← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 64

Sashe 11

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban hall ne dake shaƙe da jama'a maza da mata, mostly samari da ƴan mata ne a ciki se kuwa tsirarun manyan mata da maza da tsufa yai wa gardama sukai faɗuwar baƙar tasa.

Ihu da sowa club ɗin ya ɗauka baka jin komai se kiran sunan Queen Kissy it's kuwa se murmushi take yi yalwatacce tana ɗaga hannun ta dake riƙe da key ɗin mota, ɗaya bayan ɗaya manyan yaran wajen suka ƙarasa suna rungume ta ba maza ba mata, da ƙyar suka ƙyale ta ta ƙarasa wajen su Meenah dake zaune a permanent VIP seat ɗin su, kujera Meenah ta ja mata ta zauna wanda itace permanent wajen zaman ta se Meenah a gefen daman ta, Hameedah a gefen hagun ta se Surayya da Maleeka a ragowar kujerun wajen da suka kasance biyar se wani haɗaɗɗen madaidaicin table a tsakiyar su.

Daga inda suke take kallon ƴan wajen kowa ke sabgar gaban sa gefe ɗaya kuwa ƙaton filin rawa ne da ƴan rawa kowanne na ƙoƙarin son ganin ya nuna tasa bajintar, a nan kan table ɗin su kuwa manyan kwalaben wine ne da Maleeka tayi ordering dan iya kam cikakkiyar mashayiyar giya ce, a rana se ta shanye kusan kwalba uku ko huɗu, a irin wannan ranakun kuwa da suka zo club kafin su tashi tana iya shan biyu, ita kuwa Meenah gaba ɗaya hankalin ta yana kan lemon coke da take jijjigawa dan ƙwayoyin da ta zuba su narke, ita bata shan giya amma tana shan ƙwaya, Hameedah kuwa shisha ce take zuƙa tana fesarwa cike da ƙwarewa se Surayya da ita kuma hankalin ta ke kan mazan wajen, ita bata shaye shaye ko kaɗan se dai akwai ta da son maza, gajeren tsaki Kisnah ta saki tana fincike robar coke ɗin dake hannun Meenah dan a ɗan zaman ta na mintina talatin wannan ce roba ta biyu da Meenahn zata shanye wadda ta shigo ta tarar da wata a hannun ta.

Cikin ɗan maye kaɗan da ƙwayar kan saka ta Meenah ta ɗago ta kalle ta, wata shegiyar harara Kisnahn ta wurga mata da ta saka ta komawa ta lafe cikin kujerar ta tana kumshe idanun ta dan tasan ma'anar hararar shine ta shanye iya kason ta na yau.

Miƙewa Kisnah tayi ta zare ƴar jacket ɗin jikin ta ta ajiye kan seat ɗin ta tare da wayoyin ta, gorar sassanyan kunun ayar ta ta buɗe ta ɗaɗɗaka har yai rabi kafin ta rufe ta ajiye ta fice daga VIP ɗin ta nufi wajen masu rawar.

A take duk masu rawar suka tsaya can kafin suka fara fita ya rage saura wasu uku, nan da nan aka canja kiɗan dake tashi wajen daga American songs zuwa Indian songs, wani irin kumshe idanun tayi tana jin kiɗan na ratsa ta kafin a hankali ta fara takawa ta kai tsakiyar mutum ukun, cikin wani irin salo ta fara kakkarya gaɓɓan jikin ta cikin salon waƙar tana malkwaɗe wa, banda ihu da sowa da tafi babu abinda ke tashi a wajen dan ko shakka babu tafi asalin jarumar da ta hau waƙar iyawa, haka ta dinga yin rawar waƙoƙi da dama kafin ta dakata tace a maida mata American songs ɗin, nan ma haka ta hau yi kai kace ba musulma nace balle ɗiyar hausawa kuma.

A nan ta ɓata lokaci har kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare kafin ta fita a wajen, liƙi kam ta sha shi, manyan yaran wajen sun yi ruwan kuɗi kamar a ƙasa ake samo su, daloli da saifa sunyi kuka se ko ƴan dubu dubu dan babu ƙasa da dubun, ko da ta fito kowa ba ta kalla ba duk da ɗumbin mazan dake ƙoƙarin son yi mata magana, maida jacket ɗin tayi jikin ta kana ta zauna kan kujerar ta bayan ta kwashe wayoyin ta da gorar kunun ta ta maida kan table cikin mamakin ina Surayya ta je, takaici ne ya kamata ganin yadda gaba ɗaya daga Meenah har Maleeka suka fita hayyacin su yayinda Hameedah ke ta sambatu cikin maye.

Kawar da kai tayi daga duban su ta buɗe goran kunun ayar ta ta kafa kai ta shanye dan sosai take buƙatar jiƙa maƙoshin ta, cillar da robar tayi sannan ta ja wayar ta ta hau latse latsen ta, tsawon lokaci kafin ta fara jin kan ta yana mata nauyi, jijjiga kan tayi cikin son dena jin komai ta cigaba da danna wayar ta, wani irin jiri jiri ta fara ji kafin ta fara ganin bibiyu uku uku, da sauri ta ajiye wayar tana dafa kanta da hannu ɗaya yayinda take mutstsika idon ta da ɗaya hannun.

Sedai maimakon ta dawo daidai se ma ƙaruwa da abin yake yi dan har gani take kamar gurin na tafiya, sama ta dawo ƙass, kamar dai tana yawo a cikin gajimare, tashi hankalin ta yayi dan duk iskancin ta bata shaye shaye, ba abun da ta tsana ma a rayuwar ta kamar giya, ƙwayar kuwa ko a asibiti aka bata bata sha duk tsananin da rashin lafiyar da take yi kuwa.

Kafin kace me ta rasa hankalin ta gaba É—aya da har ta faÉ—a kan table É—in gaban ta tana wasu irin surutai marasa kan gado gaba É—aya jikin ta ya saki idanun ta sun juye.

Daga can gefen wajen zaman su wasu samari ne da kallo ɗaya zaka musu kasan manyan yara ne saboda irin shigar dake jikin su, cike table ɗin gaban su yake da kayan shaye shaye, tukunyar shisha, ƙwayoyi, kwalaben maganin tari, cocain har ma da wasu da ban ko san su ba, su huɗu ne kowanne kuma da kalar kayan mayen da yake bankawa cikin sa banda ɗaya daga cikin su da yake danna waya yanayi yana duban Kisnah a kaikaice.

Wani irin shu'umin murmushi ya saki kafin ya dubi na gefen hagun sa yana miƙewa

"Ni na wuce, yau dai tarkon da na É—ana ya kama É—awisu".

Dariya duk suka sake na gefen damar da na faÉ—in

"Kai baaba yau zaka kwashi Gara yacin, ko dai nima nazo na É—ana ne in ka gama".

Wata shegiyar harara wanda aka kira da baaba ya sakar masa

"Ka jimin É—an iska, yau ina suhan É—in taka da har kake kiran in rage maka, to bari kaji till Dawn zan yi dan haka ma kar ku jira ni ku wuce kawai zamu haÉ—e gobe".

Sowa suka sa suna tafawa kafin ya musu sallama ya wuce, wajen su Kisnah ya ƙarasa lokacin tayi nisan da har bata gane waye a kanta, hannu yasa ya shafi fuskar ta yana kunshe ido saboda tsananin taushi da santsin fatar ta, wani irin lashe leɓe yayi da harshen sa cikin salon su na gogaggun ƴan guguwa kafin ya sa hannunsa biyu ya ɗauke ta kamar wata baby doll ya fice da ita daga wajen gaba ɗaya.

A tazame Surry dake wani ɗaki ita da saurayin ta suna romance ta fincike jikin ta ganin yadda yau wani namiji ya samu damar taɓa Kisnah har ma ya ɗauke ta a hannun sa, da azama ta fita daga ɗakin wadda dama basu rufe ƙofa ba, to rufewar me zasu yi bayan kowa iskancin sa yake a fili, ko kafin taje har ya saka Kisnah a mota yayi mata key, da gudu Surayya ta koma table ɗin su ta ɗau key ɗin motar ta ta fita itama, tana fitowa compound shikuma Yana fita da motar daga building ɗin, a gigice ta figi motar ta fice kafin masu gadi su gama rufe gate ɗin da ya fita.

Hannu ta kai zata yi accelerating motar se kuma ta fasa dan in yasan an biyo shi ze iya gudun da ze tsere mata dan ƙarfin hali ne kawai take yi amma jikin ta a mace yake da abinda saurayin ta ya gama yi mata.

Sannu a hankali take bin bayan motar har suka ƙarasa bakin kasuwar durumi in da ta tabbatar ko ihu tayi za'a iya jin ta saboda shagunan masu kwana dake kan titin, ƙara gudun motar tayi taje ta sha gaban shi har ƙiris ya rage bata daki gaban motar shi ba, ajiyar zuciya ya sauke jikin sa na ɓari dan da be yi saurin tsaida motar Ba da se sun daki wanda Allah kaɗai yasan me ze faru in da hakan ya kasance.

Ƙurewa motar gaban sa ido yayi cikin son gano waye ya sha gaban sa sedai be yi nasara ba kasancewar motar me baƙin gilashi, cikin motar kuwa hannu na rawa Surayya ta danna kiran jami'an tsaron da ke police station nan gaba dasu kaɗan dan ƙa'ida ne akwai police station gaban duk kasuwannin garin.

Cikin Sa'a bugu biyu wani ɗan sanda yai picking call ɗin ta sanar dashi me ke faruwa, take ya shaida mata hadu nan tafe, cikin ɓacin rai baaba wanda asalin sunan sa Sageer ne ya fito daga motar dan ganin wane ɗan rainin hankalin ne ya tare masa hanya, a fusace ya kaiwa glass ɗin motar Surry wani mahaukacin bugu, ganin fa in aka cigaba da haka se iya fasa glass ɗin kuma ya damƙe ta yasa hankalin Surry tashi dan kallo ɗaya zaka yi wa baaba Kasan gawurtaccen ɗan Air ne, tunanin da ya zo kan Surayya yasa da hanzarin tai unlocking motar kana ta buɗe murfin da dukkan ƙarfin ta, take kuwa ya tafi ya daki kan baaba dake jiran a buɗe ya ciwa koma waye mutunci.
Chapter 11 · 0% Book details