← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 64

Sashe 29

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haɗe rai sosai Saraki yayi har fiye da yadda Kisnah tasan yana yi dan a wannan ɓangare sam baya wasa haka baya san wasa baya kuma san ayi masa wasan wanda irin wannan jajircewar ta samar masa da girmamawa da kuma ɗaukaka a cikin ƙankanin lokaci, a yanzu da yake zaune ba yana hango kansa ne zaune cikin mall ba ƴana hango kansa ne cikin court trying to find out a hidden truth.

Direct ya sauke duban sa gefe kujerar da mutumin yake wadda ba kowa kanta ya kuma kausasa murya sosai alamun ba wai wasa yake ba

"Ƙin amfani da damar da muka bayar ze sa mutimin ya fuskanci hukunci me tsananin tsauri wanda bana jin ya taɓa fuskanta a kaf rayuwar sa, ba zance kar me laifin ya gudu ba se dai ma nace Allah ya bashi sa'ar hakan wanda hakan shine baban kuskure na ƙarshe daze yi a rayuwar sa dan daga yanzun nan da muke zaune tare da ku anan Yana under supervision ɗin security agencies daban daban, gare ku ragowar maaikata, kusani ba wai an ɗauke ku aiki an ƙyale ku kowa yayi abinda ya ga dama bane, dukkan shige da ficen ku dama information ɗin family ɗin ku duk muna samu dan haka wanda ya tsaya yai aiki tsakani da Allah will receive two reward, one here from us a duniya and the other from Allah a nan duniya ko a lahira, wanna shine iya abinda zan iya cewa kan wannan batu, Allah ya ƙara muku lafiya da ƙarin gwiwar yin aikin ku kan gaskiya da Amana ya kuma ɗaukaka wanna waje".

Da Amin kowa da ke cikin hall É—in ya amsa har da Kisnah dake zaune tana kallon shi cikin jin daÉ—i da burgewa, yadda yayi addressing issue É—in ba wanda baze yarda cewa dagaske bane sun kama me laifin tuntuni bayan yar awa É—aya da ta wuce lalube ne suke yi cikin duhu sedai bata san ko yanzu ya gano criminal É—in ba kamar yadda manufar meeting É—in take.

Cikin shan jinin jiki ma'aikatan suka fita gaba ɗaya kowa na zargin kowa sedai masu gaskiya ba su wani damu ba se masu ɗan tsatsa a zuci na rashin gaskiya suke shan jinin jikin su ya saura iya manager da Kisnah se Sarakin da ya miƙa a lokacin ya fara tafiya cikin takun sa na isa ya doshi hanyar fita

"Yaa pls ka jira ni, lissafi kawai ze yi min se mu tafi". Kisnah ta katse shi da sauri ganin yana gab da ficewa

"Ina mota". Iya abinda ya faÉ—a kenan ya fice batare da jiran me zata ce ba.

Cikin sauri suka yi lissafin da ya tsaida su wanda na kayan da akafi so ne cikin watan da ya wuce dan ganin ko za'a sami damar ƙara wasu tunda ana son su, takardun da zata cike kafin a shigar da file ɗin kundin fitar da kuɗi ta karɓa hannun managern da sauri tana faɗin zatai signing a gida se ta kawo masa daga baya.

Kishingiɗe kan kujerar driver yake kamar kullum yau ma ya saka wani cassette din wa'azi ne na wani babban malamin garin inda yake wa'azi kan irin tarin zunubin da ke cikin fitar da tsiraici, da sallamar da yanzu ta zame mata dole indai zata kusanci inda yake ta shiga cikin motar, gyara zaman sa yayi yana tayar da motar har lokacin yana cigaba da saurarar wa'azin, shiru duk sukayi yayinda motar ke tafiya smoothly kan shimfiɗaɗɗen titin da ba'a daɗe da zuba masa sabuwar coal tar ba, a kaikaice yake kallon ta ta ƙasan ido cike da son ganin jikin ta yayi sanyi da irin azabobin da malamin ke faɗa sedai kwata kwata ma ya lura hankalin ta baya nan yana can wani waje ne da be sani ba dan yadda ta kafe glass ɗin motar da ido bata ko ƙiftawa irin dai mutun yayi nisa a duniyar tunanin nan, be ji daɗin hakan ba dan saboda ita ya saka wa'azin ko ta rage wasu daga cikin shigar banzan da take yi, hannu ya miƙa ya canja wa'azin zuwa karatun Alkur'ani mai girma dan ya lura saurarar sa na kashe mata jiki sosai.

Juyowa yayi gaba É—aya da san dawo da ita daga tunanin ya É—an yi gyaran murya kafin yace

"Wa kika fahimta matsayin me laifin da yayi wannan aika aikan?".

Se da ta sauke ajiyar zuciyar firgita da ta É—an yi kafin ta kalle shi itama

"Ban fahimci kowa ba dan dukkan su basu bada wata ƙofa ba duk da bakowa nake iya ganin sosai ba".

GyaÉ—a kan sa yayi tare da yin shiru na tsawon mintina kafin ya yanka

"Ni na gane shi".

Da sauri ta karkato sosai har kamar zata bar kujerar ta zuwa tasa tana magana cike da zaƙuwa
"Wane ne yaa, wace number ce a gefen ƙirjin sa?".

Ta tambaya cike da curiosity kasancewar kowane ma'aikaci akwai identity number jikin rigar sa ta gefen ƙirjin sa ta dama haka kuma akwai sunan sa a bayan rigar haka kowanne ana bashi uniform set uku ne dan gudun matsala kamar ƙonewa, yagewa ko jiƙewa.

Kallon ta yayi for some seconds kafin ya ɗauke kai be bata amsa ba kamar yadda yaga ta zaƙu ta ji, kwaɓe fuska tayi ganin abinda ya mata kafin cikin sakkakiyar murya ta furta

"Yaa Saraki mana".

Harara ya juyo ya wurga mata ya sake maida hankalin sa kan titi, da sauri ta saki dariya kamar wata zararriya, jin taki denawa yasa ya juyo ya kalle ta hakan kula ya a dariyar ta ƙaruwa.

"Dama haka ka iya harara yaa, tabb wa yaga harira sunan wata mata".

Murmushi ne ya so ƙwace masa se dai ya danne ya ƙi ko kallon ta hakan yasa ta cigaba

"Haka ma fa É—azu a hall ka harareni kuma guess what, wallahi ka iya sosai dan har wani kaÉ—awa fa gashin ifon ka ke yi".

"013". Ya faÉ—a da sauri cikin son ta bar zancen hararar dan se ya ji yana É—an jin kunya, aikuwa da sauri ta tsayar da dariyar ta tana zuba masa ido

"Number criminal É—in kenan 013".

"Amma taya akayi ka gane shi yaa, 013 sunan sa Adams kuma physically mutumin kirki ne".

"Ki bincike shi sosai though ma yadda na karanci facial expression É—in sa he's so scared and na tabbatar ze dawo da kayan kamar yadda nace".

Girgiza kanta tayi tare da gyaɗa shi at once dan tasan tun da ya faɗa ɗin to Allah ya bashi ikon gano shi ne, batare da kuma sun sake cewa komai ba suka ƙarasa gida yayi parking ta fita, kamar yadda ta saba ta jingina jikin murfin side ɗin ta da ta rufe har ya kulle motar ya zagayo ɗan yi side ɗin ɗakunan su

"Good night yaa, have a nice sleep".

"Fi Amanillah". Ya amsa ta dan yasan tun da ta daÉ—i haka to ba zata kuma fita ba yau se gobe shiyasa tun yanzu ta masa bading bye, amsa matan da yayi yasa ta juya ta wuce flat É—in su dan It's to 3 rana tayi yawa a compound É—in.

Kwana biyu bata fita ko ina ba se ana ukun da ta shirya cikin shagalalliyar shigar da munin ta yakai wadda ya kwana biyu be ganta da irin ta ba, yau ɗin suna da babban taro ne dan yau Surry take birthday party ɗin ta wanda ya wuce satin da ya wuce da bata sami damar celebrating ba saboda ba'a sallame ta ba se shekaranjiya shiyasa suka shirya grand party na murnar birthday da kuma samun sauƙin ta dan yanzu ba kowa ne ma ze ce tayi ciwo ba se su da suka sani haka kuma samarin Surryn ba ƙaramin kashe kuɗi sukai ba wajen ƙawata shi dan yayi looking so big and classy.

Shigar da suka yi yau É—in special ce, komai na jikin su kuÉ—i ne barin ma Kisnah da iya rigar da ta saka 2.3 mil tayi order É—in ta kuma tare da ribbon É—in ta take zuwa, takalmin da tasa kaÉ—ai 310k ne se sun har É—in ta me kyau da ta siya a K&S 50k Dan designer and fashionable ce sosai.

A ƙalla dai kayan da ta sanya wa jikin ta kama daga kan riga, takalmi, hat, chain, earrings, rings, watch, leg chain and glasses sun tasar wa 4mil.

A kallo ɗaya zaka yi mata kasan Yes ta haɗu, so breathtaking dan tsayawa faɗar yadda baƙar rigar me walwali ta haska ta ɓata lokaci ne, kamar wata ƴar tsanar turawa ɗin nan da ake decor da su sedai gashi Sarakin namu yaya ga Kisnah sam shigar bata yi masa ba, dan rigar a tsage take tun daga ƙasa har rabin cinyoyi haka kuma ta gefe biyun ma tsaga ce har inda ta tsakiyar ta tsaya haka ma tsakiyar bayan rigar daga ƙasa.

Daga sama kuwa ba ƙaramin kama ta rigar tayi ba kuma siraren hannu biyu gare ta se zaren da ake ɗaurewa ta baya haka kuma wuyan buɗaɗden wuya ne ta gaba da baya da yasa ake hango saman ƙirjin ta sosai ta baya kuma har tsakiyar bayan a buɗe yake.

Kallo ɗaya yayi mata tun fitowar ta ya ɗauke kai cike da takaici, takaicin yadda ƴar musulmi gaba da baya ke irin wannan shigar ba kuma a gidan ta ba a'a sedan fita wasu su gani su yaba da sunan wani abu wai party, ɗaya daga cikin manya manyan abubuwan dake ƙara yaɗa ɓarna da fasali a ban ƙasa.

Tun da ta shigo motar take washe baki tana jiran taji yace mata tayi kyau sedai taga ko kallon ta be yi ba hakan yasa ta kasa haƙuri seda ta tanka

"Yaa ba kace nayi kyau ba". Ta faÉ—a tana É—an jujjuyawa daga zaunen da take cikin motar ita a dole se yaga adon nata

"Yaa baka ji bane?, Nayi kyau ko".

Ta sake faÉ—a jin be tanka mata ba, se a wannan karon ya É—ago ya kalle ta cikin watsa mata mugun kallon da yasa take taji jikin ta yayi sanyi

"Kyau? A cikin wannan mummunar shigar kike neman kyau".
Chapter 29 · 0% Book details