← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 64

Sashe 31

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bakin gate security suka tare su demanding for their approved card Wanda ake turawa duk wanda yayi booking resort É—in wanda su ze nuna kafin a bar shi ya shige, card É—in na É—auke da sunan wanda yayi booking, photon sa, adadin kwanakin da ze yi lastly floor number and room number.

Dole tasa ya tashe ta tare da nuna mata securities É—in ta window É—in ta, da sauri ta tashi zaune sosai tare da gyara zaman ta ta janyo wayar ta ta shiga ta nuna musu card É—in ta seda suka duba suka tabbatar kafin su tambayi na Saraki shima ta nuna musu kafin a aka basu hanya suka shige.

Parking yayi gurin da wani security ya nuna musu dan komai nasu a tsare yake shiyasa ma suke da ƙayyadaddun adadin da suke approving zaman su a wajen, ko da kuwa mutane nawa ne sukai booking in dai adadin su ya cika sedai su bawa mutum haƙuri ya tara a gaba hakan yasa babu wani hayaniya ko kace nace, so classy and peaceful.

Fitowa haka yi daga motar customer service biyu suka ƙaraso da sauri, ɗaya ya ɗau ƙaramar jakar kayan saraki ɗayan kuma ya ja trolley ɗin Kisnah, key service suka biya suka karɓi card ɗin da zasu dinga locking and unlocking ƙofofin ɗaku nan su kafin su nufi elevator, a tenth floor suka fita inda nan ne ɗakunan nasu suke, bakin ƙofar wani ɗaki suka tsaya ta saka card ta buɗe ɗakin sannan suka shiga, dakatar da ma'aikatan tayi daga ajiye jakar ta tare da faɗin su jira zasu ƙarasa mata da tata nata ɗakin, card ɗin ta miƙawa saraki tana faɗin

"Yaa ga card ɗin ƙofar ka, bari in ƙarasa in yi wanka na gaji da yawa".

Wannan karon kasa yin shiru yayi dan tun daga compound ɗin wajen ya fahimci dole se ya saka ido a kanta dan yadda yaga mutane na al'amuran su kai tsaye dan majority ma'aurata ne da suka zo yawan shaƙatawa da kuma hutawa se ko samarin da kan ɗauko ƴan matan su dan holewa wanda baya raba ɗayan biyu itama wani ta biyo.

"Ina É—akin naki yake?".

"Room 50, kamar apartment yake É—an yana da parlour Wanda zamu yi sharing da su Hameedah se kuma bedroom da kowa na da nashi É—auke da toilet a ciki".

Gyaɗa kansa yayi kafin ya shige nasa ya rufo ƙofa ita kuma tayi gaba har ƙofar nasu ɗakin da duk a sake floor ne, bakin ƙofar suka ajiye mata trolley ɗin tayi musu godiya suka wuce ita kuma ta buɗe ƙofar ta shiga.

Sosai su Meenah suka nuna farin cikin ganin ta wanda da ƙyar ta samu ta zame zuwa bedroom ɗin ta tayi wanka ta saka shorts iya cinya se guntuwar shimi ta bi lafiyar gado.

A can ɗakin saraki shima wankan yayi dan ya gaji sosai kasancewar be taɓa dogon driving ba se yau shiyasa gajiya ta rufe shi.

Wanka yayi fito da bathrobe a jikin sa kafin ya zauna kan gadon É—akin ya jawo jakar sa ya zage ya É—au shorts da jallabiya ya saka yayi sallar zuhur da ta same su a hanya kana ya cire jallabiyar ya kwanta.

Bacci tayi me daɗi kafin ta tashi ta fita parlor ɗin taci abinci sannan suka shiga hirarrakin su irin na ƙawaye.

Ƙarfe bakwai da ƴan mintuna suka fito shirya kowacce cikin irin tata shigar suka nufi spa ɗin da ke wajen, ƙwataccen guri ne da ko a cikin resort ɗin iskar cikin sa ta banbanta da ta ko ina saboda madaidaitan bishiyun da aka kakkafa suna rausaya wa sunan fitar da tattausar iska da ta haɗe da ƙamshin fresh sea ɗin gefen wajen.

Kan kujerun da ke zagaye da table ɗin me ɗan girma suka zazzauna ana ta hira kafin daga bisani Kisnah tayi shiru da bakin ta ɗan tuni hankalin ta ya koma kan ruwan da yake ɗan motsi garai garai dashi gwanin burgewa, rabon ta da waje irin wannan shekara biyu kenan, da a lokacin tana Canada kusan duk week tana hanyar bakin beach da spa Sabida mayatar son ruwa da Allah ya jarrabe ta dashi, farkon zuwan ta nan lokacin tana level one ne da suka samu hutun first semester tazo tayi sati ɗaya ta koma lokacin tun kan ta san su Hameedah, dan har gwara Surayya da Leekha ta san su tun lokacin sedai ba wani good times suke ba ana dai hi hi ne, farkon alaƙarsu da Surayya tun wani group assignment da ya haɗa su ne daga nan kuma se suke dan gaisawa sosai har suka ɗan saba, Meenah kuwa se suna level two suka haɗu lokacin da ita Meenahn ta Sami carry over a first semester ɗin su tana kuka gaban notice board ɗin da aka kafe musu, sosai ta bawa Kisnah tausayi a lokacin dan haka ta ƙarasa ta ɗaga ta da alƙawarin insha Allah zata dinga koya mata course ɗin da ta faɗi har tayi catching up ƙarkari dai ta sa a ranta zata yi, Hameedah kuwa cousin ɗin Meenah ce da tayi joining ɗin su later farkon second semester, daga baya ne Leekha ta shiga cikin su sosai dan farko sedai ɗan gaisuwa.

Tapping É—in ta da Surayya tayi yasa ta É—ago da sauri tana mata kallon tambaya

"Wane irin tunani kike yi haka Kisnah, anata kiran wayar ki nima ina ta miki magana amma shiru baki jini ba".

"Ringing Kuma, amma ban ji ba?".

"Ta ina zaki tafi, Allah yasa wata bata faÉ—a tsakiyar kogin da ba mataimaki gabas da yamma ba balle kuma kudu da arewa".

"Wane irin kogi kuma wace ta faÉ—a? Ban gane ba".

"Gaya min, wane me sa'ar ne haka ya sami damar sace wannan zinariya zuciyar ta kyakkyawar budurwa kamar queen Kisnah ta?, dan da alama queen É—in mu ta faÉ—a cikin makauniya kurma ..........".

"Kuma gurguwar soyayya ko, dan nasan abinda zaki faÉ—a kenan".

Dariya suka saka duka dan sosai Kisnah tafi sakewa tayi wasa da dariya da Surayya duk cikin friends ɗin nasu kuwa, Leekha kuma, hmmm yarinyar tayi dan baza' a taɓa zama a zagi Kisnah a gabanta ba ta sani ita kanta in Kuma akayi kuskuren haka to bayan matakin da ita Leekhar zata dauka se ta kuma sanar da Kisnah ɗin, Meenah kuma tana gwada mata kulawa fiye da kowacce cikin ƙawayen nata sedai ita tasa sakin jikin ta sosai da ita duk da cewa ba wai tana ɗari ɗari da ita bane sedai ba kamar yadda ta sake da Surayya ba, Hameedah kam ba a magana dan tun da ta gane halin ta ta ci maganin zama da ita.

Ringing É—in wayar yasa ta mida hankalin ta kan screen É—in tayi picking tana kaiwa kunne

"Hello Queen".

Deeq ya faɗa daga can ɓangaren, da murmushi ta amsa da hi

"Kin ƙaraso ne?".

"Tun É—azu, har na huta mun ma fito da su Meenah, muna spa".

"Okay Bari in ƙaraso".

"K". Tace tare da kashe wayar suka cigaba da hirar su da Surayya.

Tun daga nesa da ya hango ta yake ta sake mata murmushi har ya ƙaraso kusa da su, miƙewa tayi suka rungume juna kafin ta janye jikin ta ya ƙara sa kusa da su Meenah sukayi shaking hands da dukan su Sannan ya dawo wajen ta.

Kujerar kusa da ita ta right side É—in ta ta ja masa dan ya zauna yayinda Surayya take left side sedai be zauna É—in ba se kallon kujerar yayi ya maida kallon sa kanta Yana marairaicewa

"Please kissy muyi tseren nan da muke yi da boat a Canada, Allah i missed those moments like hell".

Ɗan shiru tayi tana kallon sa kafin ta juya ga ruwan da dama tun ɗazu take hasaso shiga cikin sa sedai tana dannewa yanzu kuwa da ya faɗa se taji hakan kawai take so, miƙewa tayi yayinda Surayya ta tambaye ta ina zata ta faɗa mata, da sauri itama fa miƙe tace zata yi, kallon kanta Kisnah tayi cikin ƙarewa shigar ta kallo, doguwar t-shirt ce irin me saukowa har gwiwar nan se ɗan bumpshort da ta saka se ko farin canvas ɗin da ta sanya a ƙafar ta, gashin ta nannaɗe cikin style ɗin bun ta ɗora p-cap, gaban Leekha ta ƙarasa ta ɗau cardigan ɗin da Leekhan ta cire ta maƙala a jikin ta dan tasan dole sanyi ze iya damun ta kafin suka nufi wajen jiragen su ukun...............✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fisabilillah.

_The two hardest things to say in life are hello for the first time and goodbye for the last._

Ouummey 21 (8/11/2022 10:40 PM)

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

________________________________

                          Page 2️⃣1️⃣

________________________📖 Wajen jirgin suka ƙara sa nan Surayya ta karɓi ɗaya ta biya nata kuɗin a lokacin su kam ɗan ƙaramin receipt ɗin da yayi payment tuntuni ya nuna, guda ɗaɗɗaya kowa ya shiga shi kaɗai, seda kowa ya gama shirya wa kafin Deeq ya irga ɗaya, biyu, uku inda yana cewa ukun kowacce tayi pressing start button na jikin jirgin haka shima suka shiga gudu cikin ruwan suna kwana kwana riƙe da steering da suke controlling direction dashi.
Chapter 31 · 0% Book details