Sashe 48
Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwance kan wani gadon kara da aka shimfiɗawa wani tsumma na hango Saraki, gaba ɗaya kamannin sa sun canja dan ƙafar sa ɗaure take da wani tsumma bayan an zagaye ta da karare haka ma hannun sa na hagu, da sallama dattijon ya shiga ɗakin yana ƙara sa gaban Saraki ya tsaya tare da bin sa da kallo na wasu daƙiƙu sannan ya ajiye ƙwaryar hannun sa ya ƙara sa wajen Saraki, hannu yasa ya ɗago ƙafar ya shiga kallon tafin ƙafar da yayi jajir dashi ga kuma alamun cuwuka sosai a jiki, hannu yasa ya lakato wani mai cikin wata ƴar jakar fata dake jikin sa ya shiga shafawa a tafin ƙafar, seda ya shafe ko ina kafin ya saki ya matsa yana taɓa ƙaurin sa da yake ɗaure da kararen, se aya taɓa sosai sannan ya gyaɗa kansa tare da yayyafa wani farin Ruwa kan gurin sannan ya tashi.
Wajen hannun ya matsa ya kama hannun ya jinjina shi cikin nasa kafin ya ajiye a hankali bayan ya É—an jijjiga shi, a hankali ya sunkuya ya kai bakin sa ya shiga tofa abinda ban sanu ba kan hannun, koren magani irin wanda aka shafawa Kisnah ya lakata ya shafa masa shima a kansa kafin ya tashi ya fita bayan ya sake bin sa da kallo.
******
A can wajen su kawu kuwa duniya sabuwa bayan sun ga hujjojin da yaran su suka basu na shedar mutuwar su Kisnah, wani ɗan ƙwarya ƙwaryar liyafa ranar suka yi a tsakanin su shida Alh Haladu.
Seda aka kwana aka wuni da faruwar lamarin kafin ya shigar da ƙorafi kan ɓatan Kisnahn yana me nuna tsantsar damuwa da tashin hankali Wada da ƙyar ƴan sandan suka sami lallaɓashi ya bar police station ɗin bayan an barbaza jami'ai cikin garin manya dan nemo inda take.
Ranar farin ciki wajen su Mommy kamar sallah ko ma fiye duk da so tayi su wulaƙanta rayuwar ta sedai ko a hakan ma duk ɗaya dan haka ta shiga addu'ar kar Allah yasa Kisnahn ta bayyana, haka ƴan sanda suka ɗin ga shiga lungu lungu neman ta amma ko alamar ta, ba wani club, hotels ko cinema dake garin manya da jami'ai basu shiga neman ta ba amma duk ba wani labari, cikin ƙanƙanin lokaci gari ya ɗauka da batun ɓacewar Kisnah, kiran wayoyin da ake wa su Meenah da su Surayya na wai jaje yasa suka san meke faruwa a ranar kuma suka haɗu gaba ɗaya suka tafi gidan su Kisnahn sedai ba ƙaramin rashin mutunci Mommy ta shuka musu ba dan ko barin su su zauna bata yi ba ta shiga jifan su da munanan kalamai har tana neman ɗora musu alhakin ɓatan Kisnahn, al'amarin be musu daɗi ba haka dole suka tarkata ƙafafun su suka fice daga gidan sedai basu koma gida ba neman ta da suka shiga yi a wuraren da suka san suna zuwa.
A kwana na uku da ɓatan ne kawu ya shigar da batun wai yana zargin driver ɗin ta ne ya sace ta, nan fa lamari ya canja aka shiga neman Saraki ruwa a jallo sedai rashin sanin inda za'a iya samun sa ya sa dole aka taƙaita binciken bayan an saka jami'ai a ko wani titi dan bincike duk motar da tazo wucewa.
Ranar da suka kwana biyar da ɓata ne aka samu rahoton samun ƙonanniyar motar su da suka fita a cikin ta, jami'an bincike aka ɗauko suka shiga aikin su a daidai wajen da aka ga motar kafin daga baya suka sanar da cewa motar ta kama da wuta ne sanadin dukan tankar mai da ta tare hanya wanda ya dukan yasa murfin gidan man ɓalle wa abinda ya haddasa tashin wuta a motar kenan bayan ta hantsila har so biyar.
Al'amarin ya girgiza da yawa cikin jama'a dan zuwa wannan lokacin babu wani mazaunin garin manya da maƙoftaka da bai san da ɓatan the CEO na K &S companies ba, ranar kawu kam a asibiti ya kwana saboda yadda ya dinga sumewa ana yayyafi masa ruwa daga ƙarshe kuma ya dinga sambatu kamar wani zararre dole aka dangana dashi asibiti.
Duk yadda Mommy ke ƙin Kisnah seda ta ɗan yi sanyi sanadin mutuwar kafin kuma daga baya ta watsar ta shiga fantamawa cikin nera, su Maigado kuwa duniya sabuwa babanta ya zama me kuɗi.
Seda kawu yayi kwana uku a asibiti kafin aka sallamo shi lokacin ya dawo daidai sedai ba uhm balle uhm uhm sedai yayi ta kallon mutane, dole a ka rufe Companies É—in K&S har zuwa lokacin da kawu ze dawo hayyacin sa ga kuma jimamin mutuwar mamallakiyar wajen da ma'aikatan ke ciki.
*******
Seda Saraki ya kwana shida be san wa ke kan sa ba kafin ya farfaÉ—o, zuwa lokacin kuwa tuni ciwukan Æ™afar sa da yaji sanadin gudu cikin daji yana taka Æ™ayoyi sun fara warkewa, zuwa lokacin kuwa har Kisnah ta saba ganin su Bingel dan ta daina tsoron su sedai kuma bata kula su haka kuma bata iya cin abincin su sedai a bata fura da nono kullum........................âœï¸.
Â©ï¸ Ouummey 📚âœï¸.
☑ï¸Ote, Comment and share fisabilillah.
Ouummey 32 (8/24/2022 10:07 PM)
💠💠💠💠💠💠💠ðŸ’
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠ðŸ’
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.Aâœï¸*
_________________________________
              Page 3ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
_______________________📖 Zaune take a bakin bukkar ta kan wata tabarmar kaba tana bin Bingel da ke kwanto shanu da garken su ke can gefen bukkokin su da kallo, yadda take iya kwance su ta na shafa jikin su ba tare da tsoro ba ba kuma tare da su shanun sun wa Bingel ɗin komai ba ya matuƙar ƙayatar da ita, ba tun yau ba in taga Fulani na kora shanu abin ke burge ta da cika ta mamakin yadda suke iya controlling ɗin su, yanzu kuwa da take ganin hakan a gaban ta sosai se take jin kamar itama ta gwada sedai kuma tana tsoro.
Sanye take da kayan saƙi irin na Fulani, ƙaramar riga da bata sauka kan cikin su ba se zanin saƙi ɗaure a jikin ta shima be ko kai ƙaurin ta ba, gashin kanta ya wani barbaje kamar be taɓa ganin gyara ba, ƙafafun sanye da wani tsohon silifas da arɗo ya samo mata da ƙyar cikin garin su dan ta ƙi yadda ta saka irin takalman su.
Da sauri ta miƙe ganin Bingel na shirin ficewa da shanun bayan ta gama yi wa Nene magana cikin bahagon yaren su da ya kasance fulatanci sedai na su fulatancin ba irin na gamagarin Fulani bane, nasu na Fulani daji ya sha banban da ragowa.
"Ki tsaya ni, nima zanje".
Tsayawa Bingel tayi tana kallon Kisnah kafin ta juya ta kalli babar ta, gyaÉ—a mata kai Nene tayi alamun su je tare tun d tana so.
Ba yau ne ta fara fita kan ta ba ɗan kwali ko hula ba haka ba yau ta fara fita da kayan da basu rufe mata jiki ba shakka yasa ko kaɗan abin be dame ta ba ta fice a yadda take, ita matsalar ta ɗaya da kayan nauyi ga kuma zani da bata saba sawa ba da yake bata matsala wajen tafiya shiyasa ma in ta tashi take ɗaure shi can sama dan da ƙyar yake kai wa gwiwar ta, ɗaurin zanin kuwa dole ya bawa wanda yaga yadda ake yin sa dariya dan kawai cukurkuɗa kayan ta take ta cusa tayi gaba abinda, to ta ina zata fara wahalar da kanta, dole dai su ɗin zata saka tun da nata gaba ɗaya sun ɓaci da jini haka wasu guraren duk sun yayyage.
A hankali suke tafiya da Bingel yayinda shanun suke gaban su, kalle kalle take hannun ta riƙe da sandar da ta saka dole Bingel ta ɗauko mata itama wai zata taya ta kula da shanun, sosai garin ya burge ta ganin ko ina cike yake da korayen ciyayi, daga inda take ta hango kogin dake gaba da su sosai wanda da alama nan zasu tsaya da shanun, aikuwa suna kaiwa wajen taga duk shanun sun tsaya haka kuma sun fara ƴan ciye ciyen su, seda ta juya bayan ta sannan tasan ashe sun shiga daji sosai dan bata ma iya gane ta wace hanya suka kawo nan ɗin ba.
Ɗan kallon Bingel tayi kafin ta juya ta shiga bin wata hanya da taga wasu kyawawan tsuntsaye na tafiya a jere a jere a sama, sannu a sannu take bin tsuntsayen tana irga adadin su har tayi nisa bata ankara ba, seda ta gaji kafin kuma ta juyo dan komawa wajen Bingel sedai sam ta rasa ta hanyar da ta shiga wajen, hanyoyi ne da yawa gasu nan haka yasa ta daburce ta rasa ina zata bi, tsayawa tayi cikin tunanin wace hanya zata bi daga ƙarshe dai ta zaɓi bin hanyar dake right hand ɗin ta, without any second thought ta shiga tafiya tana me fatan Allah yasa hanyar daidai ta ɗauka, seda ta ɗan yi nisa kafin tafara jiyo muryoyin mutane da kuma ɗan kukan shanaye ƙasa ƙasa aikuwa cikin azama ta ƙara sauri wa tafiyar ta dan ta isko wajen dan tun da ta jiyo kukan shanu ta san ta dawo wajen Bingel.