← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 64

Sashe 26

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinci ta dafa mata me rai da lafiya tare da lemukan gargajiya da ta san gimbiya tafi son irin su dan ƙarin lafiya da ƙarfin jiki kana ta kwaso ta jera su kan ledar cin abinci da ta shimfiɗa gefen kilisar gimbiyar.

Ko da Mami ta fito taga aikin da Laylah tayi ba ƙaramin daɗi taji ba ta dinga saka mata albarka a ranta tana fatan Allah ya dawo mata da Sarakin ta lafiya ayi bikin su dan fa tabbas ɗan nata be fa mata bayan Laylah.

Cikin so da ƙauna da kuma shaƙuwar dake tsakanin su suka ci abincin tare suna ɗan taɓa hira jefi jefi har suka gama Laylahn ta kwashe kwanikan zuwa kitchen ta kuma wanke su tare da gyara kitchen ɗin tas.

A ranar kam ma'aikatan sashen gimbiya hutu suka yi dan Laylah ce ta sake gyara sashen tare da haÉ—e shi da sassanyan turaren wuta me shiga rai kana ta shiga É—akin gimbiyar ta gyara mata wardrobe kafin ta gyara É—akin gaba É—aya.

Waɗannan halayen na Laylah ke kuma ƙara wa gimbiya son ta Dan duk sanda tazo gidan tofa bata da zama ta dinga hidima da gimbiyar kenan har se ta koma nasu kafin ta huta wanda yanzu ma haka ne.

Ko da ta tashi tafiya kaya sosai mami ta haÉ—a mata har ledoji biyu tare da godiya da sa albarka har suka rabu.

Cikin farin ciki ranar Laylah tayi bacci wanda duk take gidan Mamin hakan ke faruwa dan sosai hankalin ta yake kwanciya da ƙaunar da Mamin ke mata har take ji a ranta bata da sauran matsala sets jiran dawowar Saraki dan ta san tabbas fa bashi da wata mata se ita Laylahn gimbiya.

***********

Zaune take cikin kyakkyawan garden din ta ta barbaza takardu a gefe gabanta kuwa laptop ɗin tace haka kuma hannun ta riƙe da wayar ta, wannan zaman duk na yin assignment ɗin CON005 ne sedai har fiye da mintina Talatin da zaman nata ba abinda ta fahimta haka ko kan pen bata saka a paper da sunan rubutu ba, dafe kanta tayi tana sauke ajiyar zuciya cikin tsananin damuwa dan zuwa yanzu kam bata san ya zata yi ba wallahi, tayi tayi amma ta kasa gashi ita bata san wani senior ɗin su ba a department ɗin law balle taje ko ɗora ta a hanya ayi, hasalima ko ƴan level ɗin su ba kowa ta sani ba balle ayi maganan saman su.

Cikin karaya ta miƙa hannu ɗan sake duba question ɗin a karo na ƙarshe taga ko zata fahimci me za'a yi dan Allah ya sani daga wannan karon in har bata gane ba to ta haƙura ta bar wa Allah kawai, ta tafi da carryover ɗin ta gyara next year.

Zaro takardar tayi se taga wasu takardu sun faɗo tare da ita, ɗan tsira wa takardun ido tayi ganin su ɗauke da rubutu alhalin ita tasan bata ajiye paper me rubutu ba se kuma ta kauda kanta ta ɗau wadda take buƙata a lokacin sedai ganin ta itama cike da rubutu yasa ta ɗan yi turus gaban ta na faduwa kafin kuma ta shiga warware ta da sauri har hannun ta na rawa.

Cikin sauri ta shiga bin paper da ido wadda ta tabbatar tata ce dan ga sunan ta da ragowar information ɗin ta da ta rubuta nan jikin paper, kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi jikin ta ya ɗau rawa kafin ta shiga karanta jerarren rubutun da akayi shi cikin ƙware wa layi bayan layi duk da kuwa takardar bame layika bace Dan plain sheet ce, tsaf ta karanci rubutun gaba da baya sedai ganin be ƙare ba yasa da sauri ta ɗauko papers ɗin da suka faɗi ɗazu ta hau neman continuation ɗin ta ɗora karatun, wasa wasa nan da nan ta gama karantawa kuma se lokacin ta fahimci me malamin ke nufi amma saboda tsabagen mugun ta yadda yayi twisting question ɗin ba za ka taɓa kawo abinda yake nufi ba kenan.

Tsananin murna ne ya kamata har da hawayen ta sosai ta ninke takardun ta maida cikin textbook É—in ta se kuma ta shiga tunanin waye ya amsa mata question É—in, ita dai in bata manta ba har jiya da ta shiga test bata rubuta ko A ba bayan question, kuma tun da ta fita da littafin ba wanda ta bawa haka kuma tun da ta dawo dasu ta kai É—aki bata kuma É—auko su ba se yanzu haka kuma ba wanda ke shigar mata É—aki balle tace.

"Yaa Saraki". Sunan yai ringing a mind É—in ta, É—an shiru tayi kafin kuma ta shiga gyaÉ—a kanta cikin yadda da shi É—in ne yayi mata dan tun a motar ta bar littafin da zata shiga test se jotter kaÉ—ai ta shiga dashi ta koya wa su Meenah abin da tayo research haka kuma da ta shiga Company a mota ta bar su gaba É—aya wanda tun da ta É—ebe su daga motar da suka dawo daga Company bata kuma fito dasu ba se yanzu, to in bashi bane waye yayi mata, aljanu ko wa? Kai shine ma, wallahi shine.

Da sauri ta kwashi takardun ta fita daga garden ɗin ta shigo ta main falo kafin ta sake fita da gudu gudu ta ƙarara compound ɗin tana ƙwala masa kira, sosai ta ke kiran shi not minding yadda ragowar workers suke binta da kallo, Isa me bawa flowers ruwa ne ya shaida mata ai yaje masallaci, bata ji daɗi ba dan ta so ta sake shi yayi mata confirming shine ta kuma gode masa sedai zata jira ya dawo.

Juya wa tayi zata koma ya turo ƙaramar ƙofar gate ɗin ya shigo da sallama a bakin sa, da sauri ta juya dan da ɗan karfi yayi sallamar hakan yasa itama ta ji, da gudu ta nufe shi wanda shi dan be lura da tahowar ta ba se ji yayi an faɗa kan sa da ƙarfi, ƙamshin turaren ta ne yasa ya gane ita ce ya kuwa yi saurin janye jikinsu a yana istigfar a ransa yan kuma haɗe fuska a fili.

Sakin baki tsirarun ma'aikatan dake kaikawo a compound É—in suka yi suna bin su da kallo kasancewar da yawa sun tafi sallar juma'a, bata ko bi ta kan su ba ta É—ago tana kallon Saraki da ya haÉ—e rai cif sedai ita ko a kwalbar rigar ta dan bata ma san abinda tayi ya haÉ—e rai ba kuma dama ya saba kusan ko da yaushe haka yake haÉ—e rai in Yana tare da ita so shiyasa ma bata wani damu ba.

"Yaa kai kayi min assignment ko, daama wallahi na kasa yi kaga tun da safe nake zaune amma ko fahimtar question É—in ban yi ba, Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ya ja da ran iyayen ka, Nagode sosai, kai ban ma san ta ya zance maka Nagode ba wallahi".

Ta faɗa sounding very very happy, addu'ar da tayiwa iyayen sa a ƙarshe ya sa ya ɗan sassauta haɗe ran da yayi yana kuma tausar kan sa da ita hakan a wajen ta bakomai ba ne and he promised to transform her so be kamata ya dinga haɗe rai haka ba dole ta nasiha ce yi mata musamman irin wannan lokutan da take cikin farin ciki.

"Kalli, ƙafar ki ko takalmi babu kika fito".

"Yaa bazaka gane farin cikin da nake ji ba, I feel like in yi ta rawa har se na gaji".

"So in kikayi rawa se a san kina farin ciki kenan? Wat of kiyi alwala kiyi sallah raka'a biyu ki gode wa Allah da yakawo miki É—auki lokacin da kika yi giving up? A tunani na hakan se fi ko?".

"Sure hakan zan yi riƙe takardun nan bari kaga in ma je inyi yanzu da sauri".

Ta faÉ—a tana sama sa takardun a hannun sa kafin tayi cikin gida da gudu, girgiza kai yayi ya wuce É—akin sa bayan ya sake haÉ—e rai ganin yadda gana É—aya ma'aikatan compound É—in suka saki aikin su suka maida hankalinsu kan su.

Zama yayi kan sofa bayan ya shigo ɗakin ya cire hular kansa ya ajiye tare da pray mat ɗin kana ya wuce wajen fridge dan ciro ruwa se kuma ya ci karo da ledar kilishin jiya da cups ɗin icecream, fasa ciro ruwan yayi ya ɗauki cup ɗaya na icecream ɗin ya koma kan sofar ya shiga sha a hankali har ya ƙarar kafin ya jefa cup ɗin cikin ƙaramin waste bin dake gefen ƙofar ɗakin.

Bum yaji an faÉ—o Masa É—aki without taking excuse hakan yasa ya É—ago da sauri dan ganin waye se kuma ya ci karo da fuskar ta tana sake masa kyakkyawan smile, É—an yamutsa fuska yayi dan Allah ya sani ya fara takura

"Me kika zo yi nan".

"Ya kai fa nazo nema, kaga tun da kayi min assignment É—in dama akwai test É—in da Zamuyi gobe kuma kaga akwai abubuwan da ban iya ba acikin shine na É—auko ka koya min, laah na manta ban faÉ—a maka ba nayi sallar na godewa Allah kamar yadda kace".

ÆŠan dafe kansa yayi saboda tsabar surutunta da har ta fara samasa ciwon kai

"Ki kwashi litattafan ki gobe na koya miki".

"Yaa ai gobe ne test É—in fa".

"To kai na ciwo yake, ya zan miki ne, a'ah".

Jikin ta ne yayi sanyi jin yace kan sa na ciwo, kwashe takardun ta da ya ajiye kan sofa a gefen sa tayi tare da juyawa zata fita

"Sorry yaa, ban sani bane Allah ya baka lafiya".

Dan tsaki yayi kafin ya dakatar da ita

"A ina zamu yi karatun dan ba dai a É—akin nan ba".

Da sauri ta juyo cikin farin ciki se kuma ta É—an rage fara'a

"Baka ce kanka na ciwo ba".

"Out in bakya buƙata".

"To muyi a garden É—ina ko main garden gashi can ta gefen gate".

"Meet me there a main garden É—in by 3pm".

Da sauri ta amsa da toh kafin ta fita cikin jin daɗi....................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fisabilillah.

Ouummey 18 (8/9/2022 8:06 PM)

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
Chapter 26 · 0% Book details