← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 64

Sashe 18

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu ya ɗaga mata kasancewar karatun yasha kansa itama bata kuma ce masa komai ba ta shiga zuzzuba masa kayan abincin da ta ƙaraso dashi dan a falon farko ma'aikata ke ajiyewa me girki kuma se ta ƙarasa dashi.

Seda ya gama karanta jaridar kafin ya ajiye ya juya gare ta, cikin sakin fuska da walwalar da yake tsintar kansa duk ya kasance tare da ita ya amsa mata gaisuwar da tayi masa É—azu yana me tambayar ta ya ta wuni.

Abincin ta tura gabansa bayan ta amsa shi da lafiya lau, cikin kwanciyar hankali ya soma cin abincin sa yayinda gimbiya Haleematu ta kafe shi da ido dan É—an ta Saraki take hangowa a tare dashi.

Yanayin nutsuwar shi, yadda yake riƙe spoon har zuwa yadda yake tauna abinci duk takawa ya gado hakan yasa yanzu take ganin kamar shine a gaban ta, a dabarance tasaka tafin hannun ta ta goge hawayen rashin ɗan ta da ya zubo mata dan bata so takawan ya lura da halin da take ciki sedai abinda bata sani ba tuni ya gane me take tunani tun sanda ta kafe shi da ido har hawayen da ta share.

Ya daɗe da sanin Haleematu macece me tsananin kawaici haka kuma yafi kowa sanin halin ta na haƙuri kuma yafi kowa shaida irin son da take yiwa gudan jinin nata.

Tissue ya zara ya goge bakin sa bayan ya gama cin abincin, tashi tayi zata janye kwanakin ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata kusa dashi

"Zauna nan Haleematu".

Kamar yadda ya umarce ta haka ta zauna dab dashi suna fuskantar juna, a hankali cike da dattako ya ruƙo kyawawan yatsun hannunta ya shiga murzawa a hankali kafin cikin murya me taushi ya shiga mata magana

"Me yake damun Haleematu na da har yake sata hawaye da damuwa? Wace irin damuwa ce haka da har gimbiyar Giwa ta kasa daurewa har raunin ta yana bayyana a fili? Shin akwai matsalar da ta shafi gimbiya ta da zata gagara sanar da ni Sarkin ta?

Duk yadda taso daurewa kasawa tayi, tsawon watanni biyu na barin Saraki masarauta yau ne takawa ya nuna yasan tana da damuwa duk da ta daɗe da sanin ya fahimci hakan yana dai kawar da kai ne dan kar ya bata fuskar tunkarar sa da batun Sarakin ko yaya sedai abinda ya manta a cikin halayen ta shine tafi kowa sanin sa da iya  karantar sa kamar yadda yafi kowa sanin ta da fahimtar ta, ya manta tunda har ya nuna baya son jin komai dangane da Sarakin ita ɗin bazata taɓa kawo masa batun ba saboda tsananin biyayyar ta.

Janyo ta yayi jikin sa yana bubbuga kafaÉ—ar ta har tayi me isarta ta share hawayen ta kafin ya É—ago ta

"FaÉ—a min, menene damuwar gimbiya ta".

Murmushin da ya tsaya iya saman lips É—in ta tayi kafin ta bashi amsa

"Ba wata babbar damuwa bace, kawai dai zuciya tace bata min daÉ—i haka ina ji na empty, shikenan"

Tsananin tausayin ta ne ya kama shi, dama ya sani ba zata kawo masa batun Saraki ba ko za'a shekara nawa ne kuwa, shi kansa yana kewar ɗan nasa sedai da ya tuno irin laifin da ya aikata se yaji baya ko san jin sunansa balle tunawa dashi, bare kuma ita da yana cikin wanda zasu bada labarin irin shaƙuwar dake tsakanin su, akan ce ƴa mace itace ta uwa mace sedai a ɓangaren Sarakin da gimbiya is different, komai nasa Mamin sa ce, itace abokiyar sa, malamar sa, Auntyn sa, yayar sa kuma mahaifiyar sa haka a gare ta Saraki ne ƙawarta, maman ta, yayar ta, kuma wanta, ya sani in yace kar ta damu ma be mata adalci ba dan haka be sake ɗaga maganar ba se nasiha da wa'azi da ya shiga yi mata har hankalin ta ya kwanta har tayi cikakken murmushin da ya fito tun daga zuciyar ta ba wai iya fatar baki ba.   (Allah Sarki uwa, i love U so much my umma💞).

................................

Babbar macece sedai ba wai irin girma sosai ɗin nan ba a kishingiɗe kan tattausan gadon da yasha shimfiɗu na alfarma, a ƙalla bazata wuce shakara 48 ba , daga kishingiɗen da take ta ke girgiza ƙafafunta da suka sha zanen jan lalle irin na zamani fuskar ta ɗauke da ƙasaitaccen murmushi, daga gefen ta kuwa matashin saurayi ne zaune kan tuntun ƙafar sa ɗaya kan ɗaya yana dubanta

"Kar ka wani damu da wannan dan ni baya cikin lissafi na ko kaɗan, ko kana manta ka girme mashi ne kuma a halin yanzu kai ke amsa sunan YARIMA ME JIRAN GADO? kana tunanin zan yi sake da sarauta zata faɗa ɗakin Haleema ne bayan ina da ɗa babba? Ko kaɗan dan haka ka kwantar da hankalin ka ka cigaba da rayuwar ka ni mahaifiyar ka RUMANA na maka alƙawarin indai ina raye to sarautar Daular Noor taka ce".

Sosai farin ciki da murna suka wanzu kan fuskar sa

"Shiyasa nake matuƙar so da ƙaunar ki Ammi na, Allah ya bar min ke ya ƙara miki lafiya me inganci ki ganni zaune kan karaga matsayin sarkin daular Noor, Sarki UTHMAN MUHAMMAD HASHEEM".  Ya ƙarasa faɗa sautin Muryar sa cike da tsananin buri da fata wanda itama gareta gimbiya RUMANA hakan ne a ranta.

***************

"Ke yanzu Laylah baza kiyi wa kanki karatun ta nutsu bane, shin baki san rayuwar mace nada limit bane, fidabilillah ace kin zauna jiran gawon shanu kin ƙi aure kin zauna jiran wanda baki san yaushe zai dawo gare ki ba, yanzu kin yiwa kanki adalci kenan? Ko kuwa kin manta har Yarima Saraki ya bar masarautar nan be taɓa son ki ba ne?".

Hawaye ne masu zafin gaske suka zubo daga idanun matashiyar dake duƙe ƙasan dattijuwar dake magana, kallo ɗaya zaka musu kasan uwa da ƴa ne saboda tsananin kamannin da suke yi, a hankali dattijuwar ta saka hannun ta ta ruƙo kafaɗar ƴar tata

"Bawai bana son ki da Saraki bane Laylah, hasalima se na fi kowa san tarayyar ku sedai dole in faÉ—a miki gaskiya, kin sani kaf masarautar nan ba da wanda na aminta sama da gimbiyar Giwa haka itama gare ta, dan Allah ki cire komai a ranki ki bawa maneman ki dama Laylah, wallahi zaman ki haka ba aure yana damu na".

Ruƙo hannun dattijuwar Laylah tayi cikin sakin murmushin da be kai zuci ba,
" Ki taya ni da addu'a Ummi na, insha Allah zan yi kamar yadda kika ce, nima ina so in manta dashi sedai har yau na kasa hakan, kullum gani nake kamar ze dawo gare ni amma insha Allah a wannan karon zan ƙoƙar ta".

Cikin tausayin autar tata Umma ta ce

"A yanzu kam ni Sameera bani da wadda nake wa addu'a kamar ke Laylah, dan haka kar ki damu kinji Allah na tare da ke".

Gyaɗa kai Laylah tayi kafin ta miƙa

"Bari in je in duba abincin can kar ya ƙone".

Ficewa tayi tana saƙa da warwara cikin ranta na yadda zata iya yakice Saraki cikin zuciyar ta....................✍️.

Hhhhhhh😂🤣🤣 su Mommy an yi laushi luɓuɓus😜😜.

Gimbiya RUMANA, ko ita kuma wacce haka🤔oho🤷

Toooooo faaaahhh😳 ke kuma Laylah daga ina, wata sabuwa inji ɗan caca, #team_saraki Ina tambaya 🤔

©️ Ouummey 📚✍️.

*☑️Ote, comment and share fidabilillah*

Ouummey 13 (8/6/2022 9:46 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                          Page 1️⃣3️⃣

_________________________📖ko da suka isa can suka tadda su Meenah and alhamdulillah jikin Surryn da sauƙi sosai dan ta ma farka har suna ta hira da Leekha, kamar yadda ta saba haka tayi wato just ta tura ƙofan ta shige without Salam yayinda Saraki dake bayanta riƙe da ledodin shopping be shiga ba se da yayi sallama ya jira izini tukunna dan ga dukkan alamu gareshi mata ne a ɗakin saboda tashin muryoyin su da ake ɗan ji daga waje.

Kujerar gefen gado Meedah ta turawa Kisnah ta zauna suka shiga gaisawa da tambayar ya me jiki kafin ta maida kanta wajen Surayya da tun da Kisnahn ta shigo take ta sakar mata murmushi.

"Ya jiki swee swee?

Ta tambayi Surry calling her with the name she used to,

"Alhamdulillah da sauƙi Kissy, Ina ta zuba ido amma shiru nace to akwai abinda ya tsaida ki, hope dai guy ɗin be miki komai ba ko?".

"Sure naso na fito da wuri sedai kuma i have to wait for my new driver da na bawa appointment É—in ganawa dashi da safen, no kar ki tashi hankalin ki ba abin da yayi min, all thanks to you my swee swee".

"Masha Allah, that's what I wanna hear tun farkawana".

"And you'll heal faster insha Allah".

"We hope so my Kissy, so your new drive brought you here".

"Yesso, ai tare ma muke, here he is".

Ta faɗa tana juya wa dan nuna mata Saraki sedai wayam bata ganshi ba, miƙewa tayi ta nufi ƙofa tana faɗin

"A'ah, ina kuma ya tsaya, i thought tare muka zo kofar É—akin".

Buɗe ƙofar tayi da niyyar fita duba shi se ta tadda shi tsaye hannayen sa riƙe da shopping bags ɗin har lokacin, zaro ido tayi cikin mamaki

"So all this while kana tsaye a bakin ƙafa still holding the bags ko ɗan ajiye wa ka huta ma baka yi ba kamar wani soja, tabɗi, okay let's enter".

Bece mata komai ba ya bi bayanta cikin ɗakin, be kalli kowacce ba cikin su dan ba wadda ta amsa sallamar da yayi ya ƙarasa gaban Kisnah ya ajiye bags ɗin ya juya ya fita, da ido duk suka raka shi banda Kisnah da hankalin ta ke kan waya tana duba messages a watsapp ɗin ta

"Lord of heaven, Ina kika samo cute and handsome guy É—in nan Kisnah?".
Chapter 18 · 0% Book details