun ce kar a sake a bada bail É—in shi ko uban waye yazo".

Jijjiga kai Kisnah tayi alamar hakan yayi kafin suka tarkata kowacce ta nufi gidan su dan ba'a kwana a asibitin dan suna da masu jinyar patients.

Ko da tayi parking ta daɗe Bata fito ba daga motar har se da taji kan ta dake ciwo ya ɗan tafi, tasan ba komai bane illa effect ɗin ƙwayar da yasa mata jiya wadda ita ke ta wahalar da ita dan ba ta taɓa sha ba, a hankali take takawa ba kamar yadda ta saba kullum ba sedai duk da haka cat walk ɗin nan dai take yi wanda haka asalin tafiyar ta yake.

Da sauri me bawa flowers ruws ya ƙarasa gaban ta ya ɗan durƙusa hakan yasa ta dakata da tafiyar da take yi ta duba shi

"Dama Inusa yace in sanar dake sun zo É—azu ba kya nan, in ba damuwa zasu dawo gobe shi da sabon driver É—in da aka samo".

Nodding kanta tayi kafin cikin rashin son magana saboda ciwon kanta tace

"Zan jira su by 9:30am".

Da hanzari ya amsa da ze faɗa musu insha Allah, bata ƙara jiran me zarce ba tayi gaba, a falo ta tadda kawu wanda wunin yau taga ya tsiro zaman falon su maimakon nasa da yake zama da, bata ko ce masa ƙala ba ta haura saman ta ta buɗe ta shige, bedroom ta wuce ta faɗa kan gado tana sakin nishin azaba kafin da ƙyar ta zare takalman ƙafar ta ta haye gaba ɗaya ta ja blanket saboda ɗan sanyi sanyin da taji yana shigar ta..........................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

*☑️Ote, comment and share fidabilillah*

Ouummey 11 (8/4/2022 4:14 PM)

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                          Page 1️⃣1️⃣

_______________________📖 Bargo ta tashi ta ɗauko da ƙyar ta ƙara kan blanket ɗin ta shige ciki.
Ranar ko kayan jikin ta bata iya canjawa zuwa na bacci ba ta kwanta dana jikin ta.

Sosai tayi bacci saboda ɗumin da ke ratsa jikin ta wanda bata farka ba se to nine, wanka ta shiga tayi ta saka Black straight English gown me ɗan gajeren hannu da ta tsaya iya ƙaurin ta, yau bata kama gashin da ribbon ko sa masa band ba ta sake shi a bayan ta bayan ta taje shi ta masa style me kyau.

Turarurrukan ta ta feffesa kafin ta jawo black designer wedge half cover shoe ta saka ta ɗebi wayoyin ta da system ɗin ta da key ta sauka falon ƙasa, kan two sitter sofa ta zauna tana zube wayoyin ta a gefen ta sannan ta jawo Centre table ta ɗora ƙafafun ta kana ta ɗora system ɗin kan laps ɗin ta ta shiga operating hankali kwance.

Maigado dake zaune kan dining ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba dan Allah ya sani ta tsani Kisnah beyond expectation, ba ƙaramin ɓacin rai da takaici take ji ba inta dubi gidan nan ta kuma tuno wai mailakin ta ne, yanzu haka da take zaune tana dai cin abincin ne dan bazata iya zama da yunwa ba amma gaba ɗaya tunanin ta yana kan yadda zata yi Mommy ta dawo gidan ne dan su fara planning yadda zasu ɗaiɗaita rayuwar Kisnahn da gaggawa, ga shima wancan banzan yaya Awwaf ɗin ya ɗau ƙafa ya bar gari wai birthday ɗin aboki.

Tsaki tayi ta dangwarar da cup É—in hannun ta ta wuce fuuuuu É—akin ta, sarai Kisnah ta jita sedai ko kallon ta bata yi ba dan ba itace a gaban ta ba, kacokan hankalin ta yana kan kuÉ—aÉ—en da spy É—in ta da ta ajiye a Companyn gine ginen ta me suna K&C (Kisnah constructions) ya turo mata an nema an rasa ba kuma batun wani bincike akai.

Kusan awa ɗaya tana latse latse a laptop ɗin kafin wayar ta da take amsa kiran ma'aikatan gidan ta hau ringing, bata ji kiran ba har se ana biyu dan gaba ɗaya hankalin ta ya tafi kan aikin da take yi, picking tayi dan ganin 0045 wato number me bawa flowers ruwa kasancewar kowane ma'aikaci yana da number base on ɓangaren da yake aiki, haka kuma an bashi phone and sim card Wanda in ya kira wannan number ce zata yi displaying, karawa tayi a kunnen ta tana sauraren bayanin da yake mata kafin ta amsa

"Su ƙaraso main falo shi da Inusan kai kuma ka koma bakin aikin ka".

Ajiye wayar tayi ta sake maida hankali kan system ɗin, tsurawa screen ɗin ido tayi ganin account details ɗin da kuɗin suka shiga bayan sun fita daga account ɗin Company, sosai ranta ya ɓaci dan wannan ne karo na kusan biyar da aka samu irin haka kuma duk ta bi diddigi wannan account ɗin dai take gani dan haka wannan karon bazata saurara ba se ta gano ainahin me shi.

Sallamar da suka yi kafin shigowa yasa ta ɗan ɗago ta kalli ƙofar kafin ta ɗauke idon ta maida screen ɗin, bata amsa sallamar ba dan hakan ba ya cikin tsarin ta, turo ƙofa Inusa yayi ya shigo yayinda Saraki ke bin sa a baya, ƙasa kan carpet Inusa ya nema ya zauna yayinda Saraki yake tsaye dan baya jin ze iya zama ƙasa wani na sama wanda ba mahaifan sa ba (Sarautar ta motsa😜😂).

Seda ta ɗan ɗauki lokaci bayan tayi saving komai sannan ta ɗago fuskar ta a sake ta dube su, da hanzari Inusa ya fara miƙa gaisuwa ta amsa fuskar ta da walwala har tana tambayar sa ya family ɗin shi da harkokin sa, amsawa yayi cikin jin daɗin yadda bata wulaƙanta su duk da sun kasance a ƙasan ta kafin ya nuna mata Saraki da bayanin shine sabon drive ɗin da aka samo mata.

Kallon ta ta maida inda Sarakin ke tsaye hannun sa cikin aljihu, idanu ta fara bin sa tun daga ƙasa kan kyakkyawar tsaftatacciyar ƙafar sa dake nan sumul kamar baya taka ta zuwa kayan jikin sa har ta kai fuskar sa sedai kallo ɗaya tayi wa fuskar tasa ta ɗauke kanta da sauri saboda wani irin kwarjini da cika ido da taga yayi mata.

Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye idanun ta na kan Inusa ta furta

"Have a seat please, za muyi magana".

Bece komai ba ya nemi one sitter sofa ya zauna yana iya ƙoƙarin sa na ganin be yi zaman da ya saba ba duk yakai zaune kan kujera wato harɗe ƙafafu kan juna, irin zaman da yayi kawai seda ya sake sata jin nauyi da ɗan shakka dan zama ne irin na cikakkun jinin sarautar da suka gawurta da isa, izza da taƙama dan ya buɗe gaba ɗaya ya cika kujerar,  wannan shine karo na farko da zata ɗauki drive batare da ta ƙare masa kallon tabbatar da tsaftar sa ba kamar yadda ta saba, shiyasa tunda bazata iya duban sa direct ba take satar kallon sa ta gefen ido.
Chapter 15 · 0% Book details