← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 64

Sashe 34

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba É—aya nan ta baro wayoyin ta dan bata san tana kallo ana damun ta da kira shiyasa ma ba zata tafi da ko É—aya ba, adai falon ta kuma tadda su har yanzu suna zaune se dariya suke yi alamun hirar tana kai musu yadda suke so gaban su cike da kayan ciye ciyen da drinks kala kala.

"Se na dawo".

"Ina kuma zaki yanzu?". Wannan karon Leekha ta tambaya, ɗan kallon Leekhan tayi cike da jin haushin yadda suke wani titsiye ta kamar wata ƙaramar yarinya sedai sanin ba halin Leekhan bane hakan se ta mata uzuri yau ɗaya dai

"ÆŠakin Asad, akwai Film É—in da zamu kalla tare a system É—in shi".

"Why not shi yazo ku kalla a nan?". Hameedah tayi interrupting sedai ko kallon ta Kisnah bata yi ba ta dubi Surayya

"Mind joining us?".

"No, am feeling somehow sleepy, kya bani labari".

GyaÉ—a kanta tayi tana É—agawa Meenah yatsu biyu

"Se na dawo babe".

"Hope you enjoy the movie". Meenah ta amsa mata sannan ta fice, tana fita Surayya ta miƙe ta musu good night ta shige bedroom ɗin ta haka ma Leekha ya saura Hameedah da Meenah, juyowa Hameedah tayi tana kallon Meenah da wani expression on her face yayinda Meenahn ta kau da kai kamar bata gani ba ta mata sallama ta wuce, dole ba dan ta so ba itama ta wuce nata bedroom ɗin dan ba yadda zata yi bayan ta kashe ƙwan ɗakin.

Knocking biyu Kisnah tayi Asad ya buɗe mata ƙofar ɗauke da murmushi a saman fuskar sa yana sanye da three quarter da farar t-shirt da ta kama jikin sa sosai, itama smile ta Masa tare da shiga ɗakin ya maida ƙofar ya rufe.

Kan doguwar sofar dake ɗakin ta zauna tana ɗan miƙe legs ɗin ta, be zauna ba ya wuce wajen fridge ɗin ɗakin ya zubo musu dambun naman dake cikin wani rufaffen madaidaicin container ya Kuma ɗauko drinks ya kawo ya ajiye kan Centre table ɗin da ke falon ya koma ya ɗauko glass cups masu kyau guda biyu ya ajiye sannan ya koma ya ɗauko system ɗin sa dake kan bed kana ya dawo ya janyo table ɗin gaban sofar a hankali kafin ya zauna kusa da Kisnah yana danne danne cikin system ɗin kafin ya ɗago ya dube ta

"Ready?".

Yesssss". Ta faÉ—a prolonging the 'S' sound.

"Here we go". Ya faÉ—a yana starting film É—in sannan ya É—ora kan table É—in suka shiga kalla.

Tun kafin ayi wani nisa sosai Kisnah ta fara kuka dan sosai Film ɗin yake da abun tausayi, lallashi ne Asad ya sha shi dan kamar wata ƙaramar yarinya haka ta koma, wasa wasa ba Film ɗin ya ƙare ba se after 2 dan it's a 3 hour film, ko da aka gama bata tafi ba wani Indian comedy na Rani Mukherjee me suna Aiya ya saka mata dan lightening mood ɗin ta, cikin ƙanƙanin lokaci kuwa se gashi tana sheƙa dariya kamar ba ita ce ta sha kuka ba, a hankali a hankali bacci yake fisgar ta dan yau ta gaji sosai har ma dai yayi nasarar sace ta gaba ɗaya, gyara mata kwanciya Asad yayi ya cigaba da kallon sa har se da Film ɗin ya ƙare wanda lokacin it's to five am sannan ya fara tashin ta a hankali.

A hankali ta fara buÉ—e idanun ta ta sauke kan sa, murmushi me sanyi ya yi mata kafin cikin cool and low tune ya Fara mata magana

"Hey sleeping beauty, it's subhi, kije kiyi sallah a É—akin ki, okay?".

Out of sleep ta gyaɗa masa kai kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa sedai dake ba sakin ta baccin yayi ba se ta kasa har se da ya riƙe ta helping her to stand ya kaita har bakin ƙofa sannan ta zare jikin ta tana lumshe masa ido alamun zata iya tafiya, waving ɗin ta yayi ta fita kafin ya maida ƙofar ya tafi toilet dan yin alwala.

Tafiya take a hankali har tana É—an layi na bacci har ta wuce É—akin su bata sani ba , daidai lokacin Saraki ya fito dan tafiya masallaci kamar yadda ya saba dan a can yake karatun Alkur'ani tare da nafilolin sa kafin exact lokacin sallah yayi, sosai yayi mamakin ganin ta a wannan lokaci and to his utmost surprise kamar ma layi take alaman bata cikin hayyacin ta sosai.

Kamar ya wuce ta sedai ya kalli ƙofar ɗakin su da ta wuce a baya sosai dan shi yana room 45 ne su suna 50 amms har ta wuce ɗakin nasu tama gota nashi, da sauri ya ƙara sa inda take tare da ruƙo ta dan dakatar da ita, a hankali ta juyo dan fa baccin ne sosai a kanta, ganin shi yasa ta ɗan ware sleepy eyes ɗin ta da suka canja kala zuwa golden brown saboda bacci

"Yaaaaaaa". Ta ja sunan sosai abinda ya sa Saraki kuma shaida ba'a hankalin ta take ba

"Yaaaaaaa É—akiiii zaaani".

Cikin takaici ya juya ta zuwa hanyar da ta baro hakan yasa ta buÉ—e idon sosai ta gan a bakin room 43 ma take

"Kaga ban ma san na wuce É—akin bama, am toooo sleeeepyyy".

Bece mata komai ba har lokacin sedai cikin ransa cewa yake taya zata san ta wuce tunda bata cikin hankalin ta?

Har bakin ƙofar ɗakin nasu ya rakata kuma be tafi ba seda yaga ta shiga cikin parlon kafin ya juya ya koma hanyar da ya baro heading to the elevator.

A falo ranar Kisnah ta kwana dan baya iya kai kanta É—aki ba saboda nauyin baccin dake kanta, se after seven ta tashi ta koma bedroom É—in ta É—ora baccin ta daga inda ta tsaya.

Ƙarfe goma ta farka ta shiga wanka sannan ta shirya bayan ta fito, yau kam ba laifi Canadian gown ta saka da yakai mata ƙasa dan har yana jan ƙasa ta baya ta sake gashin ta bayan ta taje shi tare da shafe shi da mayukan kai masu ƙamshi ta feshe shi da turaren gashi ta ɗora masa sun hat me kyau sosai kalar brown Wanda gown ɗin jikin ta milk and brown ce haka takalman ƙafar ta milk heels ne.

Ƙarar wayar ta yasa ta ƙara sa inda ta watsar dasu jiya da dare ta ɗaya wadda take ƙarar ta kai kunnen ta ganin sunan Surry

"Mun fita kina bacci Queen, in Zaki biyo mu muna highway mountain".

"Okay, I'll see in zan zo É—in".

"Okay". Surry tace tare da kashe wayar.

Zama ta É—an yi tana tunanin ta bisu ne ko kuwa tayi zaman ta?

"Garden". Kamar daga sama haka sunan ya faɗo cikin ranta, da sauri kuwa ta miƙe dan a rayuwar ta tana matuƙar son guri me korayen ciyayi da bishiyoyi shiyasa tun tana yarinya Abbi yayi mata ƙaton garden a gidan su.

A hankali a hankali take takawa kan corridor ɗin ɗakunan dan sosai marbles ɗin ke da santsin da in batayi taka tsantsan ba ze iya tiƙa ta da ƙasa saboda tsinin takalmin ta, gyaran muryar da taji a bayan ta yasa ta ɗan waiga hakan yasa suka yi four eyes da Saraki da ya fito dan zagaya wa saboda jiya gaba ɗaya a ɗaki ya wuni shiyasa yanzu yake buƙatar fresh air

"Good morning yaaa".

Gyaɗa mata kai yayi alamar amsawa dan yanzu kam ya sauko daga fushin da yake yi dan ganin abinda ya faru jiya yasan da beyi fushi ba da ko yaya ba zai bata space ɗin kwana wani waje ba dan zata kasance ƙarƙashin idon sa ne.

"To where?".

"Garden, won't mind joining me please, am lone".

"Okay". Ya ce mata dan haka suka jera suka cigaba da tafiya, daÉ—i sosai Kisnah ta ji ganin ya dena fushi da ita haka itama se ta ajiye alwashin ta a gefe.

A tare suka shiga elevator ɗin ɗan yana da faɗi sosai, a third floor suka sauka dan akwai garden me kyau a floor ɗin kafin ta masa jagora zuwa garden ɗin da tun 2 years back ta haddace hanyar shiga cikin sa though an samu sauye sauye a resort ɗin.................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fisabilillah.

Ouummey 23 (8/17/2022 8:10 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

Assalamualaikum warahmatullah ɗauka cin masoya littafin *SARAKI* daga kowane group most especially*SARAKI FANS CLUB* ina godiya sosai da addu'o'in ku ga ƴar uwa ta , Allah ya saka da alkhairi ya bar ƙauna, Allah kuma ya jiƙan dukkan musulman da suka riga mu gidan gaskiya, marasa lafiya Allah ya basu lafiya, mu da muke da ita Allah ya kara mana ya bamu ikon gode, masa Ameen summa Ameen.

Once again, nagode Allah ya bar zumunci da ƙauna 🥰.

                           Page 2️⃣3️⃣

_______________________📖 sunkuyar da kanta tayi ƙasa ganin irin kallon da yake watsa mata na rashin yarda kafin ta sake ɗagowa sedai wannan karon idon ta ya ɗan sauya launi

"I swear to God ban Sha komai ba, so nawa zan faÉ—a maka bana shaye shaye ne yaaa"?".

Ta ƙarashe maganar ranta na suya, a rayuwar ta taƙi jinin shaye shaye shiyasa kullum cikin yiwa su Hameedah faɗa take yi, ita magani ko na rashin lafiya in har ba kwantar da ita tayi ba bata taɓa shan sa, duk kuwa irin ciwon kan da zata yi ko ciki sedai ayi mata allura dan magani is her perfect enemy.

ÆŠan furzar da iska yayi daga bakin sa kafin a hankali yayi magana batare da ya kalle ta ba

"What about haÉ—a hanyar da kika ringa yi jiya da na ganki, me ya kawo shi?".

"Bacci ne a kai na sosai saboda na gaji sosai jiyan kuma ban samu hutu ba shiyasa bacci yaci ƙarfi na but am in my sence".
Chapter 34 · 0% Book details